Ma'anar Fitar da Mutane daga Duhu zuwa Haske Na Annabawa
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, Tambayarmu ta Yau me ake nufi da ma'anar cewa Annabawa suna fitar da Mutanan su daga cikin duhu zuwa ga haske? Kafin mu shiga shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi kan faifai.
**********************Musuc****************************
Masu saurare, domin amsa tambayar mu ta Yau, shirin zai fara da Ayoyi na 4 zuwa na 6 cikin suratu Ibrahim (a.s), inda suke ishara kan bayyanin gaskiya da Annabawan Allah tsarkaka ke yiwa Mutanan su tare kuma da tunatar da su Ni'imar Allah madaukakin sarki, Ayarsa gami da Kudurarsa, Shakka babu wadannan abubuwa na daga cikin misdakin buda kofofi na fitar su daga Duhu zuwa ga Haske, Allah madaukakin sarki ya ce:(Ba mu taba aiko wani Manzo ba kuwa sai da harshen mutanensa don ya bayyana musu (komai), sannan Allah yana batar da wanda Ya so yana kuma shiryar da wanda ya so.shi ne kuwa Mabuwayi, Gwani*Hakika Kuma Mun aiko Musa da Ayoyinmu cewa:"Ka fitar da mutananka daga Duhu zuwa ga haske. Kuma ka tunasar da su ni'imomin Allah (ga Al'ummun baya) hakika game da wannan da akwai ayoyi ga duk wani mai yawan hakuri mai yawan godewa* Kuma (ka tuna) lokacin da Musa ya ce da mutanensa:"Ku tuna ni'imar Allah a gare ku lokacin da ya tserar da ku daga Mutanen fir'auna:suna gana muku mumunar azaba, suna kuma yanyanka 'ya'yayenku, kuma suna raya matayanku.A game da wannan da akwai bala'I mai girma daga Ubangijinku). Mabudin wannan surat mai albarka, ya kasance kira zuwa ga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa inda take ishara kan cewa fitar da Mutane daga duhun zalinci da jahilci zuwa hasken shiriya da ilimi shi ne muhimin batun dake tabbatuwa ta hanyar abinda Allah madaukakin sarki ya saukar cikin Littafinsa mai tsarki, cikin suratu Ibrahimu Aya ta 1, Allah tabarka wa ta'ala ya ce:(ALIF LAM RA.Allah ne ya san abin da yake nufi da wadannan harufan.(shi) Littafi ne da muka saukar da shi a gare ka (Ya Muhammadu) don ka fitar da mutane daga duhu zuwa ga haske, da izinin Ubangijinsu zuwa ga tafarkin (Allah) Mabuwayi abin godewa) Masu saurare, kamar yadda kuka ji wannan Aya mai albarka tana ishara a bayyane kan cewa abinda ake nufi da haske shi ne tafarkin Allah Mabuwayi abin godewa da Mutane ke ganin cewa a cikin sa ne ke akwai buwayar Allah da zai fitar da su daga kaskanci, bayan ga hakan ga Ni'imarsa a gare su su kuma gode masa domin shi Tabaraka wa ta'ala abin godewa ne.Masu saurare, hakika wasu Ayoyi da dama cikin Alkur'ani mai girma sun siffanta Litattafai ukun da aka saukar da Haske, ko kuma fitilar da a cikin ta a kwai shiriya da haske. wannan ishara ne na cewa abinda ake nufi da ma'anar aiko da Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su, domin fitar da Mutanan su daga duhu zuwa ga haske, shi ne isar da hakikanin sanin da zai fitar da su daga duhun jahilci da bata zuwa hasken shiriya da kuma hanya madaidaiciya.da kuma hakan ne za su cimma wa hakikanin rayuwa mai kyau kamar yadda fadar Allah madaukakin sarki a Aya ta 122 cikin sutaru An'ami ke ishara da hakan, Allah madaukakin sarki ya ce:( Shin Wanda ya kasance matacce (cikin kafirci) Sannan Muka raya shi (da shiriya) Muke kuma sanya masa haske (na shiriya) yana tafiya da shi cikin mutane, (yanzu) ya yi daidai da wanda yake cikin Duhun (kafirci) kuma ba zai fita daga cikinsa ba? Kamar haka ne aka kawatar wa kafirai abin da suka kasance suna aikatawa) suratu An'ami Aya ta 122.
*************************Musuc********************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa kuma kadda a sha'afa, shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran daga nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai koma kan Nassosi na tafarkin Iyalan gidan Annabta tsarkaka da suke a matsayin shugabanin shiriya, idan mun koma cikin hadisan da aka ruwaito daga gare su, za mu samu cewa suna bayyani kan hasken dake daga mutum ya na isar da shi zuwa ga hanya madaidaiciya, wannan haske ba kamai ba ne face Shugaban gaskiya da Allah tabaraka wa ta'ala ya zabe shi a wannan matsayi na Imami.misali cikin Tafsiru Majma'ul bayyan, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) yayin da yake bayyani kan Ayar da ta gabata, sai ya ce wannan Aya ta sauko ne kan Amar bn Yasir yayin da ya yi Imani, shi kuma Abi jahal ya yi watsi da bada gaskiya da kuma Imani ga Ma'aiki(s.a.w.a) sai ya kasance cikin duhun Jahilcinsa da yanayin jahiliya.Wato Imanin Amar bn Yasir ya kasance mubaya'a da kuma koyi da Shugaban Zamaninsa kuma shugaban Talikai Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma hakan yana ishara ne a kan mubayar ko wani Mutum da Imamin zamaninsa, kamar yadda hadisai da dama suka yi ishara.misali cikin Littafin Kafi da tafsiru Ayyashi da makamantansu, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) yayin da yake ta'awili ko fasarar Ayar da ta gabata cikin Suratu An'ami, a fassarar wannan Kalma مَيْتاً sai ya ce ma'anar wannan kalma shi ne wanda bai san komai ba, kuma fadar Allah na cewa (Muke kuma sanya masa haske (na shiriya) yana tafiya da shi cikin mutane) sai Imam (a.s) ya ce abinda ake nufi da wannan haske shine Imami daga iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka, amma fadar Allah madaukakin sarki na cewa ( wanda yake cikin Duhun (kafirci) kuma ba zai fita daga cikinsa ba) ma'ana wanda bai san Imamin lokacinsa ba,A cikin Littafin Aliyu bn Ibrahim Alkummy an fassara ma'anar wannan Aya (Macacce sai muka raya shi) da cewa Ai ya kasance jahili game da gaskiya da kuma wulaya ta iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka sai muka shiryar da shi zuwa ga gaskiya gami da wulaya, sannan kuma muka sanya a gare shi hasken da yake tafiyar da shi cikin Mutane kuma wannan haske shi ne wulaya ta iyalan gidan Annabta tsarkaka. A cikin Littafin Kafi, cikin wani hadisi mai tsaho da aka ruwaito daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Rayayye shi ne Mumuni, Matacce kuma shine kafiri, wannan kuma shi ne ma'anar fadar Allah madaukakin sarki:( Shin Wanda ya kasance matacce Sannan Muka raya shi).Masu saurare takaicecciyar amsar da muka fahimta a wadannan Nassosi masu albarka dangane da tambayar da muka bijoro ta iya cikin wannan shiri shine:Ma'anar tayar da Annabawa ko kuma aiko su, domin su fitar da Mutane daga Duhu zuwa haske shi ne tseratar da su daga Duhun Zalinci da kuma Jahiliya ta hanyar bayyana musu hakikanin Imani da kuma tunanar da su kan alkawarin da suka dauka tun kafin su zo Duniya daga wajen mahalicinsu Allah tabaraka wata'ala.shi ne su sanar da su gaskiya na sanin Allah da kuma Ni'imar sa domin su bi hanya madaidaiciya ta hanyar yin biyyaya ga Shugaban gaskiya wanda Allah madaukakin sarki ya zabe shi a tsakanin su.da fatan Masu saurare Allah ya bamu damar riko da wulaya ta iyalan gidan Anabta wadanda Allah subhanahu wa ta'ala ya tayar domin su shiyar da bayinsa kuma mu yi koyi da su domin samun tsira da kuma kyakyawar makoma.
**********************Musuc***********************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.