Jan 28, 2017 05:22 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta Yau mi nene matsayin Al'ummar da sako bai isa gare ta ba daga cikin mutanan farko ? da kuma aka bayyana cewa har yanzu a kwai irin wadannan Al'umma da suke rayuwa a wasu yankuna na kasashen Afirka da Amurka latin. Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai.

***************************Musuc*************************

Masu Saurare kamar yadda shirin ya saba, ya kan komawa kan haskaken shiriya biyu domin amsar tambayarmu, da farko za mu fara da Littafin Allah mai tsarki, inda za mu samu cewa Ayoyi da dama sun firta babu wata Al'umma da Allah madaukakin sarki ya barta hakanan ba tare da ya aika mata mai galgadi da zai fadakar da ita kan abinda zai cece ta Duniya da Lahira, A cikin Suratu Fadiru daga Aya ta 24 zuwa ta 26 Allah madaukakin sarki ya ce:(Hakika Mu Muka aiko ka da gaskiya don bushara da gargadi, babu kuma wata al'umma da (ta gabata) sai wani mai gargadi da ya wuce ya zo mata*Idan kuwa sun karyata ka, to hakika wadanda suke gabansu ma sun karyata, lokacin da Manzanninsu suka zo musu da hujjoji da takardu da kuma litattafai masu haske(shiriya) * Sannan Na damki wadanda suka kafirta, to yaya narkona ya kasance?) idan kuma muka koma kan hasken shiriya na biyu watau tafarkin iyalan gidan Anabta za mu samu hadisai da suka bayyana mana ma'anar wannan Aya mai albarka, a cikin Littafin Ilalu Shara'I'I na Shekh Saduk yardar Allah ta tabbata a gare shi, an ruwaito wani hadisi, inda a cikin sa aka ce wani Mutum ya tambayi Imam Sadik(a.s) bisa wani dalili ne aka tayar ko kuma aka aiko Annabawa da Mursalai zuwa ga Mutane? Sai Imam (a.s) ya amsa da cewa: Domin ya kasance hujjar Allah madaukakin sarki ta cikka a kan Mutane bayan Ma'aika, kuma domin kadda su ce babu wani Ma'aiki ko mai gargadi da ya zo mana? Kuma domin ya kasance hujjar Allah a gare su, Shin ba ka ji fadar Allah madaukakin sarki cewa ba yayin da da yake Ambato hikayar masu tsaron jahannama da kuma jayayyarsu da Mutanan Wuta da Annabawa da kuma Ma'aika? Shin Ma'aika masu gargadi ba su zo muku ba? Sai su ce Eh! Hakika sun zo mana sai muka karyata su mu ka ce Allah bai saukar da komai ba hakika ku kuna cikin bata mai girma) masu saurare wannan hadisi mai albarka  yana ishara ne kan samuwar mai gargadi a cikin ko wata Al'umma domin ya cika hujjar Allah madaukakiya ga mabiyan gaskiya. Domin Lutufi da kuma tausayin Ubangiji ga bayinsa ya aiko Ma'aika da Masu gargadi zuwa ga ko wata Al'umma, kuma manufar wannan Al'amari, wani sananne ne, waninsa kuma ba bayyananne ba ne ya shafi Al'umma da kuma mutanan da aka aikawa ma'aikan, kamar yadda fadar Allah madaukakin sarki ta yi ishara cikin Suratu Nisa'I daga Aya ta 163 zuwa ta 165 Allah madaukakin Sarki na cewa:(Hakika Mun yi maka wahayi kamar yadda Muka yi wahayi ga Nuhu da (sauran) annabawa da suke bayansa, Muka kuma yi wahayi ga Ibrahimu da Isma'ila da Ishaka da Yakubu da 'ya'yansa da Isa da Ayuba da Yunusa da Haruna da Sulaimanu, Muka kuma bai wa Dawuda (littafin)Zabura*(Muka) kuma (aiko manzanni wadanda Muka ba ka labarinsu tun tuni, da kuma wasu manzanin da ba Mu ba ka labarinsu ba. Allah kuma ya yi Magana da Musa kai tsaye*Manzanni ne masu albishir (ga mumunai masu kuma) gargadi (ga kafirai) don haka hujja a gun Allah bayan (aiko) manzanni. Allah kuwa ya kasance Mabuwayi ne Gwani).

*************************Musuc***********************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,Hakika Hadisan iyalan gidan Anabta tsarkaka sun bayyana mana cewa  Hakika Wasu Annabawan Allah tsarkaka mai yiyuwa su kasance boyayyu ga mutanan su, amma duk da hakan suna sauke yaunin da ya rataya a kansu na Anabta daidai da fahimtar mutanansu, a cikin Tafsiru Ayyashi yardar Allah ta tabbata a gare shi an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(Ya kasance tsakanin Annabi Nuhu da Annabi Ibrahimu a kwai bayin Allah boyayyu domin haka ne ma aka boye sunansu a cikin Alkur'ani, ba a Ambato su ba kamar yadda aka Ambato wadanda suka bayyana daga cikin Annabawan Allah ba, kuma wannan shi ne fadar Allah madaukakin sarki(*(Muka) kuma (aiko manzanni wadanda Muka ba ka labarinsu tun tuni, da kuma wasu manzanin da ba Mu ba ka labarinsu ba. Allah kuma ya yi Magana da Musa kai tsaye)suratu Nisa'I Aya ta 164 ma'ana shi ne ban Ambato sunayen wadanda na boye kamar yadda na Ambato sunayen wadanda suke boye  daga cikin Annabawa ba) Masu saurare cikin wasu hadisan na daban kuma an bayyana yawan adadin Annabawa da wasiyansu, lamarin da yake karfafa amsar tambayar da ta gabata kamar  yadda muka Ambato a cikin ayoyin da suka gabata, misali cikin Littafin Basa'iru Darajat na babban  malamin hadisin nan shekh Assafar , an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce :(Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce farkon wasiyi da ya kasance a doron kasa shi ne Hibbatullahi bn Adam,kuma babu wani Annabi da ya gabata face ya nada Wasiyi, sannan sai Imam Bakir(a.s) yace ya kasance adadin dukkanin Annabawan Allah tsarkaka  dubu dari da dubu 24, biyar daga cikinsu su ne Ulu azm watau ma'abuta girma su ne Annabi Nuhu, Annabi Ibrahim, Annabi Musa, Annabi Isa da Annabi Muhamadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare su gaba daya, kuma Hakika Aliyu bn Abi Talib ya kasance Hibbatullahi ga Annabi Muhamadu, magajin Ilimin wasiyai, da kuma ilimin wadanda suka gabace shi, Kuma hakika Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka shi ne wanda ya ga ji ilimin wadanda suka gaba ce shi daga Annabawa da Mursalai) har ila yau cikin litattafan Khisal da Amaly na shekh Saduk, an ruwaito hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare su tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(Allah ya halicci Annabi dubu dari da dubu 24, kuma Nine mafi karamcin su a wajen Allah ba wai alfahari ba, kuma Allah ya halicci wasiyi dubu dari da dubu 24, wasiyi na kuma shi ne mafi karamcin su a wajen Allah da fifiko).

Masu saurare bayan karamto wadannan Nassosi, ya bayyana a gare mu cewa Hakika Allah madaukakin sarki bai bar wata Al'umma daga cikin Mutanan farko ku kuma na yanzu face an tayar mai gargadi daga cikin su daga cikin Annabawa da wasiyai da kuma suke shiryar da su zuwa ga hanya madaidaiciya da rayuwa mai kyau, domin cikar hujja a gare su.

*********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya jiki, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.