Busharar Zuwan Cikamakin Annabawa
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a Shirin da ya gabata mun kawo muku wasu jerin Nassosi da suke bayyani dangane da farkon abinda ya wajabta muyi I'itikadi da shi na cewa Hakika Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka shi ne Annabin da Littatafan da aka saukar daga sama suka yi albashir da shi doimn shakka babu siffofi da suka Ambato ba sa tabbatuwa ga ko wani mahluki face shi (S.A.W.S)kuma wannan shi ne abinda tarihi ya gaskanta kuma babu wani da yayi da'awar sabanin hakan, wannan wani sirri ne da ya kalubalanci wadanda ba su yi Imani da shi ba, daga cikin maliman Yahudawa da Nasara da sauransu daga cikin masu jayayya wajen yin inkari da Anabtar (S.A.W.S) da kuma yadda suke kokari wajen boye wannan bishara da juya fassarar wani bangare nata a cikin Littafinsu, a nan tambayarmu ita ce shin Busharar zuwan cikamakin Annabawa (s.a.w.s) ya takaita a kan sananun Addinai ko kuma ya shafi dukkanin Annabawan Allah? Kuma minene Hikimar dangane da hakan? Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari wannan?
*********************Musuc*****************************
Masu saurare, Hakika cikin Alkur'ani mai girma za mu samu cewa Ayoyi da dama sun yi Ishara tare da bayyana cewa Hakika wasu daga cikin Annabawan Allah tsarkaka sun yi albishir da zuwan cikamakin Annabawa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ta hanyar Ambato da siffofinsa ko kuma sunansa, misali a yayin da Annabi IBrahimu Khalilullah ya gina Ka'aba yayi Addu'a yana mai cewa:(Ya Ubangijinmu Ka aiko Manzo daga cikinsu (watau daga cikin zuriyar Annabi Ibrahimu a cikin Makka)ya rika karanta musu Ayoyinka ya kuma sanar da su Littafi da Hikima, ya kuma tsarkake su.Hakika Kai, Kai ne Mabuwayi Mai Hikima) Suratu Bakara Aya ta 129 Hakika Maliman tafsiri sun bayyana cewa wannan Siffar da Annabi Ibrahimu (a.s) ya bayyana ya yi daidai da Annabi Muhamadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, Sannan kuma wani Hadisi da aka ruwaito Ma'aikin Allah shi kansa ya tabbatar da Hakan inda ya ce :(Ni ne Addu'ar Ibrahimu), kamar yadda kuma Aya ta shida cikin Suratu Saffi ta yi bushara da zuwan Annabi Muhamadu (s.a.w.a) inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Kuma Ka tuna Lokacin da (Annabi) Isa dan Maryamu ya ce Ya Bani-Isra'ila Hakika Ni Manzon Allah ne gare ku, mai gaskatawar abin da yake tare da Ni na Attaura kuma mai albishir da wani Manzo da zai zo baya na sunansa Ahmadu. Sannan Lokacin da ya zo musu da (ayoyi) mabayyana sai suka ce, wannan tsafi ne mabayyani). Masu saurare, kari kan wannan Ayoyi masu albarka da kuma Ayoyin da muka nakalto muku a shirin da ya gabata dangane da busharar cikamakin Annabawa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka cikin Attaura da Litattafan Yahudawa, za mu samu cewa Hakika Allah madaukakin sarki ya dauki alkawari da Annabawansa baki daya wajen yin Imani da cikamakin Ma'aika tare kuma da taimakonsa, inda Allah madaukakin sarki ke cewa:((Kuma (ka tuna) lokacin da Allah ya dauki alkawari daga annabawa cewa:"Lallai abin da Na ba ku na Littafi da hikima sannan wani Manzo ya zo muku mai gaskatawar abin da yake tare da ku, to Lallai ku bada gaskiya da shi, kuma lallai ku taimake shi."Sai ya ce: kun yarda, kuma kun dauki alkawarina bisa wancan?sai suka ce Mun yarda."sai ya ce: "To ku shaida Ni ma ina tare da ku daga (cikin) masu shaida) suratu Ali Imrana Aya ta 81.
**************************Musuc*********************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na Karamin sani Kukumi na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci na Iran dake nan birnin Tehran, idan muka koma kan hasken Shiriya na biyu watau tafarkin iyalan gidan Anabta, Hadisai da dama da aka ruwaito daga iyalan gidan Anabta tsarkaka sun bayyana cewa Alkawarin da Allah madaukakin sarki ya dauka da Annabawansa tsarkaka na Imani da kuma taimakon cikamakin Annabawa Annabi Muhamadu (s.a.w.a), an dauke sa ne tun kafin a shigo wannan Duniya watau a Alamu Zar, kuma daga cikin misdakin ko tabbaci na wannan alkawari shi ne yin albishiri da zuwansa da kuma bayar da shaida a gareshi gami da bayyana alamominsa da kuma sanar da shi domin suyi Imani da shi a yayin da Allah madaukakin sarki ya tayar da shi,a cikin shirin da ya gabata Hakika mun nakalto Hadisai da dama da suke bayyani dangane da wannan, a matsayin Karin bayyani bari mu karanto muku Khudubar Annabin Rahama mai girma a ranar Qadir watau Khudubar da yayi a ranar 18 ga watan zillhijja na karshen Hajjinsa wacce aka ruwaito cikin Littafin Alburhan fi Tafsiril-Qur'an,inda Ma'aikin Allah (S.A.W.A) ya ce:(Ya Ku Mutane Daga kaina wallahi Mutanan farko daga Annabawa da Ma'aika, kuma Ni ne cikamakin Annabawa da Ma'aika, kuma Hujjar Allah ga dukkanin Makhlukai daga Ahlin Samai da Kasai, duk kuma wanda ya yi da wannan shi Kafiri ne, kafirci irin na Jahilan farko, duk kuma wanda ya yi kokonto da wannan fadar tawa Hakika ya yi kokonto ga dukkanin abinda na fada, kuma yin kokonto a kan hakan wuta ce, Ya Ku Mutane Allah ya so ni da wannan falala, ya kuma yi mini kyauta daga gareshi da ita, da kuma kyautatawa daga gare shi a gare Ni, babu kuma wani abin bauta face shi,zuwa gare shi godiya daga gare Ni ta har abada, har kuma karshen Duniya cikin ko wani hali) Masu Saurare daga wannan kalamai na Manzon Rahama za mu fahimci tushen hikimar da ta sanya Allah madaukakin sarki ya dauki alkawari da Annabawansa tsarkaka na yin bushara da Shi (s.a.w.a) kuma wannan Hikima ita ce cikar hujja ga dukkanin mabiya Addinan samai na wajabcin yin Imani da shi (s.a.w.a) da kuma kaucewa kafircewa da'awarsa domin tsira daga wuta.domin shi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka shine cikamakin Annabawa kuma shi ne ke dauke da karshen shari'a kuma kamallala daga Allah madaukakin sarki wacce ya cika Adininsa na gaskiya da ita kuma ya cika Ni'imarsa ga Talikai. Hakika na daga cikin Zalintar kai mutum ya haramtawa kansa Imani da wannan shari'a., a cikin Littafin Khisal, Shekh Saduk ya ruwaito hadisi daga Imam Hasan Mujtaba(a.s) hadisin na tsaho, a wani bangare na cikin sa an bayyana cewa( wasu Mutane daga Yahudawa sun je wajen Ma'aikin Allah (s.a.w.a) sai suka ce Ya Muhamad kai ne kake da'awar Anabta kuma ka ce ana yi maka wahayi kamar yadda ake yiwa Musa bn Imrana? Sai Ma'aikin Allah ya yi shuru har na tsahon awa guda sannan ya ce Na'am Ni ne Shugaban 'ya'yan Adamu ba alfakhari ba, kuma Ni ne cikamakin Annabawa da kuma Shugaban Masu tsoron Allah da kuma Ma'aiki na Ubangijin Talikai, Sai suka ce zuwa ga wa? Zuwa ga Larabawa? Ko zuwa ga wadanda ba Larabawa ba? Ko kuma zuwa gare Mu? Sai Allah madaukakin sarki ya saukar da wannan Aya:(Ka ce Ya Ku Mutane hakika ni Manzon Allah ne gare ki gaba daya, wanda milkin Sammai da Kassai nasa ne, babu wani abin bauta wa sai Shi, yana rayawa yana kuma kashewa, Saboda haka ku ba da gaskiya da Allah da Manzonsa, Annabi Ummiyi wanda yake ba da gaskiya da Allah da kuma kalmarsa(Alkur'ani) kuma ku bi shi don ku shiriya) suratu A'arafi Aya ta 158 da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu sabati wajen bin gaskiya da kuma Shugaban Mursalai da iyalan gidansa tsarkaka.
**********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu