Mar 12, 2017 05:49 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, Tambayarmu ta Yau Ta yaya za mu amsa kiran da Allah madaukakin sarki kamar yadda ya bukata daga aiko Annainsa cikamakin Annabawa (s.a.w.a) Rahama ga Talikai a aikace? Kamar yadda ya fada a Aya ta 107 cikin Suratu Anbiya'I(Ba Mu kuwa aiko ka ba sai don Rahama ga Talikai), kafin amsa wannan tambaya sai a dakace da wannan.

**************************Musuc*********************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, Ayoyi da dama daga cikin Alkur'ani mai girma sun bayyana mana cewa yin da'a da biyayya ga Ma'aikin Allah (s.a.w.a) na daga cikin mahiman hanyoyin amfani da kasancewar sa Rahama ga Talikai a aikace, Allah madaukakin sarki ya ce:(Kuma ku bi Allah da Manzo, don a yi muku rahama) suratu Ali-Imrana Aya ta 132 a cikin suratu Nur Aya ta 56, Allah subhanahu wa ta'ala ya ce:(kuma ku tsai da sallah ku kuma ba da zakka ku kuma bi Manzo don a ji kan ku), kamar yadda Aya ta 69 na sutaru Nisa'I ta sanar da mu cewa yin da'a da biyayya ga fiyayyen halitta tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka shi ne wasilar rabauta da Ni'imomin Ubangiji na musaman da kuma cimma babban matsayi na zababbu daga cikin Mumunai, Allah madaukakin sarki ya ce:(Duk wadanda kuwa suka bi Allah da Manzo to wadancan suna tare da wadanda Allah ya yi ni'ima a gare su, irin su annabawa da siddikai da shahidai da salihai.Madalla kumwa da wadancan kyawawan abokai).har ila yau a cikin yi masa da'a da biyayya akwai rabauta mai girma kamar yadda Allah madaukakin sarki ya ce:(Wadancan iyakoki ne na Allah, duk kuma wanda yake bin Allah da Manzonsa zai shigar da shi Aljannoni (wadanda) koramu suke gudana daga karkashinsu, madawwama a cikinsu, wancan kuma (shi ne) rabo mai girma) Surata Nisa'I Aya ta 13, don haka Masu saurare wasilar farko na amsa kiran Abinda Allah yake bukata gare mu na sanya Masoyinsa Mustapha tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka Rahama ga talikai, shi yin iltizami da riko da da'a gami da biyayya gare shi, kuma yin hakan na a matsayin da'a ga Allah madaukakin sarki da kuma yardarsa, tabbatuwar hakan kuma shi ne yin aiki da dukkanin abinda ya uamarce mu a bangarori daban-daban na rayuwa, kamar yadda Nassosi da dama suka shiryar da mu zuwa wasu hanyoyi daban a aikace na amfani da kasancewar babbar Rahama a gare mu, shi ne yin Tawassuli da shi zuwa ga Allah madaukakin sarki wajen neman gafarar zunubai, kamar yadda Aya ta 64 cikin Suratu Nisa'I ta sarraha, yayin da Allah tabarka wa ta'ala ya yi khuduba ga Annabinsa yana mai cewa:(Ba Mu aiko wani Manzo ba sai don a bi shi da izinin Allah.Da dai a ce lokacin da suka zalunci kansu sun zo maka sannan suka nemi gafarar Allah, Manzo kuma ya nema musu gafara, to lallai da sun sami Allah mai yawan yafewa ne Mai yawan rahama)sannan kuwa wasu Ayoyin sun bayyana cewa bujerewa da kuma kin neman gafarar Ubangiji ta hanyar Ma'aiki mai jin kai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cikin alamomin Nifaki ko kuma Munafici, yayin da yake siffanta Munafikai, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Idan kuma aka ce da su ko zo Manzon Allah Ya nema muku gafara sai su juyar da kansu, ka kuma gan su suna bujerewa kuma suna masu girman kai) Suratu Munafik'una Aya ta 5.wannan Aya ta tabbatar da wannan hukunci a lokacin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) yana raye da kuma bayan kauransa kamar hadisai da dama suka bayyana cewa baben neman tuba ta hanyar Ma'aikin Allah a bude yake har zuwa ranar Alkiyama, misali cikin Littafin Kafi, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) ya ce:(Idan ka gudiri shiga garin Madina to kayi wanka kafin ka shiga ko kuma a yayin da ka shiga sannan ka je hubbarin Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ka yi Addu'a kuma ka karanto wannan Aya:( Da dai a ce lokacin da suka zalunci kansu sun zo maka sannan suka nemi gafarar Allah, Manzo kuma ya nema musu gafara, to lallai da sun sami Allah mai yawan yafewa ne Mai yawan rahama) sannan ka ce Hakika Ni na zo ga Annabinka ina neman tuba da gafarar zunubai na Ya Ma'aikin Allah Ni na yi tawajjuhi gareka zuwa ga Allah Ubangiji Na da Ubangijinka domin ya gafarta mini zunubaina)

**************************Musuc***************************

Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran,Hakika akwai hadisai da dama masu inganci da suke tabbatar da cewa baben neman gafara ta hanyar Annabin Rahama (s.a.w.a) a bude yake musaman ta hanyar Addu'o'I na ziyartar daga kusa ne ko daga nesa, sannan kuma akwai wasu Addu'o'I da aka ruwaito cikin Litattafai masu inganci na yin Tawassuli da shi, kamar yadda daga kuma daga cikin hanyoyin amsa kira kan butar Allah madaukakin sarki gare mu na aiko masoyinsa Mustapha (s.a.w.a) Rahama ga Talikai shi ne yin koyi da shi da kuma aiki da dukkanin Sunarsa. Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Hakika abin koyi kyakkyawa ya kasance a gare ku wajen Manzon Allah, amma ga wanda yake kaunar Allah da ranar Lahira,ya kuma ambaci Allah da yawa) suratu Ahazabi Aya ta 21.wannan Aya ta kebanta ga Masoyin Allah Mustapha tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka.Na'am ba z aka samu wata Aya a cikin Alkur'ani mai girma da take Magana kan koyi ba tare da kaidi ba face ga Annabin Rahama (s.a.w.a), amma Ayar da take Magana kan koyi ga Annabi Ibrahimu (a.s) kamar yadda ya zo cikin Suratu Mumtahinatu Aya ta 4, ba ta kebanta ga Annabi Ibrahimu bas hi kadai, ta shafi Koyi da shi da kuma koyi da wadanda suke tare da shi daga cikin mumunai,a wani kayaddadan lokaci, Shi ne yin bara'a daga mutanan su Mushrikai.Amma Ayar da take bayyani kan cikamakin Annabawa (s.a.w.a) ta yi umarni da yin koyi da shi a dukkanin aiyukansa da dabi'unsa ba tare da kaidi ba, yin koyi da shi musababbin rabauta da mafi girmar martabar kamala, Na'am Ma'aikin Allah (s.a.w.a) shi kadai ne Allah tabaraka wa ta'ala ya siffanta shi da mai dabi'u masu girma. A cikin suratu Kalam Aya ta 3 da 4 Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Kuma Hakika lallai kana da lada marsa yankewa*Hakika kuma kai kana kan halaye masu girma). Masu saurare takaicecciyar amsar Shirin na Yau shi ne daga cikin hanyoyin da Nassosi suka Ambato domin amsa kiran abinda Allah madaukakin sarki yake bukata garemu na aiko Masoyinsa Mustapha Rahama ga Talikai, shi ne yi masa da'a da biyayya ga dukkanin umarninsa, neman gafara ta hanyar sa, yin tawassuli da shi zuwa ga Allah madaukakin sarki, da kuma koyi da shi cikin dukkanin aiyukansa da dabi'unta wanda hakan ke sanya a rabauta da mafi girman martabar rahamar Ubangiji.

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu