Ma'anar Gyara a sakon Annabawa
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau mine ne manufar gyara a sakonin Annabawa?kafin neman amsar tambayar bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.
*******************Musuc**************************
Masu saurare, kamar yadda shirin ya saba ya kan komawa kan nauyaya biyu watau Alkur'ani mai tsarki da kuma tafarkin iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka, domin samun amsar tambayarmu, Hakika idan muka yi nazari cikin Alkur'ani mai girma, za mu ga cewa da dama daga Ayoyin da suke bayyani kan kiran Annabawan Allah tsarkaka, sun fi bayyani kan cewa mabi yawa daga cikin Annabawan Allah an aiko su ne domin gyara wasu sananun cututtuka da suka addabi Addinin su, na dabi'u ne ko na zamantakewa ko kuma na Akida ne.abinda yake ga da'awar ko wani Annabi shi ne kokari wajen gyaran wadannan Al'umma da kuma shiryar da su zuwa hanya madaidaiciya ta hanyar kirar su zuwa ga tsoron Allah madaukakin da kuma kadaita shi wajen ibada da bauta tare kuma da kiransu na kauracewa dukkanin nau'I na shirka da yiwa Allah Kishiya, da kuma Nisantar duk wani nau'I na zalinci gami da tsarkaka daga dukkanin kaucewar hanyar da za ta hana su rayuwa mai kyau a Duniya da Lahira. Ko ya kasance kaucewa hanyar ta bangare dabi'u ne kamar yadda ya kasance ga Al'ummar Annabi Ludu(a.s) ko kuma a bangaren tattalin Arziki kamar yake ya kasance ga Al'ummar Annabi Shu'aibu (a.s) da makamantan su. Dukkanin wadannan ababe sun yi hanun riga da Adalci gami da Kyautatawar da Allah madaukakin sarki ya yi umarni da su a matsayin tushan rayuwa mai kyau. Ma'anar hakan kuwa shi ne abinda za mu fahimta a cikin Ayoyi da suka ambaci Kalmar Islahi watau gyara daga cikin wa'azi da kuma Khudubobin Annabawar Allah tsarkaka ga Mutanan su.
Masu saurare, a kwai dangantaka da kuma alaka mai kyau tsakanin bautar Allah madaukakin sarki da kuma gyara Al'umma gami da Tausayin Ubangiji wajen kore duk wani abu da yake yiwa Bayi barazana na hanasu samun kyakkyawar rayuwa a Duniya da Lahira, idan muka yi nazari dangane da Ayoyi na 84 zuwa na 88 daga cikin Suratu Hudu (a.s) da kuma suke bayyani kan Kisar Annabin Allah Shu'aib (a.s) Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuma Mun aiko wa (mutanan)Madyana dan'uwansu Shu'aibu, ya ce:"Ya mutanena, ku bauta wa Allah, ba ku da wani Ubangiji Wanins, kada kuma tauye mudu da ma'auni, Hakika ni ina ganin ku da alheri (watau wadata) kuma hakika ni ina tsoratar muku azabar rana mai kyewayewa* Kuma ya mutanena, ku cika mudu da ma'auni da adalci, kada kuwa ku tauye wa Mutane abubuwansu, kada ku yi barna da gangan a bayan kasa*Abin da zai wanzu a gare kun a alheri a wurin Allah shi ya fi muku in kun kasance mumunai.Ni kuma ba mai gadin ku ba ne*Suka ce:"Ya Shu'aibu, yanzu sallarka ce take umartar ka da (ka sa) mu bar abin da iyayenmu suke bauta wa, kada kuma mu aikata abin da muka ga dama da dukiyoyinmu? Hakika lallai kai ne sarkin hakuri shiryayye * Ya ce:"Ya mutanena, me kuke gani ne, idan na kasance a kan bayyananiyar hujja daga Ubangijina, ya kuma arzuta ni da kyakkyawan arziki daga gare shi.Ba na kuma nufin in yi sabani da ku a aikata abin da nake hana ku yin sa, ba abin da nake so sai gyara iyakacin ikona, kuma dacewata ba inda take sai ga Allah, a gare shin a dogara, kuma a gare Shi ne zan koma) suratu Hudu daga Aya ta 84 zuwa ta 88.
***********************Musuc****************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, idan muka koma kan nauyi na biyu watau bangaren shiriyar iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka, za mu samu hadisai da dama da suke bayyani kan tushan gyara a Da'awa da kuma kira na Annabawan Allah tsarkaka, misali a cikin Littafin Kafi na sikatu Islam kulaini an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Hakika Allah madaukakin sarki ya yi wahayi zuwa wani Annabi daga cikin Annabawan Allah tsarkaka ga wata masarauta ta wani Sarki mai girman kai daga sarakuna masu girman kai da suka gabata, Allah madaukakin sarki ya ce ya je yace masa Shi Allah madaukakin sarki bai ba shi wannan milki ba domin ya zubar da jinni, da kuma kwace dukiyar Al'umma, kuma Hakika Allah ya ba shi wannan matsayi ne domin ya dakile muryar wadanda aka zalinta daga wajen Allah, kuma hakika Allah ya ce Shi ba zai bari ana zalintar masu karamin karfi da raunana ba ko da kuwa sun kasance Kafirai). Masu saurare Hakika tafarkin Annabawa wajen gyaran Al'umma ya yi tajalli a aiyukan dukkanin Shugabanin iyalan gidan Annabta tsarkaka,tafarkin su suna ishara ne kan cewa manufar gyara shi ne tushe na aiki da kuma kokari wajen cimma manufofin sakon Allah tabaraka wa ta'ala, misali cikin Littafin Nahjul-Balaga an ruwaito wata Addu'a daga Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) yayin da yake bayyana dalilinsa na yakar karkatattu da kuma wadanda suka kaucewa hanya a yakin Siffin da Jamal da kuma Nahrawan:( Ya Ubangiji Hakika Ka san cewa abinda ya kasance daga gare ni, ba dan kodayin milki ba ne ba kuma ba dan abinda Duniya ba ne ba saidai domin mu mayar da Duniya zuwa ga Adininka, kuma mu bayyana gyara a garin ka, wadanda aka zalinta daga cikin Bayinka su amintu, kuma mu tayar da abinda aka bari na dokokin ka, Ya Ubangiji ni ne farkon wanda ya koma gare ka ,ya ji kuma ya amsa babu wani da ya rigaye ni tsaida salla face Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka) Hakika Kuma Dan Sa Imam Husaini (a.s) ya kira Allah madaukakin sarki da irin wannan Du'a'I a waki'ar Karbala ya yin da yake bayyana manufar tashin sa wajen fito na fito da Yazidu Dan Mu'awiya yana mai cewa: (Hakika na fito ne domin neman gyara ga Al'ummar Kakana Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma in yi umarni da kyakkyauwa in yi hani da abin ki), domin haka ne ma Masu saurare neman gyara ya kasance tushe ne a aiyukan mabiyar mazhabar iyalan gidan Annabta tsarkaka, kamar yadda Shugabanmu Imam Kazim (a.s) ya bayyana a riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Tuhuful-Ukul yayin da yake bayyana wa daya daga cikin mabiyansa yana mai cewa:(Ya Dan Bukair, Hakika Ni zan fada maka wata Magana da ta kasance daga Ma'aifana amincin Allah ya tabbata a gare su, Hakika Gaskiya na da ahalin ta kuma haka zalika karya na da ahalinta,ahlin gaskiya kuma su ne wadanda suke tafiya tare da mu zuwa ga Allah ta hanyar gyaran Al'umma, kuma Allah ya aiko mu Rahama da aminci ga masu rauni da kuma Al'umma gaba daya,Ya Kai Bawan Allah wadancan (watau masu wadannan siffofi) su ne mabiyanmu kuma wadancan su ne namu, kuma wadancan su ne Mutanan mu kuma su ne suka yi mana biyayya) da fatan Allah madaukakin sarki ya yi mana muwafaka da abinda yake so kuma ya yarda da shi wajen kokari na gyara dai dai kwalkwado dan Albarka riko da kuma biyayya ga shugabanin masu gyaran Addinin Allah Annabi Muhamadu da kuma iyalan gidansa tsarkaka gaba daya.
**********************Musuc***********************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.