Jan 28, 2017 05:34 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta yau it ace shin dukkanin Annabawa na da matsayin Imamanci da Allah madaukakin ya sanya ga Annabi Ibrahimu Halilu-Allah (a.s)? kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.

*******************************Musuc************************

Masu saurare, kamar yadda shirin ya saba, za mu fara da Littafin Allah mai girma inda wasu daga cikin Ayoyi masu girma suke ishara kan sanya Annabi Ibrahimu Halilu-Allah (a.s) a matsayin Imami, a cikin Suratu Bakarat Aya ta 124 ta yi ishara  kan wannan mahimin matsayi na sanya Khalilu-Rahaman ga Mutane Imami ko kuma Shugaba, kuma hakan ya kasance a karshen shekarunsa masu albarka (a.s), inda kuma ya nemi wannan matsayi ga Zuciriyarsa, kuma sanannan abu shi ne Annabi Ibrahimu (a.s) bai samu arzikin 'ya'ya ba sai ya kasance Lattijo mai yawancin shekaru kamar yadda Nassi Alkur'ani mai girma ya yi ishara cikin hikayar sa ta karbar bakunci Mala'ikun Allah (a.s)  kafin daga bisani su fice zuwa ga Mutanan Annabi Ludu (a.s) domin su saukar da azaba a gare su.a cikin Suratu Bakarat Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ku tuna Lokacin da Ubangijin Ibrahimu ya jarrabe shi  da wasu kalmomi sai ya cika su, ya ce da shi: Ni zan sanya Ka Shugaba a kan Mutane, (Sai Annabi Ibrahimu) ya ce"har ma daga cikin Zuriyata. "(Allah) Ya ce Azzalumai ba za su samu alkawarina ba.) suratu Bakara Aya ta 124.idan kuma muka koma kan hasken shiriya na biyu watau tafarkin Annabi Muhamadu da kuma na iyalan gidansa amincin Allah ya tabbata a gare su za mu samu hadisai masu yawa da suke bayyanin cewa matsayin da Annabi Ibrahimu ya samu na Shugabanci ya biyo bayan cin jarrabawa ce da ya ci,a cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Bakir (a.s) ya ce:(Hakika Allah madaukakin sarki ya riki Annabi Ibrahimu Bawa kafin ya rike shi Annabi, kuma ya rike shi Annabi kafin ya rike shi a matsayin Ma'aiki, ya kuma rike shi ma'aiki kafin ya rike shi aboki, ya kuma rike shi aboki kafin ya rike shi Shugaba, yayin da ya hada wadannan ababe, sai ya ce masa Ya Ibrahimu NI zan sanya ka Shugaba a kan Mutane, da wannan matsayi na Shugabanci yayi girma a idanuwan Annabi Ibrahimu (a.s) sai ya ce Ya Ubangiji har ma daga cikin Zuriyata. "(Allah) Ya ce Azzalumai ba za su samu alkawarina ba).A cikin Littafin Basa'iru Darajat, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) yana bayyanin cewa matsayin Imamanci ko shugabanci ya fi martaba da matsayin Wulaya na waliyan Allah madaukakin sarki yayin da yake fadar cewa:(suna inkarin Shugaban da aka wajabta yi masa Da'a ko biyayya kuma suna jayayya da shi,Na Rantse da Allah babu wani abu a doron Kasa da ya fi girman matsayi a wajen Allah da Imami ko shugaban da aka wajabta yi masa Da'a, Hakika kuma Annabi Ibrahimu ya kasance tsahon lokaci yana nema kuma yana girmama wannan matsayi har Allah madaukakin sarki ya ce masa NI zan sanya ka Shugaba a kan Mutane, Annabi Ibrahimu ya san wani matsayi ya nada falala sai ya ce: har ma daga cikin Zuriyata), a wani hadisi na daban kuma da aka ruwaito cikin Littafin Basa'iru Darajat Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya yi bayyani kan matsayin Annabawan Allah tsarkaka yana mai cewa:(shi kuma imami koShugaba ne kamar Ulul-Azam., kuma Hakika Ibrahim ya kasance Annabi ba Imami ba har lokacin da Allah ya ce Ni zan sanya ka Shugaba ga Mutane sai ya ce Ya Ubangiji har ma daga cikin Zuriyata. "(Allah) Ya ce Azzalumai ba za su samu alkawarina ba, watau wanda ya taba bautar gumki ko kuma ya yi sujada ga wanin Allah ba za su samun wannan matsayi na Imamanci ba) abin fahimta a wannan hadisi shi ne hakika Ma'aika Ulul-Azmi sun  kasance su nada matsayin Shugabancin mutane daga wajen Ubangijinsu  kuma ba dukkanin Annabbawa ne  dake matsayin  Ulul Azmi amincin Allah ya tabbata a gare su.

**************************Musuc***********************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,ci gaban shirin zai fara da riwayar da shekh kulaini ya ruwaito cikin Littafin kafi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) inda ya ce: (Shugabanimn Annabawa da Mursali biyar su ne Ulul-azmi daga cikin ma'aika kuma gare su wahayi ke kai kawo, sune Nuhu, ibrahimu, Musa,Isa da Muhamadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare su tare da iyalan gidansu da kuma dukkanin Annabawan Allah tsarkaka),Masu suarare, idan muka yi nazari a Aya ta 124 cikin suratul-bakara da ta gabata, Hakika Allah tabaraka wa ta'ala da hikimar sa ta daukaka ya sanya Khalilinsa Ibrahimu (a.s) ga Mutane Shugaba bayan da ya jarraba shi da kalmomi da kuma Umarni wanda daga cikin su akwai Umarnin yanka Dansa Isma'il (a.s) kuma hakika wannan ibtila'I ne mai girma kamar yadda Alku'ani mai girma ya bayyana cikin Aya ta 106 na Suratu Safati, watau hakika Allah madaukakin sarki ya saka masa bisa girman meka wuyan da ya yi na umarninsa inda ya sanya shi ga Mutane Shugaba, kuma meka wuya a wannan martaba na daga cikin mafi daukaka na fiskokin Ibada khalisa ga Allah madaukakin sarki, da wannan kuma zai bayyana gare mu girman martaba na Imamincin Ubanmgiji da ya kebbance wasu daga cikin Annabawansa da shi sannan kuma ya sanya sauren Ma'asumai wadanda ba sa sabo ko kuma kuskure wajen isar da sakon Ubangiji ga Al'umma daga zuciyar Annabi Ibrahim har zuwa ranar Alkiyama wacce ta ci gaba har zuwa Shugaban Annabawa da Halittu gaba daya da kuma Limamai 12 daga Zuriyarsa amincin Allah ya tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka.cikin wani dogon Hadisi da aka ruwaito cikin Littafin Kafi, a wannan fakara Shugabanmu Imam Ridha (a.s) na cewa:( Hakika Imamanci ko kuma Shugabanci girmanta, matsayinta da kuma sha'aninta ya daukaka da Hankulan Mutane, ba  za su fahimci girma da kuma matsayinta,ko kuma su cimmata da ra'ayinsu, ko kuma su tsayar da Imami ta hanyar zabinsu, Hakika Imamanci Allah tabaraka wa ta'ala ya kebe Khalilinsa Annabi Ibrahimu da Imamanci bayan Anabta da kuma daukaka shi zuwa ga matsayi na uku da kuma falala da ya albarkace da ita, ya kuma shiryar da shi zuwa ga ambatonsa har ya ce Ni zan sanya ka ga Mutane Shugaba, kuma wannan shugabanci ba ya kushe ga zuriyarsa har zuwa Ma'aikin Allah (s.a.w.a), kuma wannan matsayi ya kasance tsarkakekke  a gare shi har sai da Imam Ali (a.s) ya gaje shi daga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) bisa Umarnin Allah kuma ga kasance ga zuriyarsa zababbu da Allah ya basu Ilimi da Imani).Takaicecciyar amsar tambayar mu ita ce Imamanci ko kuma Shugabanci shi matsayi ne da Allah ya sanya shi ga Shugabanin Annabawa daga cikin Ma'aika, su ne Ulul Azmi kuma ya sanya shi bayan Annabi Ibrahimu Khalilullah (a.s) ga Ma'asumai daga Zuriyarsa sannan zuwa ga zuriyar Annabi Muhammadu (s.a.w.a) har zuwa Ranar Alkiyama.

*************************Musuc******************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.