Babbanci tsakanin Annabawa da Ma'aika
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta Yau Mine ne babbanci tsakanin Annabawa da Ma'aika? Shin dukkanin Annabawa Ma'aikan Allah ne?, ko kuma dukkanin Ma'aika Annabawan Allah ne? kafin amsa wadannan tambayoyi bari mu saurari tanadin da aka yi mana a kan faifai?
*****************************Musuc******************************
Masu saurare, idan muka koma zuwa ga Alkur'ani mai girma za mu samu cewa ya siffanta Annabi da Ma'aiki a matsayin jakadun Allah madaukakin sarki kan bayinsa, sannan wasu daga cikin su suna hada dukkanin wadannan siffofi na Ma'aika da Annabawa kamar yadda ya zo cikin Suratu Maryam Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka Kuma ambaci (labarin) Musa cikin (wannan) Littafi (Alkur'ani). Hakika shi zababbe ne, Ya kuma kasance Annabi ( kuma) Manzo)Suratu Maryam Aya ta 51har ila yau cikin wannan surat mai Albarka Allah madaukakin sarki ya siffanta Annaabin Allah Isma'il da mai cika alkawari kuma Manzo, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Kuma Ka ambaci (labarin) Isma'ila a cikin (wannan) Littafi(Alkur'ani). Hakika shi ya zama mai cika alkawari ne kuma ya kasance Annabi (kuma) Manzo) suratu Maryam Aya ta 54 kamar yadda wasu Ayoyi masu albarka ke bayyana cewa Hakika Allah madaukakin sarki ya tayar da Ma'aiki ga ko wata Al'umma, kuma ya tayar da Manzo cikin ko wani gungu na Alkarya wacce ta hada Al'umma guda, a cikin Suratu Nahali Aya ta 36, Allah tabarka wa ta'ala ya ce:(Hakika kuma Mun aiko Manzo a kowacce al'uma cewa:" Ku bauta wa Allah, kuma ku nisanci shaidan. To akwai daga cikin ku wanda bata ya tabbata a kansu (har mutuwa), to ku yi tafiya a bayan kasa sai ku ga yadda karshen masu karyatawa ya kasance) har ila yau cikin suratu Kasasi Aya ta 59, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Kuma Ubangijinka bai zamanto Mai hallakar da alkaryu ba har sai ya aiko da Manzon a cikin manyan biranensu, yana karanta ayoyinmu. Kuma ba Mu kasance Masu hallaka alkaryu ba sai idan mutanansu sun zama azzalumai), masu saurare Masana Tafsiri sun bayyana cewa yayin da Allah madaukakin yake ambaton Alkarya wacce ta gumshi wani bangare na Al'umma, ba yana nufin Ummul kura wato garin Makka ba, da yake ambaton Ma'aiki da siffar Annabi ko mai gargadi. A cikin Suratu A'arafi Aya ta 94 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Kuma ba Mu (taba) aiko wani Annabi cikin wata Alkarya ba (da Mutananta suka karyata shi) sai Mun kama mutanen nata da tsanance-tsanance da cututuka don ko sa kaskantar da (kansu ga Allah)) har ila yau cikin suratu Saba'I Aya ta 34 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ba mu taba aiko wani mai gargadi cikin wata alkarya ba sai mawadatan cikinta sun ce:"Mu dai Masu kafirce wa abin da aka aiko ku da shi ne).Masu Saurare abinda za mu iya fahimta cikin wadannan Ayoyi masu albarka da suka gabata shi ne aikin Ma'aiki ya fi fadi da aikin Annabi, kuma Al'umma guda it ace wacce ta hada siffofi mabanbanta kuma ta kumshi Alkarya guda.kuma da wannan ma'ana zai bayyana cewa a yayin da za mu Ambato siffar Ma'aika, Ulul Azm watau ma'abota girma daga cikin Annabawa su waye ne su? A cikin shirin mu na gaba da yardar Allah.domin haka babbanci dake tsakanin Ma'aiki da Annabi, kamar yadda muka fahimta cikin wadannan Ayoyi masu albarka da suka gabata shi ne, Ko wani Ma'aiki yana iya kasancewa Annabi, kuma ko wani Annabi bai ya isa kasance Ma'aiki watau ko wani Ma'aiki Annabi ne ba kuma ko wani Annabi ba ne Ma'aiki kamar yadda muka fahimta a zahirin wadannan Ayoyi masu albarka da suka gabata.
***************************Musuc*************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran, ci gaban shirin zai koma kan hasken shiriya na biyu watau tafarkin iyalan gidan Annabta tsarkaka.inda za mu samu bayyanin dake bayyana babbanci dake tsakanin Ma'aika da Annabawa, da farko za mu fara da riwayar da shekh Kulaini ya ruwaito cikin Littafinsa Alkafi wacce aka ruwaito daga Zurara bn A'ayun jin kan Allah ya tabbata a gare shi, yayin da ya tambayi Imam Muhamad Bakir (a.s) dangane da fadar Allah madaukakin sarki na cewa (kuma ya kasance Annabi (kuma) Manzo) sai ya ce mine ne babbanci tsakanin Annabi da Manzo? Imam Bakir (a.s) ya amsa masa da cewa Annabi shi ne wanda yake karbar sakon Ubangiji a cikin barci kuma ya na jin sautin sakon yana farke, amma ba ya karba kai tsaye daga Mala'ika, shi kuma Ma'aiki shi ne wanda yake karbar sako ta hanyar sauraren sauti, da kuma cikin barci kuma yana karbar sakon kai tsaye daga Mala'ila amincin Allah ya tabbata a gare shi), cikin Littafin Basa'iru Darajat, shekhun malamin nan mai suna Assafar ya ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam bakir (a.s) ya ce:(Ma'aiki ko kuma Manzo shi ne wanda Mala'ika Jibrilu ya ke sauko masa ya gansa kuma ya yi Magana da shi, amma Annabi shi kuma shi ne wanda yake gani a cikin mafarki kamar yadda Annabi Ibrahimu ya gani a mafarki, kuma kamar yadda ya kasance Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka yana gani cikin barcinsa wasu dalilai na Annabtarsa kafin wahayi ya sauko masa har lokacin da Mala'ika Jibrilu ya zo masa da sakon Annabta daga wajen Allah madaukakin sarki) har ila yau cikin wani hadisi na daban da aka ruwaito daga shugabanin shiriya Imam Bakir da Imam Sadik amincin Allah ya tabbata a gare su , sun yi Karin bayyani fiye da hadisan da suka gabata dangane da tambayar shirin watau babbanci Manzo da Annabi, hakika ya zo cikin riwayar su cewa:(Annabawa da Mursalai su nada matsayi mababbanta guda hudu,Na farko a kwai Annabin da aka bashi Annabta amma kawai shi Annabi ne a karan kansa ba hujja ba ne ga waninsa, Na biyu a kwai Annabin da yake karbar sako a cikin barci kuma yana jin sautin sakon a farke amma ba a aiko shi zuwa ga wani ba kuma zai kasance ya nada shugaba kamar yadda ya kasance Annabi Ibrahimu (a.s) Shugaba ne ga Annabi Ludu (a.s), masu saurare abinda ake nufi a nan shi ne kafin a tayar da Annabi Ludu zuwa ga Mutanan sa ya kasance kalkashin jagorancin Annabi Ibarahimu (a.s) duk kuwa da ya kasance Annabin Allah daga bisani kuma Allah ya aike shi zuwa ga mutanansa, Na Uku kuma a kwai Annabin da yake gani a cikin barcinsa, kuma yake sauraren sautin sako kuma yana haduwa da Mala'ika a cikin barcinsa, sai kuma na Hudu shi ne Wanda yake gani a cikin barcinsa, yana kuma sauraren sauti a farke ya kuma hadu da Mala'ika kaba da kaba ya karbi sakon da ya zo masa da shi daga wajen Allah madaukakin sarki wannan shi ne Manzo ko kuma Ma'aiki, kuma shi ne Imami ko shugaba kamar yadda ya kasance Annabawa masu mikamin Ulul Azm, kuma Hakika Annabi Ibrahimu (a.s) ya kasance Annabi ne ba Imami ba har lokacin da Allah madaukakin sarki ya ce da shi Ni zan sanya ka Shugaba a kan Mutane) Masu Saurare a karshe abinda muke so mu yi ishara da shi a nan shi ne, wannan rarrabe-rarrabe da Imam (a.s) ya yi na matsayin Annabawa da Manzani yana fadakar da mu fadadar Rahamar Ubangiji ga dukkanin halitunsa.
*********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.