Jan 28, 2017 05:38 UTC
  • Misdakin Taimakon Annabawa ga Manzon Allah

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta yau ita ce minene Misdaki na taimakon Annabawan da suka gabata ga cikamakin su Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka?kafin amsa tambayar bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.

***************************Musuc**********************************

Masu saurare, shirin na yau zai fara da Aya ta 81 cikin Suratu Ali-Imrana,inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(kuma (ka tuna) lokacin da Allah ya dauki alkawari daga Annabawa cewa : Lallai abin da Na ba ku na Littafi da hikima sannan wani Manzo ya zo muku mai gaskatawar abin da yake tare da ku, to lallai ku ba da gaskiya da shi, kuma lallai ku taimake shi.Sai ya ce:" kun yarda, kuma kun dauki alkawarina bisa wancan?" sai suka ce:"Mun yarda.sai ya ce:'To ku shaida Ni ma ina tare da ku daga (cikin) masu shaida) hakika maliman tafisiri sun ruwaito hadisai da dama dangane misdakin wannan taimakon da Annabawan Allah (s.a.w.a) suka dauki alkawari da Ubangiji, shi ne taimakon Annabawa (a.s) ga Annabi Muhamadu (s.a.w.a) da kuma da'awarsu zuwa ga na bayanasu kan su yi imani da zuwansa kuma su taimaka ma shi. Wannan Misdaki mun yi bayyani kansa a Shirin da ya gabata, kuma Nassosin da muka Ambato sun yi mana bayyani kan kiran da Annabawan da suka gabata suka yi ga magoya bayan su  na su yi biyayya ga Annabin Rahama tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa ga wanda ya riske sa, kuma a wannan kira a kwai shiriya a gare sun a imani ga Shugaban Annaba (a.s) kuma taimaka masa a kwai rabauta mai girma ta samun daukaka da shiriya ga hanya madaidaiciya. Kuma kamar yadda yake a bayyane  wannan misdaki shi ne jin kan ubangiji na yin Imani da Addinan Annabawan da suka gabata, baya ga hakan a kwai misdaki na daban shi ne Alkawarin da Annabawa suka dauka na a matsayin jin kan Ubangiji ga Annabawan da suka gabata.Babban Malamin Tafsiri Aliyu bn Ibrahim cikin tafsirinsa mai suna tafsirul-qummy ya ruwaito wani hadisi mai mahimanci daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) da yake bayyani kan Tafsiru Ayar Misak inda a cikin say a hadaAyoyi guda biyu sannan kuma ya fitar da sakamako dangane da wadannan Ayoyi masu albarka,  sune Aya ta biyu wajen daukan alkawarin  Ayar da Allah madaukaki sarki ya yi ga Annabawansa tsarkaka wacce ta zo cikin suratul-Ahzabi kuma wannan Aya sananniyar Aya ce da ake kira da Ayar Alkawarin da Allah tabaraka wa ta'ala ya dauka daga Halittu tun daga Alamu Zar, Aya ta farko ita ce Aya ta 7 cikin Suratul-Ahzabi inda Allah madaukakin sarki ke cewa :(Kuma (ka tuna)lokacib da Muka riki alkawura daga Annabawa (na isar da aike) kuma daga gare ka, kuma daga Nuhu da Ibrahimu da Musa da Isa dan Maryamu, Muka kuma riki Alkawari mai kauri daga gare su) afin fahimta a wannan Aya mai labalka shi ne wannan Umarni na Ubangiji da ya  umartar Annabawa su taimakawa na karshen su mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka bai takaita ga wasu kadai ba, domin ya shafi waninsu har ma da shi kansa Annabi Muhamadu (s.a.w.a) ya dauki wannan alkawari, Aya ta biyu kuma ita ce ta Alamu Zar inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Kuma(ka tuna)lokacin da Ubangijnka ya fiddo zuriyar 'yan Adam daga tsatsonsu,ya kuma sa su suka yiwa kansu shaida,(ya ce da su): Yanzu ba Ni ne Ubangijinmu ba? Suka ce: Ba Ja, (kai ne Ubangijinmu),mun shaida".(Mun yi haka ne) don kada ku ce a ranar Alkiyama:Hakika mu ba mu da masaniya a wannan) suratu A'arafi Aya ta 172 masu saurare hakika hadisai da dama sun bayyana cewa wannan alkawari an dauke shi ne a Alamu Zar ga dukkanin halittu da ya gumshi bisa kan Imani da rububiyar Allah madaukakin sarki da kuma anabta cikamakin Annabawa da yin wulaya ga wasiyansa 12 amincin Allah su tabbata a gare su baki daya.

**************************Musuc******************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta iran dake nan birnin Tehran, bayan saurare bayan bayyani daga wadannan Ayoyi masu albarka Shugabanmu Imam Sadik (a.s) ya bayyana cewa:(Babu wani Annabi da aka tayar wanda ya fito daga tsatson Annabi Adamu sai da ya dawo Duniya  ya taimaki Shugaban Mumunai (a.s) kuma shi ne ma'anar fadar Allah madaukakin sarki (to lallai ku ba da gaskiya da shi) ana nufin  ma'aikin Allah (s.a.w.a) kuma (lallai ku taimake shi)watau Shugaban Mumunai (a.s)  sannan kuma ya ce musu a cikin Duniyar Zar ko kuma Alamu Zar (kun yarda, kuma kun dauki alkawarina bisa wancan?) watau Alkawari sai suka ce mun dauka, Allah ya cewa Mala'ikai ku shaida Ni ma ina tare da ku daga cikin masu shaida.wannan shi ne ma'anar daukan misaki ko alkawari daga wajen Anabawa a Alamu Zar sannan sai Imam (a.s) ya ci gaba da bayyana dalili da Ayar dake cikin suratu Ahzabi wacce ta gabata kan abinda ake nufi da Taimako , Taimakon Shugaban Mumunai (a.s) sai ya ce:wannan da kuma Ayar da ta gabata cikin Suratul-Ahzabi na fadar Allah madaukakin sarki (Kuma (ka tuna)lokacib da Muka riki alkawura daga Annabawa (na isar da aike) kuma daga gare ka, kuma daga Nuhu , kuma da Ayar Kuma(ka tuna)lokacin da Ubangijnka ya fiddo zuriyar 'yan Adam daga tsatsonsu , hakika wadannan Ayoyi guda uku sun zo cikin surori guda uku na Alkur'ani mai girma), Masu saurare hakika Shekh Mufid cikin Littafin Khasa'is an ruwaito hadisi daga Abi Saeed Khudry ya ce:(Na ga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka kuma na ji shi yana fadar cewa (Ya Ali babu wani Annabi da Allah madaukakin sarki ya tayar ya kira shi zuwa wulayarka) bayan wadannan bayanai tambayar da za ta biyo baya it ace ta yaya za mu tabbatar da taimakon cikamakin Annabawa Manzon Rahama da kuma wasiyinsa amincin Allah ya tabbata a gare su gaba daya?Wannan shi ne abinda zai tabbata a zamanin bayyanar karshen wasiyan Annabi Muhamadu, Mahdi da muke jira Allah ya gaggauta bayyanarsa , kuma wannan shi ne abinda Shugabanmu Imam Sadik (a.s) cikin hadisin da aka ruwaito cikin Tafsirin Aliyu bn Ibrahim kalkashin fasarar Aya ta 51 cikin Suratu Gafir inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Hakika mu lallai za mu taimaki manzanninmu da kuma wadanda suka ba da gaskiya a rayuwar duniya da ranar da shaidu za su tsaya) sai Imam (a.s) ya ce wannan wallahi ya kasance ga Raja'a ne watau zamanin zuhurin Imam Mahadi (a.s) shin ba ku san cewa ba mafi yawan Annabawa bas u ci nasara ba a nan Duniya aka kasha su da kuma Shugabani imamam Bayan su an kashe su ba tare sun ci nasara a wannan Duniya ba? Wannan shi ne tabbatuwar wa'adin Ubangiji na Nasarar shi a Raja'a.

*******************Musuc*********************88

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.