Dalilin Kebance Ma'aikin Allah da siffar Rahama ga Talikai
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, Tambayarmu ta Yau minene dalilin da Allah Subhanahu wa ta'ala ya kebance Annabi Muhamadu (s.a.w.a) da Rahama ga Talikai?kuma mine ne dalilin da ya sanya aka kebance shi da wannan siffa daga cikin Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su? Shin dukkanin su ba rahama ba ne ga Talikai? wani irin darasi ne za mu dauka a aikace a rayuwarmu ?Kafin amsa tambayar bari mu saurari tanadin da aka yi mana a bisa faifai.
**************************Musuc*********************************
Masu saurare, a cikin suratu Anbiya'I Aya ta 107, Allah tabaraka wa ta'ala ya kira Annabinsa mai girma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka da cewa:(Ba Mu kuwa aiko ka ba sai don rahama ga talikai) maliman Tafsiri sun bayyana cewa wannan Aya mai girma ta tabbatar da cewa tushen manufa na tayar da Annabi shi ne isar da Rahama zuwa ga Talikai, Hakika cikin wani Hadisi da aka ruwaito daga gare shi, Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya bayyana cewa tushan samuwarsa shi ne Rahama yayin da yake cewa:(Hakika Ni Rahama ne mai shiryarwa),amma tambayarmu a nan mine ne dalilin da ya sanya Allah tabaraka wa ta'ala ya kebance Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka da wannan Siffa? Muna iya fahimtar daya daga cikin fuskokin amsarmu da wannan Ayar kanta,domin ita tana siffanta shi da Rahama ga talikai gaba daya domin shi an aiko shi ne ga Talikai gaba daya har zuwa ranar Alkiyama, wanda kuma hakan bai tabbata ba ga waninsa daga cikin Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su.A cikin Littafin Amaly na shekh Tusy, an ruwaito Hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:( An bani ababe biyar da ba a baiwa wani Annabi da ya kasance ya gabace ni,an aiko ni zuwa farar fata,da bakar fata da kuma jar fata,kuma an sanya mini Kasa Masallaci da abin tsarki, an kuma halatta mini dabbobi wanda kuma ba a halatta mana wani Annabi da ya gabace ni ba, kuma an bani dukkanin kalmomi watau Alkur'ani). Hakika Masu saurare idan muka yi nazari a wannan hadisi za mu fahimci cewa lallai Rahamar Ubangijin da Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya zo da ita ta shafi kowa da kowa da kuma komai da komai, wannan kenan, na biyu kuma ta zo ne domin samarwa halittu sauki kan tsananin da suke fuskanta na hukunce-hukunce da suka gabata sannan kuma ta samar da tsarkakakkiyar rayuwa, wannan shi ne abinda Aya ta 157 cikin Suratu A'arafi ta ishara da shi kamar yadda muka bayyana a shirin da ya gabata, Allah madaukakin sarki ya ce: :((Su ne) wadanda suke bin Manzo Annabi Ummiyi wanda za su same shi a rubuce a gurinsu cikin Attaura da Linjila, yana Umartar su da aikin alheri yana kuma hana su ga yin mugun aiki, yana kuma halatta musu (abubuwa) tsarkaka yana kuma haramta musu najasa, yana kuma sauke musu nauye-nauyensu da hukunce-hukumcen da suka kasance a kansu. Saboda haka wadanda suka bada gaskiya da Shi, suka kuma girmama Shi, suka kuma taimake shi, suka kuma bi hasken da aka saukar a tare da shi, to wadannan su ne marabauta) Hakika ita wannan Aya mai Albarka tana ishara ne kan kamilar shari'a ta karshe da aka saukar da ita kuma wacce ta tabbatarwa Dan Adam mafi kamala fuskokin sa'ada da kuma rabauta a Duniya da Lahira kuma wannan shi ne abinda Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya yi ishara da shi a yayin da yake siffanta Shari'arsa yana mai cewa:(Na zo muku da Sauki ).
***********************Musuc******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar Jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, Hakika Masu Saurare, daga cikin bayyanar Rahamar da ta kebanta da Annabin Muhamadu (s.a.w.a) shi ne tayar da shi a matsayin Ma'aiki ya sanya aka yi afuwa ga hukunce hukuncen Kaskanci da kuma abin Ki ga Al'ummar da ta gabata,Wannan shi ne abinda Shugabanmu Amiru-Mumunin Imam Ali (a.s) ya yi ishara da shi cikin wani hadisi mai tsaho inda a cikin sa ya amsa tambayar wasu Zindikai watau batattu wadanda suke bayyana Imani suna kuma boye kafircinsu, inda ya sanya shakku a fadar Allah madaukakin Sarki :(Ba Mu kuwa aiko ka ba sai don rahama ga talikai) ya ce: Hakika ka ga Mutanan da suka kasance kafirai suka kuma tsaya gyam a kan kafircinsu, da ya kasance Rahama a gare su? da sun shiryu sun kuma tsira daga wutar Sa'ira, Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa Hakika an aiko Ma'aikin Allah (s.a.w.a) domin fadakar da Mutanan Duniya ya na mai cewa:(Hakika Annabawan da suka gaba ce shi (s.a.w.a) an tayar da su ne bisa tasrihi ba ta'aridi ba, Ma'ana duk annabin da ya kira Mutanan sa zuwa ga Umarnin Allah, idan suka amsa masa sai amintu su kuma amintar da Iyalansu ga duk wata Azaba, idan kuma suka saba masa sai su hallaka su kuma hallaka Mutanan su da wata azaba da ta kasance Annabinsu yayi masu alkawari da ita, ya kuma tsoratar da su da wadanda suke kewaye da su, haka Azabar za ta sauka da ga cikin nau'in Azaba kama daga tsawa,iska, girgizar kasa da sauransu daga nau'in azabar da ta hallaka Al'ummomin da suka gaba ce mu, amma shi kuma Ma'aikin Allah (s.a.w.a) an jinkirtawa Mutanansa yi musu Azaba aka kuma basu damar tuba har zuwa karshen rayuwar su ba tare da an saukar musu da wata azaba ba wacce Al'ummomin da suka gabata suka aikata aka kuma saukar da azaba gare su ta hallaka su)a karshen bayyaninsa Imam (a.s) ya yi Ishara kan dabi'antuwar Annabi mai girma tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsaraka haka zalika da wasiyansa da daraja madaukakiya na Hakuri da kuma ya sanya su Rahama mai girma ga Talikai, ya kuma buda babe na madakata da kuma tsoratarwa ga Kafirai, Imam (a.s) ya ce:(Hakika Allah ya sanar da Annabinmu (s.a.w.a) da kuma hujjojinsa a doron kasa watau wasiyansa , Hakudin da babu wani Annabi daga cikin Annabawan da suka gabata su makamancinsa, sai ya tayar da su ya kuma tabbatar da matsayin su Hujjar Allah a doron kasa, inda a cikin wasiyarsa Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:duk wanda na kasance Shugabansa, to Ali Shugabansa, kuma shi a wajena kamar matsayin Haruna ne a wajen Annabi Musa saidai babu Annabi bayana) har ila yau Masu saurare ya ci gaba da cewa (ba Khalifar Annabi ba ne ko kuma mai bin hanyarsa wanda zai fadi maganar da ba ta da ma'ana, ya kamata Al'umma ta san cewa yayin da Anabta da Dan uwanci ta kasance khalifanci (bayan Musa, da Harun) karamci ne da Allah madaukakin sarki ya baiwa Annabi Muhamadu (s.a.w.a) kamar yadda ya baiwa Annabi Musa da Dan uwansa Harun, kuma wajibi ne Al'umma ta san cewa Allah ya zabi Khalifar Ma'aikin Allah ga Al'ummarsa kamar yadda aka zabi Annabi Harun ga Al'ummar Annabi Musa a yayin da ya ce masa ka zama madadina a gun Mutane na, da kuma ya ce musu kadda ku bi shugabancin wane da kansa ko kuma Azaba ta sauka a gare ku, da Azaba ta sauka a gare su, da ku baben jira da tanadi ya gushe).
Masu Saurare, takaicecciyar amsar da za mu fahimta a wannan shiri, shi ne Hakika Allah madaukakin sarki ya kebance Annabinsa mai girma tsira da amnicin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kasancewar babbar Rahama ga Talikai ta yadda ya san irin hakurinsa da kuma Hakurin wasiyansa na juriya da babu wanda zai iya irinsa, hatta da Annabawan da suka gabata amnicin Allash ya tabbata a gare su, domin haka ya aiko su zuwa ga Talikai domin isar da kamilin sakon sa da kuma yi musu hakuri ba tare da ya azabtar da su, saboda su tuba ga Allah madaukakin sarki su kuma tsiratar da kansu daga Azaba mai radadi.da fatan Allah madaukakin sarki ya bamu ikon tabbatar da hakinsa domin Albarkar riko da wulayar Ahlulbait-(a.s).
**********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu