Feb 27, 2016 07:17 UTC
  • Daesh Na Kwace Yankuna A Gabashin Libya

Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da kua cikin wannan shiri na Afirka a mako.

Shirin kan yi dubi kan wasu daga cikin muhimman lamurra da suka wakana a wasu daga cikin kasashen Afirka, inda a yau idan ana tare da mu za a ji mu dauke da wasu labaran

…………………………….
To bari mu fara daga tarayyar Najeriya, inda a cikin wannan mako ne hukumar da ke kula da samar da wutar lantarki a kasar ta sanar da kara kudin wutar lantarki da kashi 45%, lamarin da ya fuskanci akkakusar suka daga babbar kungiyar kwadago ta Najeriya.
Kungiyar ta gudanar da gangami da zanga-zanga a birnin Abuja fadar mulkin Najeriya a ranar Litinin da ta gabata, tare da yin kira ga gwamnati da a dauki matakin janye wannan Karin wutar lantarki da aka yi a kasar nan da makonni biyu masu zuwa, idan kuma ba haka za su dauki matakai da ba za su yi gwamnati dadi ba.
Wannan ya sanya hukumar mai kula da harkar samar da wutar lantarki a Najeriya fitowa ta kare wannan mataki, ta hanyar bayyana cewa ya zama dole ne a yi hakan, domin kuwa babu kudin da za a biya kamfanonin da suke aikin samar da wutar lantarki a kasar, wanda ta hanyar wanann Karin ne kawai za a iya samo kudin da za a biya su.
……………………………………..
To bangare guda kuma wani abun wanda shi ma ya dauki hankali matuka a Najeriya shi ne batun ikirarin da sojojin kasar suke yi dangane da yankunan da suka kwace iko da su daga hannun ‘yan Boko Haram a cikin jahar Borno, bayan da dan majalisar dattijai daga jahar Borno ya karyata ikirarin sojojin, inda ya ce kanann hukumomi 3 ne kawai daga cikin jahohi 27 na jahar suke da cikakken tsaro, yayin da kuma a wasu kanan hukumomin ma ‘yan Boko Haram ne cin Karen babu babbaka, kamar yadda wasu daga cikin al’ummomin jahar ta Borno suka ta tabbatar da hakan.
Wannan furuci da dan majalisar dattinaj na jahar Borno ya yi, ya sanya wasu daga cikin al’ummomin Najeriya diga alamar tambaya dangane da ikirarrin da sojojin suke yi na cewa sun karya kungiyar ta Boko Haram a cikin jahar Borno tare da kwace yankunan da kungiyar ke iko da su.
…………………..
A can kasar Libya kuwa a daidai lokacin da ake ci gaba da kokarin ganin an kafa gwamnatin hadin kan kasa domin kawo karshen badakalar siyasa a kasar, mayakan ‘yan ta’adda na ISIS suna ci gaba da kwace yankuna a gabashin kasar, musamman ma yankunan da ke da arzikin danyen man fetur da iskar gas, yayin da ita kuma kasar Tunisia ta sanar da cewa ta fara gida wata Katanga da za ta rufe iyakokinta da kasar Libya, saboda barazanar ‘yan ta’adda.
…………………………..
To bari mu sake komawa tarayyar Najeriya, inda a cikin wannan makon ne fadar shugaban kasa a Najeriya ta sanar da cewa kasafin kudin da aka yi a bana za a iya karbar shawarwari a kansa, yayin da kuma ake ci gaba da batun karbar bashi domin cike gibin da kasafin kudin yake fuskanta.
………………………………..
To a bangare guda kuma wani dan majalisar wakilai daga jahar Neja  a tarayyar ta Najeriya Hon. Abubakar Lado, ya dauki nauyin koyar da matasa 1000 sana’oin hannu daban-daban, tare da basu kayan aiki da kudade a matsayin jari idan sun kamala samun horon domin su dogara da kansu.
……………………………………..
To jama’a masu saurare lokacinmu ya kaow karshe a nan za mu dakata, sai Allah ya kai mu mako na gaba za a ji mu dauke da wani jigon.