Abinda ake nufi da Siffar Ummiyi ga Annabi (s.a.w.a) 1
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma
Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta Yau mi ake nufi da Annabi Ummuyi kamar yadda Alkur'ani mai tsarki ya wassafa cikamakin Annabawa (s.a.w.a)? kafin amsa wannan tambaya sai a da kace mu da wannan?
************************Musuc*****************************
Masu saurare kamar yadda shirin ya saba yak an komawa ne ga haskaken shiriya guda biyu domin samun amsar tambayar da ya bijoro da ita,idan muka buda Alkur'ani mai girma za mu samu cewa ya siffanta ciffanta cikamakin Annabawa (s.a.w.a) da Nabiyil-ummyi kamar yadda ya zo cikin wasu Ayoyi guda biyu a yayin da yake yiwa Ahalil kitab daga yahudawa da Nasara Khuduba a kan su yi Imani da cikamakin Annabawa kamar yadda ya siffanta shi a cikin Litattafansu da aka saukar daga Sama watau Injila da Attaura, Allah tabaraka wa ta'ala ya ce:((Su ne) wadanda suke bin Manzo Annabi Ummiyi wanda za su same shi a rubuce a gurinsu cikin Attaura da Linjila, yana Umartar su da aikin Alheri yana kuma hana su ga yin mugun aiki, yana kuma halatta musu (abubuwa) tsarkaka yana kuma sauke musu nauye-nauyensu da hukumce-hukumcen da suka kasance a kansu.Saboda haka wadanda suka ba da gaskiya da shi, suka kuma girmama shi, suka kuma taimaki shi, suka kuma bi hasken da aka saukar a tare da shi, to wadannan su ne marabauta) Suratu A'arafi Aya ta 156. Masu saurare a bayyane yake siffanta Cikamakin Annabawa (s.a.w.s) da Ummiyi a wannan Aya mai albarka ya zo ne domin yin tuni da abinda aka Ambato cikin Litattafan da aka saukar da sama, kuma wannan shi ne abinda Ayar da ta gabata ta tabbatar da shi, a yayin da aka Ambato shi da sunan Ummiyi, siffar imaninsa ne (s.a.w.a) da Allah madaukakin sarki da kuma wadanda suka gabace shi daga cikin Annabawa wadanda suka yi bushara da zuwan sa a cikin Suratu A'arafi Aya ta 158 Allah madaukakin sarki ya ce: (Ka ce Ya Ku mutane, hakika ni Manzon Allah ne gare ku gaba daya, wanda mulkin sammai da kassai nasa ne, babu wani abin bauta wa sai Shi, yana rayawa yana kuma kashewa. Saboda haka ku ba da gaskiya da Allah da Manzonsa, Annabi Ummiyi, wanda yake ba da gaskiya da Allah da kuma kalmarsa (Alkur'ani) kuma ku bi shi don ku shiriya) idan muka yi nazari cikin amfani da Alkur'ani ya yin a siffanta Annabi Muhamadu (s.a.w.a) da Ummiyi za mu fahimci cewa wannan ma'ana ta yi kalubalanci ahlil kitab watau cikamakin Annabawa ba zai fito daga cikin su ba, za a tayar da shi wata Al'umma da ake kira da Ummiyina kamar yadda ya zo cikin Aya ta 2 cikin Suratu Juma'a, (Shi ne wanda ya aiko manzo cikin Ummawiyawa daga gare su, yana karanta ayoyin sa a gare su yana kuma tsarkake su, kuma yana sanar da su Littafi da Hikima ko da yake da can sun kasance lallai cikin bata mabayyani) abinda ake nufi da Kalmar Ummiyina a nan shi ne ba wai rashin sanin rubutu da karatu ba saidai jahilci da kuma rashin sanin Litattafan da aka saukar daga Sama, kamar yadda Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya bayyana mana a riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Kafi( Yak u Mutane Hakika Allah tabaraka wa ta Ta'ala ya aiko muku Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, kuma ya saukar muku da Littafi da gaskiya alhali kuna ummawiyawa daga Littafin, da kuma abin da ya saukar da kuma Ma'aiki da abinda ya aiko shi a wani lokaci daga Annabawa da kuma tsahon gafalarku da Mutanan da suka gabata da kuma Jahili game da abinda ya wakana a baya) a cikin wani hadisi na daban daga Imam Muhamad Bakir (a.s) cikin wata wasika ta Tarbiya da ya aikewa Sa'adul Khair Rahamar Allah ta tabbata a gare shi cikin riwayar da aka ruwaito cikin Littafin Arrauda daga kafi ya yi ishara kan cewa Kalmar Ummiya ana nufin Jahilci na abinda ke cikin Litattafan da aka saukar da sama, ba wai rashin kyautata Karatu da Rubutu ba, hakika yayin da yake aibata miyagun maliman da mabiyansu ya ce:(Jahilai Sun hallaka a kan abinda ba su Sani ba, sun kasance Umawiyawa a yayin da suke karanta Littafi suna gaskanta shi suna kuma karyatawa a yayin da aka fada musu yadda aka murguda gaskiyarsa, wadancan suna kama da maliman Yahudai da Nasara, Shugabani wajen bin son rai…)
***********************Musuc***************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga Sashen hausa na muryar Jumhoriyar Musulinci na Iran dake nan birnin Tehran,Hakika idan muka yi nazari za mu fahimci cewa Kalmar Ummiyi a fahimtar Alkur'ani bay a nufin wadanda ba su san rubutu da Karatu ba, abinda ake nufi shi ne wadanda bas u san Littafi ba ko kuma ba ahalili kitab daga cikin Yahudawa da Nasaba ba, ko kuma wadanda suke karanta Littafi amma ba sa fahimtar ma'arsa ba.ma'anar ta uku wacce kuma shakka babu ta nisanta ga cikamakin Annabawa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka, wanda yake bayyana wa Mutane abinda aka saukar masu, amma ma'anar da ta ce a nan ita ce kasancewarsa daga cikin Al'ummar da ba ahlil kitab daga Yahudawa ko nasara ba, wannan ita ce sahihiyar ma'ana to amma shin wannan manufa ake nufi da siffata Annabi da Ummiyi?Shugaban Imam Muhamad Bakir (a.s) ya amsa mana wannan tambaya a hadisin da aka ruwaito cikin Tafsirul Ayyashi da littafin Ilalu Shara'I'I da sauransu, daga cikin sum un za bo muku wacce Shek Saduk ya ruwaito a cikin Littafin Ilalu Shara'I'I daga Ja'afa bn Muhamad Sufi ya ce: Na tambayi babban Ja'afar Muhamad bn Ali Albakir (a.s) na ce masa Ya Dan Ma'aikin Allah mine ne ya sanya ake kiran Annabi (s.a.w.a) da Ummiyi? Sai Imam (a.s) ya ce mi Mutane suke fada? Sai ya ce suna fadar cewa ana kiransa ne da Ummuyi saboda bai iya rubutu ba, sai Imam (a.s) ya ce sun yi karya la'anar Allah ta tabbata a gare su, idan wannan Magana, alhali Allah tabaraka wa ta'ala cikin Littafinsa yana fadar cewa Shi ne wanda ya aiko manzo cikin Ummawiyawa daga gare su, yana karanta ayoyin sa a gare su yana kuma tsarkake su, kuma yana sanar da su Littafi da Hikima) to ta yaya ya kasance yana koyar da su alhali shi ba iya ba? Sannan Imam (a.s) Na rantse da Allan Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya kasance ya karanta da kuma Rubutawa na harshe 72 a wata riwaya na harshe 73, dangane da shakku a riwayar da take cewa ana kiran Annabi Muhamadu (s.a.w.a) da Ummiyi saboda ya kasance daga mutanan Makka, ita kuma Makka na daga cikin Ummahatul-kura kamar yadda Allah madaukakin sarki ke cewa:(don kuma ka gargadi uwar alkaryu (watau mutanen Makka) da wadanda kuma suke daura da ita) suratu An'ami Aya 1a 92 Masu saurare ganin cewa Imam (a.s) ya la'anci wanda ya fassara Kalmar Ummiyi da cewa wanda bai iya rubuta ba yana ishara ne ga wadanda suke tsakuda wannan fahimta da mumunar niya ga Annabi mai girma (s.a.w.a).tambayar da za ta biyo baya a nan shi ne yaya za mu fassara wannan Aya mai girma (Ba ka zamanto kuma kana karanta wani littafi kafin sa ba (wato Alkur'ani), ba ka kuma rubuta shi da hannunka ba, (da kuwa haka ya faru) to sai mabarnata su yi kokwanto) Suratu Ankabutu Aya ta 47, amsar wannan tambaya za a da kace mu a shiri nag aba da yardar Allah.
**********************Musuc***************************
Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.