Feb 27, 2016 07:13 UTC
  • Kasashen Nahiyar Afirka
    Kasashen Nahiyar Afirka

Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da kua cikin wannan shiri na Afirka a mako

Shirin da kan yi dubi kan muhimman batutuwa da suka danganci nahiyar Afirka, inda shirin na yau zai duba batun zaman shugabannin kasashen Afirka a birnin Addis Abba, da kuma batun shirin zabe a J. Nijar, da kuma batutuwa na tsaro a Najeria da Kamaru, gami da batun gabatr da kwamitin binciken rikicin Zaria daga bagaren jahar kaduna, da ma wasu batutuwan na daban gwargwadon yadda lokaci ya bamu hali.
Da fatan za  akasance tare da mua  cikin shirin.
…………………………………………….
To bari mu fara da zaman taron shugabannin Afirka da aka gudanar a cikin wannan mako, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka danganci nahiyar ta Afirka, musamman batun bunkasa ci gaban nahiyar, da kuma kare hakkokin mata da kananan yara, gami da hada karfi da karfe a tsakanin kasashen nahiyar wajen yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka addabi wasu daga cikin kasashen nahiyar, irin su Boko haram Alshabab da sauransu.
Haka nan kuma an zabi shugaban kasar Chadi Idris Deby a matsayin sabon shugaban kungiyar na karba-karba.
…………………………………………
Dangane da kdammar da kwamitin bincike kan rikicin Zaria da gwamnatin jahar Kaduna ta yi kuwa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan mabiya mazhabar shi’a sakamon harbi da bindiga kansu da sojoji suka yi.
………………………………………….
To za mu sake komawa tarayyar Najeriya daga bisani, amma yanzu bari mu nufi jamhuriyar Nijar, inda a cikin wannan mako ne aka sanar da bude yakin neman zabe a hukumance, domin fuskantar zabukan da za a gudanar a kasar nan da yan kwanaki masu zuwa.
…………………………..
To bari mu sake komawa tarayyar Najeriya, inda majalisar dattijan kasar ta amince da kasafin kudin shekara da shugaba Muhammad Buhari ya gabatar mata.
…………………………
To dangane da batun tsaro kuwa, mutane kimanin 86 suka rasa rayukansu sakamakon mummunan hare-haren bam da bindiga da kungiyar Boko Haram ta kai kauye Dalori da ke garin Maiduguri a arewa maso gabashin Najeriya, wanda ke tazarar kilo mita 12 daga birnin Maiduguri, kamar yadda kuma bayanai suka tababtar da cewa mayakan na Boko Haram sun kona gidajen jama’a da dukiyoyi, kamar yadda kuma suka kona mata da kananan yara kurmus a cikin gidaje, sa’anan kuma suka kwashe musu abinci.
Mayakan na Boko Haram sun kai irin wannan hari a  yankin tabkin Chadi, inda suka kasha mutane 3 tare da jikatta wasu da dama, kamar yadda mahukunta  akasar suka tabbatar.
……………………………………..
Jama’a masu saurare da wannan muka kawo karshen namu na wannan lokaci, sai Allah ya kai mu mako nag aba, za a jimu dauke da wani shirin, kafin lokacin nake yi muku fatan alkhairi wassalamu alaikum.