Jan 28, 2017 05:31 UTC

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan g

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta Yau wasu siffofi ne suka kebanta da Annabawan Allah amincin Allah ya tabbata a garesu har Allah tabarka wa ta'ala ya zabe su a matsayin Annabawa?wannan tambaya nada mahimancin gaske a bangare tarbiya, amma kafin neman amsar tambayar bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.

**************************Musuc********************************

Masu saurare kamar yadda shirin ya saba , za mu fara da hasken shiriya na farko watau Alkur'ani mai tsarki, inda za mu ga cewa Ayoyi da dama sun bayyana cewa gaskiyar fuskantarsu  zuwa ga Allah da kuma kadaita shi, ikhlasi cikin bautar sa na daga cikin mahiman dabi'o'in da Allah madaukakin sarki ya ni'imta Annabawansa tsarkaka da su, misali cikin suratu Maryamu Aya ta 58 da kuma ta 59 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Wadannan su ne annabawa wadanda Allah Ya yi Ni'ima a gare su, daga Zuriyar Adamu, da kuma wadanda Muka dauko (a jirgin ruwa) tare da Nuhu, da kuma zuciyar ibrahimu da Isra'ila (wato Yakuba), da Kuma wadanda Muka shiryar da su Muka kuma zabe su.Idan ana karanta musu ayoyin (ubangiji) Mai rahama sai su fadi su yi sujjada suna kuka*Sai wasu suka maye gurbinsu bayansu wadanda suka watsar da salla suka kuma bi sha'awace sha'awacen (Duniya na sabo), to ba dadewa ba za su hadu da gayyu(watau wani kwari na azaba a Jahannama). Hakika su amincin Allah ya tabbata a gare su  masu kiyaye salla ne da kuma bautar Allah madaukakin sarki, Hakika kuma sun 'yantu daga kangi na cewa Nine, domin haka ne suka tsarkakku daga kiran Mutane na bauta musu suka kuma mayar da hankulansu baki daya wajen kiran Mutane zuwa ga Ibada domin ganin sun zamanto  Mukhlisan bayin Allah madaukakins sarki ,a cikin Suratu Ali-Imrana Aya ta 79 Allah Tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ba zai yiwu ba ga mutum idan Allah ya ba shi Littafi da Hikima da annabci sannan ya ce da mutane: "ku zama bayina ba na Allah ba, "Sai dai (ya ce): "Ku zama malamai na Allah saboda Kasancewarku kuna koyar da Littafin(Allah) kuna kuma masu karantar da shi) Masu saurare Isma na daga cikin mahiman siffofin Annabawa (a.s) da hukuncin kasancewar su jakadar Allah zuwa ga halitunsa da kuma masu isar da hukunce –hukuncensa zuwa ga Bayinsa, kamar yadda shugabanmu Imam Ridha (a.s) ya yi ishara inda ya bayyana dalili na hankali bisa hakan. Hakika Shekh Saduk cikin Littafinsa Ilalu Shara'I'I ya ruwaito Hadisi daga Imam Ridha (a.s) yayin da yake amsa tambaya kan illar wajabcin sanin Ma'aika da samun tabbaci da su da kuma yi musu da'a da biyayya ya ce:(A yayin da ya kasance tsakakin Halittu da Mutane babu wani da yake yi musu bayani kan abinda yake maslaha ne a gare su, kuma Hakika Mahalicci madaukaci ya Kasance yana son ganin maslahalar Al'umma, kuma su kuma watau Mutane rauninsu da kasawarsu sun kasa idrakin sa ko fahimtarsa  a zahiri, domin haka ya kasance dole ya tayar da ma'aiki da zai kasance wasila ko tsani tsakaninsa da su Mutanan, kuma ya kasance ma'asumi ma'ana wanda ba ya sabo kuma ba ya kuskure da kuma zai isar da Umarninsa da kuma Haninsa, kuma ya shiryar da su kan abinda yake amfani da maslaha a gare su kuma ya kare su da abinda zai cutar da su) har ila yau daga cikin tushen siffofin Annabawa, Hakuri wajen jurewa dukkanin wahalhalu na isar da sakon Ubangiji da kuma shiryar da Bayu, tare kuma da dogaro ga Allah madaukakin sarki a kan hakan, kamar Aya ta 11 da kuma ta 12 cikin Suratu Ibrahimu ke ishara da hakan, Allah madaukakin sarki ya ce:( Manzanninsu suka ce: 'Mu ba kowa ba ne in ban da mutane kamarku, sai dai Allah yana yin baiwa ga wanda  Ya so ne daga bayinsa, kuma bai kamata a gare mu ba mu zo muku da wata hujja sai dai da yardar Allah.Muminai kuwa lallai su dogara ga Allah kawai*kuma me zai hana mu mu dogara ga Allah, alhali kuwa hakika ya shiryar da mu hanyoyinmu? Lallai za Mu yi hakuri bisa irin cutar mu da kuke yi. Lallai kuwa masu dogaro su dogara ga Allah kawai) suratu Ibrahimu Aya ta 11 da kuma ta 12.

***************************Musuc**********************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, ci gaban shirin zai ci gaba da bayyani kan siffofin Annabawan Allah tsarkaka, Hakika cikekken hankali da kamalarsa da kuma mu'amala ta hankali wacce ta yi hanun riga da son rai da kuma bin zuciya na daga cikin tushen siffofin Annabawa Allah zababbu, kamar yadda shugabanmu Imam Kazim (a.s) ya yi ishara da hakan cikin hadisi da aka ruwaito cikin Littafin Almahasin, Imam (a.s) ya ce:( Hakika Allah bai tayar da wani Annabi ba face mai cikekken hankali, kuma wasu Annabawan sun fi wasu daukaka, kuma Annabi Souleimane bai gaji Ma'aifinsa Annabi Dawuda ba har sai da aka jarabci hankalinsa, Annabi Suleimane ya gaji Ma'aifinsa Annabi Dawuda yayin da yake da shekaru 13 a Duniya), a karshen wannan hadisi Imam Kazim (a.s) ya na ishara kan rashin tasiri na karamcin shekaru dangane da cikar kamalar hanakali na Annabawan Allah (a.s), Hakika su Allah ya hore wa wannan matsayi  sakamakon shirinsu da kudura da Allah madauakin sarki ya basu kamar yadda Annabin Rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya yi ishara cikin hadisin da aka ruwaito a Littafin Basa'iru Darajat, inda ya ce:( Mu Annabawa Idanuwanmu na barci amma zukatanmu na farke, kuma muna ganin abinda ke bayanmu kamar yadda muke ganin abinda ke gabanmu) har ila yau cikin Littafin Almahasin, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) yayin da aka tambaye shi ta yaya ya  san cewa Ma'aika, Ma'aika ne? sai ya amsa da cewa an yaye mana duk wani hijjabi muna ganin komai a hakikaninsa) daga cikin siffofin Annabawa kuma shi ne himmatuwa da neman arziki na Halali tsarkakekke,da kuma kaucewa duk wata Shubuha da dukkanin Nau'o'inta, abinda ake nufi da shubuha shi ne karyar da tayi kama da gaskiya, a cikin Littafin Amaly na shekh Tusy an ruwaito wani hadisi inda a cikin sa aka ce wani mutum a wajen Imam Sadik (a.s) ya bayyana cewa Ya Ubangiji Hakika Ni ina rokon ka da tsarkakekken Arziki, sai Imam (a.s) ya ce:Wannan abincin Annabawa ne). Takeicecciyar amsar da muka fahimta a cikin wadannan Nassosi masu albarka shi ne mafi mahimancin Siffofin Annabawa da Allah madaukakin sarki ya zabe su a matsayin Annabawa shi ne kamala da kuma cikakken hanhali, ikhlasi ga Allah,Hakuri wajen shiryar da Bayinsa da kuma isar da Umarninsa da kuma sakonsa, gami da dogaro ga Allah tabarka wa ta'ala a kan hakan, da fatan Masu saurare Allah madaukakin sarki ya arzuta mu da wadannan kyawawen siffofi dan albarkar riko da Wulayar Annabi Muhamadu da kuma iyalan gidansa amincin Allah ya tabbata a gare su gaba daya.

*********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya jiki, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.