Zaben Shugaban Kasa A Jamhuriyar Nijar 2016
Shiri na musamman dangane da zaben shugaban kasa da kuma na 'yan majalisar dokoki da aka gudanar a jamhuriyar Nijar a cikin wanann mako.
Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu da sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na musamman na musamman wanda zai yi dubi kan yadda aka gudanar da zabukan shugaban kasa da kuma nay an majalisar dokoki na jamhuriyar Nijar a ranar a 21 ga wannan Fabrairu, inda zan kasance tare da abokan aikina a cikin nan dakin watsa shiryenumu wato Muhammad Awwala Abubakar Bauchi, daga kuma Hassan Barka Agadez, kamar yadda kuma za mu ji ta bakunan ‘yan siyasa daga jamhuriyar ta Nijar a bangaren masu mulki da kuma masu mara musu baya, da kuma yan adawa gami da jamari gari, kamar yadda kuma za mu ra’ayoyin masu saurare da suka aiko mana ta kafofin sadarwa na sada zumunta, whatsaap da kuma facebook.
Da fatan za a kasance tare da mua cikin shirin.
Music………………………………………..
Jamhuriyar Nijar wacce ke yankin yammacin Afirka, kasa ce mai fadin murabba'in kilomita miliyan daya da dubu dari biyu da sittin da bakwai (1,267.000 km).
Kasar wacce birnin Yamai yake a matsayin fadar gwamnatinta, ta yi iyaka da kasashen Najeriya, Jamhuriyar Benin, Burkina Fasa, Mali, Aljeriya, Libya da kuma Chadi.
Kuma yawan al'ummar kasar ya tasamma sama da mutane milyan 17 a halin yanzu.
Ita dai wannan kasa tana daya daga cikin kasashe 15 da suka samu yancin kansu daga kasar Faransa a cikin shekara ta 1960, inda kasar ta samu nata 'yancin a ranar 3 ga watan Agustan shekarar ta 1960.
Kasar Nijer wace ta kunshi jihohi guda takwais da suka da hada da Niamey babban birni, Zinder, Maradi, Tawa, Dosso, Tillabery, Diffa, da Agades, ta kunshi albarkatun kasa masu yawa, kama daga Zinare, karfe, Gol, Urenium da kuma man fetur, duk kuwa da cewa dai har ana lissafa kasar ta Nijar a cikin kasashe masu fama da talauci.
Gabatarwa 2
Idan muka koma ga maudi’in da muke son yin magana a kansa kuwa a wannan shirin, za’a iya cewa a shekara 1990 ne guguwar demukuradiya ta fara kadawa a Nijer a lokacin mulkin shugaban rikon kwarya soja Kanal Ali Shaibu wanda ya amunce da bukatar kungiyoyin fara na ganin an kai ga mulkin demokuraddiyya, hakan ne kuma yasa ya amunce da hakan tare da sallamar fursunonin siyasa da ‘yan gwagrwamaya a lokacin.
Kuma da hakan ne sannu a hankali jam’iyyun siyasa da kungiyoyi fara hula suka fara kafuwa a wannan kasa.
An dai fara zaben shugaban kasa na farko a jamhuriya ta Nijer a watan Maris na shekara 1993, wanda hakan ya baiwa Mahamane Usman zama shugaban kasa na farko.
Sannu a hankali dai tafiya na tafiya wannan shi ne zabe na biyar a jamhuriya Nijer.
Zaben na bana ya hada dana shugaban kasa gami dana ‘yan majalisun dokoki.
Kuma ‘yan takara 15 ne ciki har da shugaban kasar mai barin gado Mahamadu Issufu ke zawarcin kujera shugaban kasa.
Sanan kuma ‘yan kasar zasu zabi ‘yan majalisu 171 da zasu wakilce su a zauren majalisar dokokin kasar.
…………………….
Studio///////////////
A – Barka
B – Bauchi
Akwai yan korafe-korafe da aka samu a wasu yankunan jinkirin kai kayan zabe, wanda hakan ya sanya har aka ja lokacin ya kai wan shekare a wasu wuraren.
Ga dai Maryama Katanbai mataimakiyar shugaban hukumar zabe a Niger da Karin bayani kan lamari.
(1)………………………………
To yanzu kuma mu ji ta baki wasu daga cikin ‘yan siyasa daga jam’iyyu da suka fata a wannan zabe, za mu fara jin ta bakin Tijjani Ume na PDNS tarayyar mai mulki a Nijar, kan yadda suka ga zaben…….
(2) …………………………………………………………….
To ko su a nasu bangaren jam’iyyun adawa ya suka ga zaben? Bari mu ji ta bakin Tsalha Abdu na Lumana Afirka…
(3) ………………………………………………………..
To su ma yan jam’iyyar MNSD Nasara suna da nasu ra’ayin kan wannan zabe, kan ahakn bari mu ji ta bakin Yahaya Ari mamba a wannan jam’iyya.
(4) …………………………………..
Studio//////////////////////////
A – Barka, tasirin matsalolin ga sakamaon zabe
B – Bauchi
To bari mu ji ra’ayoyin wasu daga cikin al’ummar Nijar kan wannan zabe da kuma yadda ya gudana.
(5) ………………………………………………
To a can kamaru ma an gudanar da zaben, inda mutanne kasar Nijar mazauna kasar suka kada kuri’unsu, bari mu ji ra’ayoyin wasu daga ciki.
(6)……………………………
To sai Abdulssalam Cisse waikilin hukumar zaben ta Nijar a Kamaru ya yi mana karis hakske kan su suke kallon lamarin daga bangarensu.
(7)…………………………………………..
Studio///////////////////////////
A –Barka, yadda ake sanar da sakamakon zabe, an hana kafofin yada labarai cewa komai.
B – Bauchi, Facebook
To wani abu kuma wanda shi ma ya zama daga cikin abubuwan da suka dauki hankali wanda shi ma har an samu koraefe-korafe kansa shi ne batun zabe ta hanyar sheda, kan hakan mu ji ta bakin Malam Kasim Mukhtar dan takarar shugabancin kasa a karkashin inuear jam’iyyar CPR Inganci, ko mene ne ra’ayinsa kan hakan?
(8)……………………………..
To amma Malam yahuza Salisu Madubi dan takarar majalisar dokoki a karkashin inuwar jam’iyyar RSD Gaskiyaya bayyana mana tasa mahangar.
(9) ………………………………..
To shi ma a nasa bangaren Alh. Abdullahi Zuciya, daya daga cikin jagororin yan Nijar mazauna Najeriya, wadanda su ma suka kada kuri’un nasu a Naijeriya, ya bayyana mana ra’ayinsa kan zaben da kuma yadda ya gudana.
(10)……………………
Studio///////////////////////
A – Barka
B – Bauchi
To jama’a masu saurare a nan muka kawo karshen wannan shiri na musamamn da muka gabatar muku kan zaben shugaban kasa da nay an majalisar dokoki da aka gudanar a ranar 21 ga wanann wata na Fabrairun shekara ra 2016,a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin a faifai musamman Muhammad Muhammad Aminu Kiyawa da ya dauki shirin, da kuma abokan aikina Muhammad Awwal Bauchi da Hassan Barka da suka dafa mani wajen gabatarwa, ni Abdullahi salihu Katsina ke yi muku fatan alkhairi, wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.