Da'awar Annabawa kan Masu Girman Kai
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta yau it ace mine ne matsayin Da'awa ko kiran Annabta a kan girman kai kuma mine ne za mu amfana a cikin wannan rayuwar mu ta wannan zaman daga matsayin Annabta? Amma kafin shiga cikin shirin bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.
**************************Musuc*********************************
Masu saurare, idan muka buda Alkur'ani mai girma za mu samu ayoyi da dama masu albarka da suke bayyanin cewa Hakika Allah madaukakin sarki ya aiko Annabawa ne domin tunkarar masu girman kai da kuma kare masu karamin rauni, domin haka ne Ya kasance masu girman kai su ne a sahun farko wajen yakar Da'awar Annabawan Allah amincin Allah ya tabbata a gare su.baya ga haka Ayoyi da dama sun bayyana cewa yin bara'a ko tawaye ga girman kai na daga cikin rukuni na biyu ga tsarkakekken tauhidi, ko kuma kadaita Allah, misali cikin suratu Nahli Allah madaukakin sarki ya ce:(Hakika kuma Mun aiko Manzo a kowacce al'uma cewa:"Ku bauta wa Allah, kuma ku nisanci sahidan."To akwai daga cikinsu wadanda Allah ya shirya, akwai kuma wadanda bata ya tabbata a kansu (har mutuwa).To ku yi tafiya a bayan kasa sai ku ga yadda karshen masu karyatawa ya kasance)suratu Nahali Aya ta 36. Abin fahimta daga cikin wannan Aya mai albarka shi ne daga cikin mahiman manifofin Da'awa ko kuma kiran Annabawan Allah shi ne 'yantar da Mutane daga kangin masu girman kai domin su bude musu wani sabon fage na kyakkyawan rayuwa mai inganci, Allah madaukakin sarki ya ce:(Wadanda kuwa suka nisanci gumaka don kin bauta musu, suka kuma koma ga Allah, suna da albishir (na Aljanna). To ka yi wa bayina albushir*Wadanda suke jin Magana sannan su bi mafi kyawunta, wadannan su ne wadanda Allah ya shirya, kuma wadannan su ne ma'abota hankula) suratu zumari Aya ta 17 da kuma ta 18. Wasu Ayoyin kuwa sun bayyana cewa hakika Allah tabaraka wa ta'ala ya aiko Annabinsa Musa (a.s) domin 'yanto Bani isra'ila daga kangin bauta da Azaba da babban fajirin na mai girman kai da ma ya kira kansa a matsayin Ubangiji watau Fir'auna, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Muna karanta maka labarin Musa da fir'auna na gaskiya don mutanen da suke ba da gaskiya*Hakika Fur'auna ya yi dagawa a bayan kasa ya kuma sanya mutanenta kungiyoyi daban-daban, yana bautar da wata kungiya daga cikinsu, yana yanka 'ya'yayensu Maza, yana kuma raya mata.Hakika shi ya kasance cikin masu barna*Muna kuma so Mu yi baiwa ga wadanda aka wulakanta a bayan kasa, muka kuma sanya su Shugabanni, kuma mu mayar da su magadan (milkin Fur'auna)*Mu kuma Kafa su a bayan kasar, kuma Mu nuna wa Fir'auna da Hamana da rundunoninsu gaba dayansu abin da suke jin tsoro game da su(mutanen))suratu Kasasi daga Aya ta 2 zuwa Aya ta 6. Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya bayyana mana cewa Hakika Allah madaukakin sarki ya umarci Annabawansa tsarkaka da kari na yin tawalu'u domin karya kayar masu girman kai cikin zukata, kuma Al'umma su koyi bijerewa masu girman kai, a cikin Littafin Irshadul Kulub, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya ce:(Annabi Suleimana (a.s) ya kasance tare da wadanda suke tare da shi na sarakunan lokacinsa, yana sanya kayan alfarma, idan kuma Dare ya riske shi ya kan daure hannayansa zuwa ga yuyansa hakan zai kasance yana kuka har safiya, kuma ya kasance abicin sa daga abincin masu karamin karfi yana girkawa da hanunsa, Hakika shi ya bukaci milki ne daga domin domin ya karya lagon masu milki na Kafirci).
****************************Musuc*********************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara ne da Hadisin Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) a cikin Littafin Nahjul-Balaga, Imam (a.s) y ace:(Da Allah madaukakin sarki zai saukaka girman kai ga wani daga cikin Bayainsa da ya saukaka shi ga Annabawansa da waliyansa, to saidai shi madaukakin sarki ya gyama shi girman kai a gare su , ya kuma amnice musu da tawalu'u,sai suka saje da mutane a doron kasa, sannan kuma suka kasance masu sauki kai ga mumunai).a wani bangare na wannan Khuduba Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya yi ishara kan cewa bayyana Tawalu'u daga wajen Annabawa ya kasance yaki ne a aikace ga duk wani ruhi na girman kai a cikin zukatan masu girman kai kuma babbar izza ne ga Annabawan Allah a bangare guda, kamar yadda ya kasance ga Annabi Musa (a.s) da Fur'auna.Imam (a.s) ya ce:( Hakika Allah madaukakin sarki yana jarabtar bayin sa masu girman kai da waliyansa masu rauni a idansu daga cikin su (watau abinda ake nufi da masu rauni a idanuwansu, wadanda su suke ganin su masu rauni saboda rashin Dukiya ko milki), imam (a.s) ya ci gaba da cewa Hakika Musa Dan Imran tare da Dan uwansa Harun amincin Allah ya tabbata a gare su sun shiga wajen Fur'auna suna sanye da rigar da aka saka da gashin dabbobi kuma a hanunsa a kwai sanda sai suka gindaya masa sharadi, idan har ya musulinta zai ci gaba da milki kuma girmansa da buwayarsa zai dawwama, sannan Imam Ali (a.s) ya ci gaba da bayyana kan yadda Fur'auna ya yi kokarin kalubalantansu wajen yin tasiri ga matsayinsu a cikin mutanansa, sai Fur'auna ya ce, shin ba kuyi mamaki da abinda wadannan suke fada ba, suna gindaya mini sharadi na dawwamar girma da kuma ci gaba da milki, alhali su kuma suna cikin hali na talauci da gaskanci Shin b azan jefa musu wasu mundãye na zinari ba?Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya takaita maganar zuwa ga sakamakon bayyanin wajen bayyana tafarkin Annabta yana mai cewa sai dai Allah mdaukakin sarki kuma ya sanya Ma'aikansa mafi karfi wajen azamarsu da kuma rauni ga abinda idanuwa ke gani na yanayinsu tare da wadatar zuci da ta cika zukata.
Masu saurare takaicecciyar amsa na tambayar shirin mu na Yau, shi ne yakar girman kai da kuma bijerewa masu girman kai gami da 'yantar da kai daga gare su da kuma ciratar da Al'umma daga kanginsu, na daga cikin mahimancin rukuan sakon Annabawa da aiyukansu.
**********************Musuc***********************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.