Feb 29, 2016 08:50 UTC
  • Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya
    Shugaban Kasar Kamaru Paul Biya

Jama’a masu saurare Assalamu Alaikum barkanku da warhaka barkanmu kuma da sake saduwa da ku a cikin wanann shiri na Afirka a mako.

Shirin kan yi a dubi a kan muhimman lamurra da suka wakana a nahiyar Afirka a cikin mako, a yau kamar kowane mako da yardar Allah za mu duba wasu daga cikin muhimman lamaurra da suka wakana a wannan mako a nahiyar, daga cikin abubuwan da za mu tabo har da batun harin da aka kai a kasar Mali, da kuma dambarwar siyasa a Burundi, kamar yadda za mu leka kasashen Nijar, Najeriya Kamaru da Ghana, da ma wasu kasashen gwargwadon yada lokaci ya ba mu hali, da fatan za a kasance tare da mu.  ………………………………..

 

To bari mu fara shirin namu kai tsaye daga kasar Mali, inda a ranar Juma’a da ta gabata wasu ‘yan bindiga na kungiyar Ansaruddin da ke da alaka da alkaida ska kaddamar da hari a kan wani otel a garin Sevare, inda suka yi garkuwa da mutane a cikin otel din, wanda hakan yasa ala tilasta aka yi amfani da karfi domin kubutar da mutanen.

Hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 13, da suka hada da sojoji 4, da kuma ma’aikatan Majalisar dinkin duniya 5 gami da ‘yan bindiga 4.

Kakakin rundunar sojin Mali Souleymane Maïga ya fadi cewa, wasu ‘yan bindga sun sake kai wani hari a kauyen Gaberi da ke arewacin kasar inda suka kashe mutane 10, amma hakan ba shi da alaka da hare-haren na Sevare.

…………………………….

A can birnin Bujumbura na kasar Burundi kuwa a daren lahadin da ta gabata an yi barin wuta mai tsanani tsakanin jami’an tsaro da kuma wasu masu dauke da makamai da ba a san ko su wane ne ba.

Mahukuntan kasar dai sun ki su ce uffan danagne da abin da ya faru a yammaci har zuwa tsakar daren Lahadin da ta gabata a birnin na Bujumbura, amma sun ce an kame wasu da suke da hannu wajen kisan gillar da aka yi wani janar na soji kuma babban na hannun damar shugaban kasar.

Masu adawa da shugaba Nkurunziza dai sun ce ba za su taba amincewa da zaben da aka gudanar a kasar a ranar 21 ga watan Yulin da ya gabata ba, wanda masu sanya ido na kasa da kasa suka ce bai gudana kan sahihin tafarki na imokradiyya ba.

……………………………………….

To bari mu nufi kasar Kamaru, inda hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya WHO ta bayar da lambar yabo da girmamawa ga ma’aikatar ayyukan gona ta kasar, dangane da kokarin da ta yi a cikin shekarun baya-bayan nan wajen magance matsaloli da dama da suka danganci karancin abinci, da hakan ya hada tamowa a tsakanin kananan yara, saboda samar da abinci da ake yi sakamakon bunkasar ayyukan noma a kasar, wanda hakan ne ma yasa ma’aikatar ayyukan gona ta kasar ta shirya a birnin Yawunde bayan samun wannan lambar yabo.

……………………………………..

A Najeriya kuwa kungiyar IPMAN ta masu dakon man fetur a kasar ce ta yi kira ga gwamnati da ta sanya kamfanoni masu zaman kansu da ke sayar da man a cikin kasa su rika sayar da shi a kan farashin da gwamnati ta kayyade, maimakon barin kowa ya sayar yadda ya ga dama.

…………………………………..

 

To a can Jamhuriyar Nijar kuwa badakalar siyasa ce ake ta fama da ita, musamman ma batun fitar da jadawalin tsare-tsaren zabe da aka fitar, wanda jam’iyyu amsu adawa a kasar suka yi watsi da shi, wanda kuma har ta kai ga jam’iyyun na adawa a halin yanzu sun mika bukatar neman ganin an gudanar da babban taro na jam’iyyun siyasa na kasa, kuma yanzu haka suna jiran amsa daga Firayi ministan kasar, wanda har har yanzu bai ce komai kan lamarin ba.

……………………………………..

A kasar Ghana kuwa a cikin wannan mako ne malamai a jami’oin kasar da ma manyan makarantu suka tsunduma cikin wani yajin aiki, bayan da likitoci a kasar su suka shiga wani yajin aiki tun fiye da makonni biyu da suka gabata, inda dukkanin bangarorin da ke yajin aikin, suke bayyana cewa suna yin hakan domin matsa lamba kan gwamnatin kasar, domin ta biya su wasu ahkkokinsu da suka makale.

Da dama daga cikin al’ummomin kasar ta Ghana dai suna nuna matukar damuwa dangane da wanann yajin aiki, da kuma mummunan tasirin da yake da shi ga kasa da kuma rayuwar al’ummarta, musamman a bangaren kiwon lafiya, inda masu jinya suke samu kansu cikin wani mawuyacin hali saboda rashin likitoci a asibitoci, inda ake ta yin kira ga gwamnati da ta saurari masu yajin aikin, domin a samu daidaitawa  atsakaninsu.

……………………………………………………

 

To jama’a lokacin da muke da shi dai ya kawo jiki dole a nan za mu dakata, sai Allah ya sake hada mu a mako nag aba  acikin wani sabon shirin, kafin lokacin a madadin wadanda suka hada mana sautin shirin a faifai har ya kammala musamman Muhamamd Aminu Ibrahim, ni Abdullahi Salihu katsina da na shirya kuma na gabata, ke muku fatan alkhairi, wassalamu alikaum wa rahmatullah.