Nov 29, 2016 19:16 UTC

, Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, Tambayarmu ta yau a matayinmu na Musulmi Mine ne matsayin dangane da Annabawan da suka gabata? Kafin amsa tambayar bari mu saurari wannan.

******************************Musuc******************************

Masu saurare, kamar yadda shirin ya saba yak an komawa kan haskaken shiriya, Littafin Allah watau Alkur'ani mai tsarki da kuma tafarkin iyalan gidan Anabta tsarkaka domin samun amsar tambayar mu, da farko za mu fara da Alkur'ani mai girma inda za mu samu umarni Ubangiji na yin Imani ta hanyar abinda ya saukar ga Annabawansa gaba daya, da kuma abinda aka basu daga Ubangijinsu da kuma maika wuka dangane da hakan.A cikin Suratu Ali imrana daga Aya ta 83 zuwa Aya ta 85 za mu samu wannan umarni tare da gargadin Ubangiji na kadda mu riki wani Addini face Addinin Musulinci da ke a matsayin meka wuya ga Allah madaukakin Sarki, Allah madaukakin sarki ya ce:(To yanzu wani addini suke nema ba na Allah ba,alhali kuwa abin da duk yake sammai da (wanda yake) Kassai gare shi ne ya mika wuya da sonsa da kinsa, kuma wurinsa ne za a komar (da su)? Ka ce Mun ba da gaskiya da Allah da abin da aka saukar mana, da kuma abin da aka saukar wa Ibrahimu, da Isma'ila, da Ishaka,da Yakubu,da Jikokinsa, da abin da aka bai wa Musa, da Isa, da Annabawa daga Ubangijinsu, ba ma bambantawa tsakanin daya daga cikinsu, kuma mu masu mika wuya ne gare shi (Allah)* Wanda kuma ya nemi wani addini ba musulinci ba, to har abada ba za a karba ba daga gare shi kuma shi yana cikin tababbu a Lahira) Suratu Ali-imrana daga Aya ta 83 zuwa ta 85.Masu saurare har ila yau Alkur'ani mai girma ya bayyana cewa Imani da Ma'aikan Ubangiji na daga cikin siffofin mumuni kuma koyi ne da Shugaban Annabawa da Mursalai Masoyin Allah Mustapa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, Allah madaukakin sarki ya ce:(Manzo ya ba da gaskiya da abin da aka saukar masa daga Ubangijinsa, haka ma muminai kowanne ya ba gaskiya da Allah da Mala'ikunsa da Litattafansa da manzaninsa: ba ma bambantawa tsakanin daya daga manzanninsa, kuma suka ce:Mun ji mun bi, gafararka (muke nema) Ya Ubangijinmu, makoma kuma zuwa gare ka ne) suratu Bakara Aya ta 285 masu saurare kamar yadda Imani da Annabawan da suka gabata amincin Allah ya tabbata a garesu na daga cikin siffofin masu tsoron Allah kamar yadda Allah madaukakin sarki cikin suratu Bakara ya bayyana siffofin masu tsoron Allah kuma sune marabauta Allah madaukakin sarki ya ce:(Da wadanda suke bada gaskiya da abin da aka saukar a gare ka (Annabi Muhammadu) da abin da aka saukar a gabaninka (ga Manzannin da suka gaba ce ka ) alhali kuwa sun kasance da (ranar) Lahira*wadancan suna kan shiriya ta Ubangijinsu, kuma wadancan su ne masu samun babban rabo (Duniya da Lahira) suratu Baraka Aya ta 4 da kuma ta 5.abin da za mu amfana da shi daga wadannan Nassosi na Alkur'ani mai girma da suka gabata shi, Mu a matsayin mu na musulmi wajibi ne kanmu da mu yi Imani da dukkanin Annabawan da suka gabata ba tare da bambanci tsakanin daya daga cikin Annabawa da Ma'aika amincin Allah ya tabbata a gare su dangane da tushen annabcin su da kuma kiran su na tsarkakekken Tauhidi, mu yi Imani da dukkanin abinda suka zo da shi, shi ne Tauhidi da kuma musulinci daga wajen Ubangijin Talikai, kuma duk abinda ya sabawa hakan a cikin Litattafan da aka saukar daga sama da suke hannu a halin da ake ciki, to sanya shi aka yi ba wai daga wajen Ubangiji ba ne.

*********************************Musuc*************************

Masu saurare,barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta iran dake nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai koma kan hasken shiriya  na biyu watau tafarkin Iyalan gidan Anabta tsarkaka, inda za mu samu kyawawen bayyanai na tushen tauhidi na hanyar Imani da dukkanin Annabawan da suka gabata tare da karramasu amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya. Ya zo cikin wata riwaya inda aka wani Zindiki ya tambayi shugabanmu Imam Sadik (a.s) kan dalilin yin Imani da Annabawa da Ma'aika. Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa:(Hakika bayan mun tabbatar da cewa mu nada mahalicci da ya kera komai kuma madaukaki a gare mu da kuma dukkanin abinda ya halitta kuma ya kasance mahaliccin mai hikima ne bai inganta ba ga abinda ya halitta su ganshi, ko kuma su taba shi, ko kuma su tunkare shi kai tsaye ko kuma shi ya tunkare su kai tsaye, su yi jayayya da shi ko kuma shi ya yi jayayya da su, sai ya tabbata cewa shi ya nada Jikadu a cikin halitunda wadanda suke shiryar da su a kan abinda yake maslaha a gare su da kuma amfanin su, samuwar da rashin samuwar su wane ne ya fi? Bayan Imam (a.s) ya bayyana wannan Hujja ta hankali wajen tabbatar da samuwar Annabawa da Ma'aika amincin Allah ya tabbata a gare su, ya kuma bayyana mana siffofinsu na tushe gami matsayin su madaukaki a wajen Allah subhanahu wa ta'ala tare kuma da karfafa su ta hanyar basu Mu'ijiza da kuma dalilai mabayyana na inganci da sahihancin Anabtar su, Imam (a.s) ya ci gaba da cewa sai ya tabbata ga masu Umarni da Nahi daga Masani mai Hikima cikin halitunsa, kuma sune Annabawa da zababbu daga cikin halitun sa, masu hukuncin da aka tarbiyatar da hikima kuma aka aiko su da ita, tabattatu daga wajen masani mai hikima,da hikima da kuma dalilai gami da hujjoji da shaidu na raya matattu da warkar da masu cutar kuturta da makabta, kuma babu yadda kasar Allah za ta kasance ba tare Hujjar Allah ba da zai kasance tare da shi Ilimi da zai yi tabbatar da gaskiyar maganar ma'aiki da kuma tabbatar da adalcinsa).

Masu saurare, takaicecciyar amsar da muka fahimta cikin wadannan Nassosi da suka gabata dangane da tambayarmu ta wannan shiri shi ne ya wajabta a kan mu da mu yi Imani da dukkanin Annabawan da suka gabata, wadanda Anabtar su ta tabbata ta hanyar dalilai da Ayoyi. Kuma mu girmama su gaba daya saboda karamar da suke da ita a wajen Allah madaukakin sarki da kuma matsayin sun a zababbu , masu isar da sakon Allah madaukakin sarki, kuma mu yi Imani da abinda suka so da shi Addinin Allah ne kuma tauhidi ne tsarkakekke. Baya ga hakan mu tsarkake su daga duk wani abu da ya sabawa musulinci na gaskiya da kuma tsarkakekken tauhidi kan abinda aka danganta su da shi na wadanda suka kaucewa hanya daga mutanan su gami da Al'ummar su.

*********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.