Wasu Annabawa Ne Ulul-Azm
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, kamar yadda muka yi bayyani a shirin da ya gabata tambayarmu ta Yau Wasu Ma'aika ne ake kira Ulul Azm kuma mine ne ya sanya Nassosi suka yi tabbaci a kansu? Amma kafin nan bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.
**********************Musuc*************************
Masu saurare, kamar yadda shrin ya saba ya kan neman amsar tambayar ne ta hanyar komawa kan haskaken shiriya biyu Littafin Allah watau Alkur'ani mai tsarki da kuma kalaman iyalan gidan Anabta amincin Allah ya tabbata a gare su, ba boyayyen abu ba ne ga ko wani musulmi cewa Kalmar (Manzani Ulul Azm ) Istilahi ne na Alkur'ani mai tsarki kuma hakika ya Ambato wannan istilahi so guda a Aya ta 35 cikin suratu Ahkafi, inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Sai ku yi hakuri kamar yadda Ulul Azmi watau manyan manzanni (masu karfin niyya da kauriya)suka yi hakuri, kadda kuma ka yi musu gaggawa. Kai ka ce su ranar da za su ga abin da ake yi musu alkawari ba su zauna ba (a Duniya)sai tashon sa'a daya (tak) na wuni.isar da aike ne, (naka) ba wanda za a hallaka sai fasikan mutane) abin fahimta cikin wannan Aya mai albarka shi ne daga cikin kebabbun siffofi na wannan bangare na Annabawa shi ne girman hakurinsu wajen isar da sakon Allah madaukakin sarki har suka zamanto abin koyi a hakan ga masu da'awa ko kira zuwa ga Addinin Ubangiji na gaskiya. Da wannan ma'ana za mu shaida cewa (Kalmar Azamul- Umur watau manyan al'amura) ta zo cikin Alkur'ani mai girma kadai ne kan masu dabi'ar hakuri, kamar fadar Allah madaukakin sarki:(Ba shakka za a jarrabe ku cikin dukiyoyinku da rayukanku, kuma ba shakka za ku ji cuta mai yawa daga wadanda aka bai wa Littafi a gabininku, haka kuma daga mushrikai. To, idan kuka yi hakuri kuka ji tsoron Allah, to hakika(yin) wancan yana cikin manyan al'amura) suratu Ali-imrana Aya ta 186, da wannan ma'ana aka ruwaito hadisi daga bangare makarantar nauyaye biyu, Hakika cikin tafsirin Aliyu bn Ibrahim Qummy da yake a matsayin babbab malami masanin hadisai na karni na uku bayan hijrar Ma'aikin Allah daga Makka zuwa Madina, a yayin da yake fassara Ayar da ta gabata ta cikin Suratu Ahkafi ya ce, kuma wadanda ake nufi da Manzanni Ulul Azmi su ne wadanda suka gabaci Annabawa da tabbaci ga Allah, suka yi Imani da dukkanin Annabawan da suka gabace ku da kuma wadanda za su zo bayansu kuma suka kasance masu niya mai karfi a kan hakuri duk da irin karyata su da kuma cutar da su da aka yi) Masu saurare abin fahimta cikin wannan hadisi da ya gabata shi ne a kwai falala ko kuma fifikon Mazanni ulul Azmi a kan sauren manzanni da Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su kuma hakika Risalar su ko kuma muce sakon da suka zo da shin a Litattafai da Suhuf hujja ce ga dukkanin Al'umma.a cikin Littafin Kamilil Ziyarat, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Sajjad Zainul-abidin (a.s) ya ce:(duk mai so Allah ya hada shi da Annabawa dubu 100 da dubu 24 to ya ziyarci kabarin babban Abdallah Imam Husain (a.s) a tsakiyar watan Sha'aban, domin a wannan lokaci ruhin Annabawan Allah amincin Allah ya tabbata a gare su za su nemi izini a wajen Allah madaukakin sarki na ziyarar sa sai a yi musu izini daga cikin su kuwa a kwai biyar masu mikamin Ulul Azmi, sai wanda ya ruwaito hadisin ya ce muka ce su wa nene Annabawa masu wannan mikami na ulul Azmi sai Imam (a.s) ya ce Annabi Nuhu, Annabi Ibrahimu, Annabi Musa, da Annabi Muhamadu amincin Allah ya tabbata gare su baki daya.sai Rawin ya ce:Muka ce masa mi ake nufi da ma'anar Ulul Azmi, sai Imam (a.s) ya ce wadanda aka aiko zuwa gabashin kasa da yammacinta, Aljanunsu da Mutanan Su).
*********************Musuc*****************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran, a ci gaban shirin za mu kawo muku wani gungu na Nassosi da suke tabbatar da cewa Manzanni Ulul Azmi su ne biyar din da aka Ambato cikin riwayar da ta gabata kuma wasu hadisan ma sun yi ishara da cewa su ne ma'abota shariar Ubangiji. Hakika cikin Littafin Uyunul Akhbaru Ridha, an ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Aliyu bn Musa Aridha (a.s) ya ce:(Hakika an sanya musu sunan Ulul Azmi, saboda Su sun kasance ma'abota girman niya da kuma shari'a, domin haka duk wani annabi da ya zo bayan Annabi Nuhu (a.s) har zuwa aiko da Annabi Ibrahimu (a.s) sun kasance bisa Shari'a, tafarki da kuma Littafin Annabi Nuhu (a.s), kuma ko wani Annabi da ya kasance a zamanin Annabi Ibrahimu(a.s) da kuma bayan sa zai kasance bisa shari'a, tafarki da kuma littafinsa (a.s) har zuwa Lokacin Annabi Musa (a.s) kuma haka zalika dukkanin Annabin da ya kasance a zamanin Annabi Musa (a.s) da kuma bayansa yana bisa shari'a, tafarki da kuma Littafinsa ne har zuwa Lokacin Annabi Isa Dan Maryamu (a.s), Kuma dukkanin Annabin da ya kasance a zamanin Annabi Isa (a.s) da kuma bayansa, yana bisa shari'a, tafarki, da kuma Littafinsa ne har zuwa lokacin da aka tayar da Annabinmu Muhamadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma wadannan su ne Manzanni biyar da ake kira Ulul Azmi watau ma'abota jimiri da dauriya kuma su ne mafi fifiko da falala daga cikin Annabawa da Manzani amincin Allah ya tabbata a gare su kuma shari'ar da Annabi Muhamadu (s.a.w.a) ya zo da ita ba ta kushewa ko canzawa har zuwa ranar Alkiyama, kuma babu wani Annabi bayansa har zuwa ranar Alkiyama). Masu saurare cikin wani hadisi na daban kuma ,an bayyana illa ta daban da ta sanya aka sanya Manzani hudu masu manyan shari'a da suka gabaci Annabinmu mai girma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka sunan Ulul Azmi, shi ne kasancewarsu sun gabaci Annabawa kulla alkawarin Ubangiji na taimakon karshen Annabawa da wasiyinsa amincin Allah ya tabbata a gareshi da garesu gaba daya.karin bayyani zai zo cikin wannan Nassi na Aya mai girma da kuma hadisan da suke Magana kan matsayin Annabawa (a.s) dangane da Risalar karshe ta karshen Annabawa (a.s), ba ri mu wadatu da wannan hadisin guda da aka ruwaito cikin Littafin Ilalu shara'I'I da Tafsirin Aliyu bn Ibrahim Qummy wanda suka ruwaito daga Jabir bn Yazid, yayin da ya tambayi Shugabanmu Imam Bakir (a.s) dangane da ma'anar fadar Allah madaukakin sarki:(Kuma Hakika Mun yi alkawari da (Annabi) Adamu tun kafin (ya ci bishiyar da aka hana shi) sai ya manta (alkawarin), sai ba mu same shi mai juriya ba) suratu Daha Aya ta 115. Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa Allah ya yi alkawari da shi a kan Muhamadu (s.a.w.a) da kuma wasiyansa bayansa sai ya bari bai kuma kasance mai dauriya a kan hakan ba, kuma su Annabawan da ake kira Ulul Azmi sun samu wannan suna ne domin an yi alkwari ne da su a kan Annabi Muhamadu (s.a.w.a) da kuma wasiyansa bayansa har zuwa Imam Mahadi da kuma tafarkinsa sai suka hada dauriyarsu a kan hakan ya kasance tare da tabbaci da shi).Masu saurare, takaicecciyar amsa da za mu iya fahimta a wadannan Nassosi masu albarka shi ne Manzani Ulul Azmi sune mafi fifiko da falala daga cikin Annabawa da manzanin Allah kuma adadin su biyar ne domin sune aka baiwa shari'a masu girma kuma an babbance su da hakuri gami da dauriya wajen isar da sakon Allah da kuma rikekkeniya wajen amincewa da alkawarin da Allah tabarka wa ta'ala yayi da su dangane da taimakon karshen Annabawa da wasiyansa bayansa har zuwa na karshen wasiyai Imam Mahadi amincin Allah ya tabbata a gare su gaba daya.
*********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.