Mar 23, 2017 12:04 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta Yau mine ne tushen aikin Annabin Rahama Muhamadu Dan Abdullahi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka? Amsar wannan tambaya za ta shiryar da mu wajen sanin irin aikin da Annabin Rahama yayi domin cimma manufar da aka tayar da shi saboda da ita a gare mu da ma al'umma gaba daya, amma kafin mu shiga cikin shirin , sai a dakace mu da wannan.

***********************Musuc******************************

Masu saurare kamar yadda shirin ya saba yak an komawa ne ga haskaken shiriya guda biyu domin samun amsar tambayar da ya bijoro da ita, da farko za mu fara da hasken shiriya na farko watau Al'kur'ani mai girma inda Allah madaukakin sarki ya ce:(Manzo ne da yake karanta muku Ayoyin Allah mabayyana, don ya fitar da wadanda suka bada gaskiya suka kuma yi aiki na gari daga duffai zuwa haske.Duk kuwa wanda ya bada gaskiya da Allah ya kuma yi aiki na gari zai shigar da shi aljannoni wadanda koramu suke gudana ta karkashinsu madawwama a cikin su har abada, Hakika Allah ya kyautata masa arziki) suratu Talaki Aya ta 11,wannan Aya mai albarka ta yi ishara kan tushen aikin Ma'aiki (s.a.w.a) watau shi ne fitar da bayi daga duhun jahilci ta hanyar koyar da su Ayoyin Allah zuwa hasken kyakkyawar Rayuwa a Duniya da Lahira, abin tambaya a nan ta yaya Annabi yake cimma wannan manufa ta sa? Aya ta 164 cikin suratu Ali-Imrana ta amsa mana wannan tambaya inda ta Ambato mafi girmar ni'imar da Allah madaukakin sarki ya yi kan bayinsa, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:(Hakika Allah ya yi ni'ima a kan muminai, yayin da ya aiko musu Manzo daga cikin su, yana karanta musu ayoyinsa, yana kuma tsarkake su, yana sanar da su kuma littafi(Alkur'ani) da hikima, ko da yake sun kasance gabanin haka suna cikin bata mabayyani), wannan Aya mai girma ta sanar da mu cewa fitar da bayi daga duffai zuwa haske yana tabbatuwa ne ta hanyar tsarkake su daga bangaren Ma'aikin Allah (s.a.w.a) kuma wannan shi ne abinda yake yi, har ma yak an amshi sadaka daga gare su ya rabata ga mabukata domin su tsarkaka, kuma ya tsarkake su ta hanyar umarinsa da kuma hanisa, Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka karbi Sadaka daga dukiyoyinsu da za ka tsarkake su da kuma wanke su da ita, ka kuma yi musu Addu'a. Hakika Addu'arka nutsuwa ne a gare su. Allah kuwa mai ji ne masani* shin yanzu ba su sani ba ne cewa Allah shi yake karbar tuba daga bayinsa yake kuma karbar sadakoki,kuma Hakika Allah ne Mai yawan karbar tuba Mai yawan Rahama) suratu Tauba Aya ta 103 da kuma ta 104, masu saurare a nan kuma za mu tambayi kanmu shin koyarwa da kuma tsarkakewar Annabi Muhamdu (s.a.w.a) ta kebanta ne kawai ga Mutanan zamaninsa? Shi Addu'arsa da ta kasance Nutsuwa ga Mumune ta kebanta ne kawai ga Mumunai da suka kasance a zamaninsa? Bayan kaurarsa shi Kenan komai ya kare?idan muka yi nazarin Ayoyi daga na biyu zuwa na 4 cikin suratu Juma'a wadanda suka  yi kusa da Aya ta 164 cikin suratu Ali Imrana da ta gabata inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Shi ne wanda ya aiko manzo cikin mutanen da bas a karatu da rubutu daga gare su, yana karanta ayoyin sa a gare su yana kuma tsarkake su, kuma yana sanar da su Littafi da Hikima ko da yake da can sun kasance lallai cikin bata mabayyani*Wasu kuma daga gare su har yanzu ba su hadu da sub a, alhali kuwa shi mabuwayi ne Mai hikima*Wadancan falala ce daga Allah yana bayar da ita ga wanda ya so, Allah kuwa ma'abocin falala ne Mai girma) domin haka shiryarwar Ma'aikin Allah(s.a.w.a) ga Bayinsa wajen fitar da su daga cikin duffai zuwa ga haske da kuma koyar da su Littafi gami da hikima ta gumshi Mutanan da suka yi zamani da shi kamar kuma yadda ta gumshi Mutanan da suka zo bayan sa har zuwa ranar Kiyama, kuma wannan shiriya tana tabbatuwa ne ko saboda Lutufi da tausayinsa gami da cetonsa ga wadanda suke tawassashi da shi zuwa ga Allah madaukakin sarki, ko kuma ta hanyar Khalifansa da wasiyansa 12 amincin Allah su tabbata garesu baki daya.

*********************Musuc***************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta iran,a cikin wasu Nassosi na daban za mu ga cewa Addu'ar Ma'aikin Allah tsira da amnicin Allah su tannata a gare shi tare daiyalan gidansa tsarkaka ta kasance mai wanzuwa har zuwa ranar Alkiyama kuma wannan Addu'a ita ce abinda ake nufi da Nutsuwa a gare su, kamar yadda ya zo cikin Suratu Tauba Aya ta 105 Allah madaukakin sarki na cewa:(Ka kuma ce da (su) Ku yi aiki, Allah ne zai ga aikin naku, sai da Manzonsa  da kuma mumunai), a cikin Tafsirin Aliyu bn Ibrahim Alkummy, an ruwaito hadisi daga Shugabanmu Imam Muhamad Bakir (a.s) ya ce:(Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaska ya ce matsayina tsakanin ku alheri ne gare ku domin Allah Ya ce:(Allah kuwa bai zamanto mai yi musu Azaba ba alhali kai kana cikinsu) suratu Anfali Aya ta 33 kuma kaura ta daga cikin alheri ne gare ku? Sai sahabai suka ce masa Ya Ma'aikin Allah matsayinka gare mu alheri ne, to ta yaya zai kasance rabumarka gare mu alheri? Rabuta da ku za ta kasance alheri domin ko wata ranaikun Alkhamis da Litinin ana gwadamin aiyukan ku, wanda ya kasance mai kyau ne sai in yiwa Allah godiya a kan hakan, idan kuma mumuna ne sai in nema muku gafarar Ubangiji).Masu saurare hakika Nassosin da aka ruwaito da wannan ma'ana su nada yawa, a wani hadisi na daban kuma an ruwaito Hadisi daga Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya ce:(duk wanda ya yi mini salati guda, Allah zai yi masa salati goma) hakika masu saurare wannan hadisi ya Shafi duk wanda ya yi masa salati tun daga Lokacinsa har zuwa ranar Alkiyawama.

Takaicecciyar amsa da za mu fahimta a wannan shiri, tushen aikin Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka shi ne kiyon bayi ya kuma fitar da su daga duffai na jahilci zuwa ga hasken shiriya ya kuma koyar da su Littafi watau Alkur'ani da Hikima gami da tsarkakewa da kuma nema musu gafarar Ubangijnsa zuwa hakan zai ci gaba har zuwa ranar Alkiyama ko ya kasance kai tsaye ko kuma ta hanyar khalifofinsa da wasiyansa 12 daga cikin zuriyar sa amincin Allah ya tabbata gare su baki daya.

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu