Shin Annabawa Ma'asumai ne?
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta Yau Shin dukkanin Annabawa Ma'asumai ne? idan sun kasance Ma'asumai ta yaya Annabin Allah Musa (a.s) ya ce NI ne mafi sani daga cikin Mutane sannan kuma Allah ya yi masa wahayi a kan sabanin tunaninsa ya kuma tura masa bawan Allah nan Khadaru? Kuma haka yanayin ya kasance tare da Annabin Allah Yunus (a.s) shin Ismar Annabawan Allah (a.s) ya fi karfi ko kuma Ismar Iyalan gidan Annabta (a.s)? a hakikanin gaskiya wadannan tambayoyi misalai ne na tambayoyi da dama dake yawo cikin kwakkwalan Mutane? Amma kafin shiga cikin shirin bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.
**************************Musuc*********************************
Masu saurare, kamar yadda shirin ya saba, mu kan komawa kan haskaken shiriya guda biyu domin samun tambayar da muka bijiro da ita, da farko idan muka koma kan hasken shiriya na farko watau Alkur'ani mai girma za mu samu cewa fadar Alkur'ani mai tsarki ta bayyana cewa Hakika Shaidan ba zai iya batar da bayin Mukhlisai ba domin sub a zai yiyu su fada cikin sabo ba ta hayar batan Shaidan kamar yadda wadannan Ayoyi masu albarka su ka bayyana, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Sai ya ce: "Na rantse da girmanka lallai zan batar da su baki daya *Saidai bayinka wadanda aka tsarkake daga cikinsu) Suratu Sad Aya ta 82 da kuma ta 83. Wata Ayar ta daban kuma ta siffanta wasu Annabawa da cewa suna cikin Mukhlisai, misali cikin suratu yusuf Aya ta 24 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce :(………Kamar haka (Muka nuna masa hujjar) don Mu kawar da mummunan aiki da barna daga gare shi.Hakika shi yana daga bayinmu na gari) a cikin Suratu Maryamu Aya ta 51 Allah tabaraka wa ta'ala daga bakin Annabi Musa (a.s) ya bayyana cewa:( ka kuma ambaci (labarin) Musa cikin (wannan) Littafi(Alkur'ani). Hakika shi zababbe ne, ya kuma kasance Annabi (kuma) Manzo) domin haka Annabawan Allah amincin Allah su tabbata a gare su suna cikin bayin Allah Mukhlisai da Shaidan ba zai iya galaba gare su wajen batar da su da kuma jefa su cikin sabon Allah madaukakin sarki, kamar yadda Alkur'ani ke bayyana cewa Hakika Su basa fadar komai dangane da Allah tabaraka wa ta'ala face gaskiya, Hakika su Ma'asumai ne a wannan bangare, Allah madaukakin sarki na cewa:(Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffanta (shi da shi)*sai dai bayin Allah wadanda aka tsarkake) suratu Saffati Aya ta 159 da kuma ta 160. Wannan Aya mai Albarka ta tabbatar da tsarkakar Annabawan Allah (a.s)sakamakon ikhlasin su ga Allah madaukakin sarki suka samu wannan matsayi na Isma, Wannan shi ne abinda Ayoyi na 45 zuwa na 47 cikin suratu Sad suka yi ishara da shi,inda Allah tabaraka wa ta'ala ya bayyana cewa ambaton Allah da kuma Ranar Lahira da Annabawan Allah (a.s) key i wajen fuskantar Allah da ikhlasi gare shi madaukakin sarki, sakamakon wannan aiki na su kuma shi ya sanya aka zabe su a matsayin Annabawa da kuma kare su daga yin sabo, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Ka kuma tuna bayinmu Ibrahimu da Ishaka da Yakubu ma'abota karfi da basira*Hakika Mun tsarkake su da tsananin tuna Lahira*Kuma Hakika su a wurinmu suna daga cikin zababbu nagari) Suratu Sad daga Aya ta 45 zuwa ta 47.Masu saurare, da wannan Ma'ana ne Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) cikin bayaninsa na dalilin da Annabi Yusuf (a.s) ya sanya shi kaucewa sabon Allah madaukakin sarki, Hakika ya zo cikin Tafsiri Majma'ul Bayyan na Allama Tabrasi, Imam Sadik (a.s) ya ce Hujja ko kuma dalilin shi ne Anabta wacce ke hana aikata Alfahasha, da kuma Hikima dake kiyaye Mutum aikata Mumuna.
*****************************Musuc************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, Hakika Hadisin da ya gabata ya nuna cewa Anabta a karan kanta tana a matsayin Isma ga Annabawa (a.s) watau tana hana hana su aikata Alfahasha da sabo saboda ta gumshi Hikimar dake haskaka Basirar Mutum ta sanya yana ganin hakikanin ko wani mumuna ya kuma kaurace masa , kamar yadda Shugabanmu imam Sadik (a.s) ya bayyana a hadisin da ya gabata, kuma Hakika Ayoyi da dama sun Bayyana cewa Allah tabaraka wa ta'ala ya baiwa Annabawansa wannan Hikima da take kiyaye su daga aikata duk wani sabo kuma wannan Alheri mai yawa kamar yadda ya wassafa ta. Misali cikin Aya ta 81 na suratu Ali-Imrana Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuma (ka tuna) lokacin da Allah ya dauki alkawari daga Annabawa cewa:Lallai abin da Na ba ku na littafi da hikima sannan wani manzo ya zo muku mai gaskatawar abin da yake tare da ku, to lallai ku ba gaskiya da shi, kuma lallai ku taimake shi, sai y ace: ku yarda kuma ku dauki alkawarina bisa wancan? Sai suka ce: Mun yarda Sai ya ce:" To ku shaida Ni ma ina tare da ku daga (cikin) masu shaida). Don haka masu Saurare Alkur'ani mai girma ya sarraha Ismar Annabawa (a.s) saboda shirin sun a zati da ya hade da Ikhlasinsu ga Allah madaukakin sarki, da kuma tabbaci na Ubangiji suke gane hakikanin Komai suna fahimta mumuna na Sabo su kuma kaurace masa saboda Ikhlasinsu ga Allah da kuma tunanin Lahira da Ranar Hisabi.
Wannan Shi ne abinda muka fahimta da bayananu na Ayoyin Alkur'ani mai girma kuma bisa tushensa ya kamata mu fahimci Ayoyi mutashibihai bisa bayyanonin Ayoyin da suka gabata kamar yadda ya zo cikin Kissatu Yunus (a.s) da kuma kissar Annabi Musa (a.s), kamar yadda kuma ya kamata mu fahimci wadannan Ayoyi mutashihai bisa Asasin Zatin Annaban Allah tsarkaka na nisantar mumuna da kuma tabbacin Ismar su kamar yadda ya zo a cikin Al'kur'ani mai tsarki da Hadisan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare kuma da na iyalan gidansa tsarkaka.
*******************Musuc*********************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.