Matsayin Annabi dangane da Annabawan da suka gabata
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tamabayarmu ta yau mine ne maukifi ko kuma mu ce matsayin cikamakin Annabawa dangane da Addinan da suka gabata da kuma sakonin Annabawan da suka gabata? Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari wannan.
***********************Musuc*******************************
Masu saurare kamar yadda shirin ya saba ya kan komawa ga Haskaken shiriya guda biyu watau Alkur’ani mai girma da kuma tafarkin iyalan gidan Annabta tsarkaka domin amsar tambayarmu, idan muka fara da Alkur’ani mai tsarki za mu samu Ayoyi da dama wadanda suke bayyani a kan Imanin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka da dukkanin Annabawan Allah da suka gabace shi, sannan ya sarraha cewa Imani da su wani sashe ne na Imani da Allah madaukakin sarki, a cikin Suratu A’arafi Aya ta 158 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka ce: "Ya Ku Mutane , Hakika ni manzon Allah ne gare Ku gaba daya, wanda mulkin Sammai da Kassai na sa ne, babu wani abin bauta wa sai shi,yana rayawa yana kuma kashewa, saboda haka ku bada gaskiya da Allah da Manzonsa, Annabi Ummiyi wanda yake ba da gaskiya da Allah da kuma Kalmarsa (Alkur'ani) kuma ku bi shi don ku Shiriya") Maliman tafsiri kamar shaihin Malamin Tafsirin nan Faid Kashani cikin Tafsirinsa watau Assafi ya ce abinda ake nufi da Wanda ya yi Imani da Allah da kalmominsa shi ne shi ne yin Imani da abinda aka saukar a gareshi da kuma wadanda aka saukar ga Annabawan da suka gabace shi,ma’anar kuma suka bishi domin samun shiriya shi ne shiriya da ilmin Ladduni wanda zai yi musu jagora zuwa ga soyayyar Ubangiji da kuma wulayarsa wanda kuma shi wannan Ilimi ba ya tabbata saida Imani da kuma yin biyayya ga Ma’aikin Allah (s.a.w.a) gami da bin umarnin wanda yayi Umarnin a yi masa biyayya tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, wannan shike tabbatar da cewa Ma’aikin Allah (s.a.w.a) yayi Imani da dukkanin sakonin da suka gabace shi, kuma yana kira zuwa ga yin imani da dukkanin Annaban Allah amincin Allah ya tabbata a garesu kamar yadda yazo cikin farko suratu Bakara da kuma karshenta yayin da Allah madaukakin sarki yake bayyani kan siffofin Mumunai.wannan kenan, na biyu kuma Hakika Ma’aikin Allah ya zo ne domin gaskanta Sakonin Annabawan da suka gabashi a bangare guda, a wani bangaren kuma ya zo ne domin cika wadannan sakonni.da kuma kore canje canjen da shugabanin Bata suka samar a cikin wadannan sakonni da kuma bayyana gaskiya da suka boye, misali muna iya cewa Ma’aikin Allah (s.a.w.a) ya zo ne domin tsarkake sakonin da suka gabata daga tahrifi da kuma bayyana gaskiyar da aka boye a cikin su kamar yadda Allah madaukakin sarki yayi ishara cikin Ayoyi biyu na cikin Suratu Ma’ida da suke kore duk wani nau'in Shirka da Maliman Yahudawa da Nasara suka samar, Allah madaukakin sarki ya ce:(Ya Ku ma'abuta Littafi, Hakika Manzonmu ya zo muku yana bayyana muku (abubuwa) da yawa daga abubuwan da kuka kasance kuna boyewa daga Litattafan (Attaura da Linjila)yana kuma kyale abubuwan da yawa, Hakika Haske ya zo muku daga Allah(shi ne Annabi) da kuma Alkur'ani mabayyani* Da Shi Allah yake shiryar da wanda ya bi yardarsa hanyoyin kubuta, yake kuma fitar da su daga duffan(kafirci) zuwa hasken Imani da Izininsa, yake kuma shiryar da su zuwa tafarki madaidaici) Suratu Ma’aida ta 15 da ta 16.
************************Musuc***************************
Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na Karamin sani Kukumi na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci na Iran dake nan birnin Tehran, Shakka babu cikamakin Annabawa (s.a.w.a) ya zo ne domin yin gyara ga Sakonin Allah da aka saukar daga sama bayan da aka yi tahrifinsu ko kuma murguda gaskiyar dake cikin su ,da kuma cikka wadannan sakonni da mafi kamalallar Risala da Allah madaukakin sarki ya Ni’imta bayinsa da ita wacce ta ‘yantar da Mutane daga kangin dukkanin tahrifi kuma ta buda mafi girmar babe da kuma martabar kamala a gare su, Allah madaukakin sarki ya ce:((Su ne) wadanda suke bin Manzo Annabi Ummiyi wanda za su same shi a rubuce a gurinsu cikin Attaura da Linjila, yana Umartar su da aikin alheri yana kuma hana su ga yin mugun aiki, yana kuma halatta musu (abubuwa) tsarkaka yana kuma haramta musu najasa, yana kuma sauke musu nauye-nauyensu da hukunce-hukumcen da suka kasance a kansu. Saboda haka wadanda suka bada gaskiya da Shi, suka kuma girmama Shi, suka kuma taimake shi, suka kuma bi hasken da aka saukar a tare da shi, to wadannan su ne marabauta)Suratu A’arafi Aya ta 157.bayan gudanar da bincike, babban malamin Tafsirin nan Allama Tabataba'I cikin Tafsiru Mizan ya bayyana dalilai na wannan Aya kamar haka: Hakika abinda Annabi Muhamadu tsira da amincin Allah su tabbata gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya zo da shi, shi ne Addini cilo da aka kago daga jikin Umarni da kyakkyawa da kuma hani da mumuna da kuma yake wanzar da kokari wajen cimma ruhin rayuwa, ya kuma cimma manufarsa na da'awa ba tare da yin Jihadi saboda Allah , dukiya da kuma rayuka ba, Allama yardar Allah ta tabbata gareshi ya kara da cewa Shi ne Addini cilo da ya kiddanya dukkanin abinda ya shafi rayuwar Mutum daga Al'amura da aiyuka, sannan ya rarrabe shi zuwa tsarkakekke ya kuma halarta shi,zuwa kuma Najasa ya haramta shi, babu wani abu daga cikin dokokin da aka shar'anta na Addini ko zamantakewa da za a kwatamta shi da shi,a wani bangare daban na kalamansa Allama Tabataba'I ya yi nuni dangane da mahimancin gyaran da Ma'aikin tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayi ga Addinan da suka gabata,Allama ya ce Shine Addinin da ya shafe dukkanin hukunce hukunce masu wahala wadanda aka sanya wa Ahlil-Kitab da Yahudawa musaman, da kuma wadanda malimansu suka kallafa musu ko kuma suka samar da su sabanin abinda ke cikin Litattafansu.a karshe Allama ya takaita bahasinsa zuwa wannan sakamako yana mai cewa Hakika cikar kamala na wadannan al'amura biyar cikin wannan Al'umma ta Annabi Muhamadu(s.a.w.a) shi ne mafi gaskiyar shaida da kuma mabi bayyana wajen bayyanar da gaskiyar Da'awarsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma Shari'ar da ya zo da ita ita ce mafi kamalar Shari'ar Annabi Musa Kalimullah da Isa Dan Maryamu Ruhullah amincin Allah ya tabbata a gare su.Shin ana bukatar wata shari'a ta gaskiya face wacce ta sanar da kyakkyawa sannan kuma ta ki mana abin ki, ta kuma halatta tsarkakekke sannan ta haramta Najasa ta kuma yi watsi da duk wani matsi gami da takurawa?.Masu Saurare takaicecciyar amsar da za mu fahimta a cikin wannan shiri,shi ne matsayin cikamakin Annabawa Annabi Muhamadu (s.a.w.a) dangane da Annnabawan da suka gabata, da kuma sakon da suka zo da shi, shi ne tabbatar da su ta hanyar Imani da Allah da kuma Kalmominsa watau Alkur'ani, tsarkake sakoninsu na Allah daga duk wani canje-canje da maliman Yahudawa da Nasara suka yi gami da cika kamalar Shari'ar Ubangiji wacce take shiryarwa zuwa mafi martabar gyara da rabauta.
**********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu