Feb 02, 2017 09:20 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta Yau mine ne farkon abinda ya wajabta muyi I'itikadi da shi dangane da cikamakin Annabawa Muhamadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka? Wannan tamabaya nada mahimancin gaske amma kafin amsa ta bari mu saurari tanadin da aka yi mana kan faifai.

**************************Musuc***************************

Masu Saurare kamar Shirin ya sabawa ya kan komawa kan haskaken shiriya biyu domin samun amsar da muka bujiro da ita, idan muka koma hasken shiriya na farko watau Alkur'ani mai girma za mu ga cewa yana karfafa wajibcin yin imani da Muhamadu Dan Abdullahi (s.a.w.a) kan cewa shi ne cikamakin Annabawa da Annabawan da suka gabata amincin Allah ya tabbata a gare su suka bayar da busharar sa, kuma mahimancin I'itiki da kuma imani da wannan Al'amari shi ne ya wajabta ga dukkanin 'yan adam daga Adinai daban-daban yin imani da shi da yi masa biyayya, bayan da Litattafansu ya Ambato Siffofin cikamakin Annabawa , kuma wannan Siffofi babu ga wani mahluki da suka tabbata kansa face Nabiyil-Ummuyi amincin Allah ya tabbata gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, A cikin Suratu A'afafi Allah madaukakin sarki ya ce:((Su ne) wadanda suke bin Manzo Annabi Ummiyi wadanda za su same shi a rubuce a gurinsu cikin Attaura da Linjila, yana umartar su da aikin alheri yana kuma hana su ga yin mugun aiki, yana kuma halatta musu mugun aiki, yana kuma halatta musu (abubuwa) tsarkaka yana kuma haramta musu najasa, yana kuma sauke musu nauye-nauyensu da hukunce-hukuncen da suka kasance a kansu.Saboda haka, wadanda suka ba da gaskiya  da Shi, suka kuma taimake shi, suka kuma bi hasken da aka saukar a tare da shi, to wadannan su ne marabauta) Suratu A'arafi Aya ta 157. Hakika Shugabanin Shiriya daga Iyalan gidan Anabta tsarkaka sun kafa dalili wajen tabbatar da Anabtar cikamakin Annabawa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka na Nassosi da dama daga cikin Litattafan Attaura da Injila, kuma wannan ya kasance musababbin yin imani  na mutanan da suka yi jayayya  da su daga cikin Malimam sauran Addinai, inda akalla suka tabbatar musu da sahihancin dalilansu. Kamar yadda aka ruwaito hadisai da dama da Allama Tabrasi ya tattaro su cikin Littafin Al-Ikhtijaj daga Shugaban Mumunai Aliyi bn Abi Talib da kuma Imam Kazim da Imam Ridha amincin Allah ya tabbata a gare su gaba daya.A cikin Alkur'ani mai girma a kwai fadakarwa da dama dangane da Siffofin cikamakin Annabawa (s.a.w.a) cikin Littatafan da aka saukar daga Sama da suka suke Magana a bayyane dangane da hakan, ta yadda kuma babu yadda  maliman Yahudu da Nasara za su yi inkari wajen dabbaka su a kan Annabi Muhamadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, domin haka ne ma suka kwanmace su boye wadannan Siffofi, saboda kafircin da suke da shi na Annabatar Annabi Muhamadu(s.a.w.a) A cikin Suratu Bakara Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Wadanda Muka bai wa Littafi sun san shi (watau Annabi Muhammadu) kamar yadda suka san 'ya'yansu, Hakika kuma wasu Jama'adaga cikinsu suna boye gaskiya, alhali suna sane(da cewa gaskiya ce) suratu Bakara Aya ta 146, har ila yau cikin wannan Surat mai albarka Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuma Lokacin da Littafi ya zo musu daga wajen Allah, wanda yake gaskata abin da yake tare da su(sai suka yi muso bayan ) a da can kuwa sun kasance suna neman nasara a kan wadanda suka Kafirce. Lokacin da abin da suka sani yazo musu (sai) suka kafirce da shi, to tsinewar Allah ta tabbata a kan kafirai) suratu Bakara Aya ta 89, har ila yau a wani bangare na wannan Surat Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Lokacin da Manzo ya zo musu daga wajen Allah mai gaskatawar abin da yake tare da su (Attaura) sai wasu Jama'ar wadanda aka bai wa Littafi suka yi jifa da Littafin Allah can bayan bayansu, kai ka ce ba su san (Littafin) ba) suratu bakara Aya ta 101.

***************************Musuc*********************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa Shirin na karamin sanin Kunkumi na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,Malimam Tarihi, kamar yadda aka kawo cikin Tafsirin Aliyu bn Ibrahim Alqummy yardar Allah ta tabbata a gare shi an ce Umar bn Khatab ya tambayi Abdullahi bn Salam shi daya daga cikin Malimam Yahudawa ne na Garin Madina: Shin kun san Muhamadu a cikin Littafinku? Wannan Malimi na Yahudawa ya amsa masa da cewa Na'am wallahi mun san shi a kan siffofin da Allah ya siffanta shi ,idan mun ganshi a cikin su kamar yadda dayanmu ya san dansa a yayin da ya gansa tare da Bayi, wanda yake wannan rantsuwa shi ne bn Salam, domin ya ce sanin da ya yiwa Annabi Muhamadu (s.a.w.a) ya fi sanin da yayi kowa daga cikin sahabai kamar yadda Umar ya bayyana. A cikin Littafin Khisal na Shekh Saduk, an ruwaito Hadisi mai tsaho daga Shugabanmu Imam Mujtaba (a.s), inda a cikin sa aka ce wani gungun Jama'a daga Yahudawa sun je wajen Ma'aikin Allah (s.a.w.a) sai suka tambaye shi wasu ababe , a yayin da suka fahimci gaskiya sai suka yi imani da shi. Kuma a wannan lokaci sai wani malamin yahudawa ya fitar da farar takarda wacce a cikin ta a kwai dukkannin ababen da Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya basu Labari a rubuce sannan kuma ya ce:(Ya Ma'aikin Allah, Na rantse da wannan ya aiko da gaskiya, ba muyi kofin wannan Labari ba a wani wuri face cikin Allunan da Allah madaukakin sarki ya rubuta ga Annabi Musa Dan Imrana (a.s), kuma Hakika na karanta falalarka cikin Littafin Attaura har saida na yi shakka  da shi, kuma hakika na kasance idan goge sunanka tun shekaru 40 da suka gabata, kuma duk Lokacin da na shafe, idan na sake komawa sai in same a tabbace kamar yadda yake a baya, kuma Hakika na karanta cikin Littafin Attaura wannan tambayoyin da muka yi maka babu mai amsa su face kai, kuma a Lokacin da kake amsa wadannan tambayoyi zai kasance a kwai Mala'ika Jibrilu a gefen ka na dama, da kuma Mala'ika Mika'ilu a gefenka na hakum, kuma wasiyinka a gabanka. Sai Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce ka yi gaskiya wannan Mala'ika Jibrilu ne a gefena na dama kuma wannan Mala'ila Mika'ilu ne a gefena na hakum, kuma wannan Shi ne wasiyina ko kuma mu ce Khalifa Aliyu bn Abi Talib(a.s) a gaba na, sai wannan Bayahude yayi Imani kuma ya kyautata Imaninsa) Masu Saurare takaicecciyar amsar da su mu fahimta a cikin wannan shiri shine  farkon abinda ya wajabta gare mu yin imani da Masoyin Allah Mustapha tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka kasancewarsa wanda Annabawan Allah (a.s) da suka gabata suka yi bushara da zuwansa  kuma hakika shi ne wanda Allah tabarka wa ta'ala ya sanar da siffofinsa da kuma alamominsa a cikin Littatafan da aka saukar daga sama wanda wannan siffofi ba za sa tabbatuwa kan ko wani mahluki face Shi (s.a.w.a).

*********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya jiki, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.