Suratul Ankabut, 01-07 (716)
Suratul Ankabut, aya ta 1-7 (716)
Muna faraway da sunan Allah Mai rahama Mai Jin Kai.
Bismillahi rahamani Rahim, jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.
*******************
To Madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren ayoyin farko a cikin suratun Ankabut.
الم
1-ALIF LAM MIM. Allah ne Ya san abin da Yake nufi da wannan.
أَحَسِبَ النَّاسُ أَن يُتْرَكُوا أَن يَقُولُوا آمَنَّا وَهُمْ لا يُفْتَنُونَ
2—Yanzu mutane suna tsammanin za a kyale su ne saboda suna cewa: Mun ba da gaskiya,kuma ba za a fitine sub a?
وَلَقَدْ فَتَنَّا الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ فَلَيَعْلَمَنَّ اللَّهُ الَّذِينَ صَدَقُوا وَلَيَعْلَمَنَّ الْكَاذِبِينَ
3- Hakika kuwa Mun fitini wadanda suke gabaninsu,hakika kuwa Allah Yana sane da wadanda suka yi gaskiya,lallai kuma Yana sane da makaryata.
Sunan da aka bawa wannan sura kamar sauraren yan uwanta da aka bawa sunan dabbobi ko kwari kuma a aya ta 41 ne aka bawa wannan suran sunan tautau da hakan ya samo asali da kwatamta ayyukan shirka da gidan tautau mafi rauni da rushe.Har ila yau wannan sura na daga cikin surori 29 na surrorin kur'ani da ke faraway da haruffa da babu wanda ya san fassararsu sai Allah da ya boyewa kansa sani don hikima da buwaya. Kuma wannan wata mu'ujiza ce daga Allah don nuna girma da girman littafinsa da buwayarsa a ilimi. Babu wani mutum ko halitta da za ta iya fassara wadannan haruff sai dai mu karanta ba tare da sanin ma'anarsu ba kuma babu wanda zai iya yin hakan.Aya ta biyu kuma na bayani ne kan sunna da tsarin Allah mafi hikima da ke nuni da a tsawon tarihi haka lamarin yake ko da mun yi imani sai an jarraba mu da gano duk wani abu da muka boye a zukatanmu da fahimtar wadanda ke rayawa daga cikin masu yin riko da gaskiya ciki da bai. Wasu daga cikin wadanda suka yi imani da zarar sun fuskanci wata jarrabawa sai rauninsu da kafircinsu ya bayyana a fili tamkar bas u ba sabanin wasunsu masu riko da imani da kaddara mai kyau ko marar dadi a rayuwa babu wani abu daidai da kwayar zarra da ke canjawa sai ma ya kara masu imani da daukaka. Wasu kuwa munafikai ne da suka bayyana imani amma suka boye kafirci da sajewa a cikin jama'a suna rayuwa da su,wasu kuwa sun yi imani ne don kar wta manufa da wani amfani da suke son cimmawa da bayyana imani a zahiri da sauran ayyuka na addini amma irinsu da zararra sun fuskanci matsala sai kafircinsu ya bayyana a fili karara.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu:
Na farko: Shi imani ba kawai fada da baki da rayawa ko yayatawa ba ne,a'a ana bukatar juriya a duk wata jarrabawa ,mutum dole ya nuna a aikace da kare imaninsa ta kowane hali da yanayi da sadaukarwa.
2- Ita jarrabawa a rayuwa wata sunna da tsari na Allah ne a tsawon tarihi,wani da dukiya ake jarraba shi ,wani kuma da talauci ,yayin da wani kuwa da mulki ko rashin lafiya da sauran hanyoyi na jarrabawa.
Yanzu kuma lokaci ne na sauraren aya ta 4 da ta 5 a cikin wannan sura ta Ankabut.
أَمْ حَسِبَ الَّذِينَ يَعْمَلُونَ السَّيِّئَاتِ أَن يَسْبِقُونَا سَاء مَا يَحْكُمُونَ
4- Ko kuma wadanda suke aikata munanan ayyuka suna tsammanin za su gagare Mu ne ? Abin da suke hukuntawa ya munana.
مَن كَانَ يَرْجُو لِقَاء اللَّهِ فَإِنَّ أَجَلَ اللَّهِ لَآتٍ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ
5- Wanda ya zama yana tsoron haduwa da Allah ,to hakika lokacin haduwa da Allah llai mai zuwa ne.kuma Shi mai ji ne Masani.
Wadannan ayoyi ma kamar ayoyin da suka gabace su ne da ke bayani kan sunna Allah ta jarraba bayunsa kuma suna Magana ne kan gungu biyu na Kafirai da Muminai da yin barazana ga kafirai da cewa: kar su yi zaton za su iya kaucewa Azabar Allah da yin galaba kan kudurar Allah. Duk wani bijirewa dokokin Allah da cutar da muminai da suke yi suna nan a rubuce a kundin rubuta ayyukansu kuma za a yi masu hisabi kan su a ranar kotun adalci ta Allah a ranar hisabi na karshe ranar lahira.
A dabra guda ayar na Magana ga ma'abuta imani da kiran su da su ci gaba da yin da'a da biya ga dokokin Allllaaah da karaaa matsa kaimi a ibada da dogaro da dokokin Allah da manzonsa da nuna juriya kan matsaloli da takurawar makiya kar su sa su sami rauni a imaninsu.Kuma alkawalin Allah zai tabbata na mai abkuwa a ranar tashin kiyama da za a nunawa kowa aikin da ya aikata na alheri ko akasin hakan a kotun da alkalinta Allah ne Mahaliccin kowa da komi.
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:
Na farko :Aikata sabo da ci gaba da aikata sabon yana tasiri hatta a gani da jin mutum da haddasa masa matsaloli iri iri a rayuwa.
Na biyu: masu sabo da banna a doran kasa kar su yi alfahari da wannan dama da jinkiri da Allah yayi masu ko bajima ko ba dade Alkiyama za ta zo inda wanda ya aikata alheri da hakuri zai sadu da alkawalin da Allah yayi masu.
***********************
To madallah daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 6 da 7 a cikin wannan sura ta Ankabut:
وَمَن جَاهَدَ فَإِنَّمَا يُجَاهِدُ لِنَفْسِهِ إِنَّ اللَّهَ لَغَنِيٌّ عَنِ الْعَالَمِينَ
6- Duk wanda kuwa yayi jihadi,to yana jihadin ne don kansa. Hakika Allah lallai Mawadaci ne daga talikai.
وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَلَنَجْزِيَنَّهُمْ أَحْسَنَ الَّذِي كَانُوا يَعْمَلُونَ
7- Wadanda kuma suka bada gaskiya suka kuma yi ayyuka nagari,lallai za Mu kankare musu munanan ayyukansu,kuma lallai za Mu saka musu mafi kyan abin da suka kasance suna aikatawa.
Ya ku wadanda kuka yi imani ku sani duk wani aiki alheri da kuka aikata za ku ga sakamakonsa na alheri kuma amfanin kanku da kanku zai koma don haka ku ci gaba da bada kokari da himma wajen ciyar da addinin musulunci da musulmi idan ya zama wajibi ku yi gwagwarmaya da makiya addinin Allah. Kuma yana da kyau mu sani Allah bay a bukatuwa da imaninmu ko mu kare addininsa duk wani amfani da lada a gare mu zai komo idan muka aikata babu wani abu da zai kara ko rage Allah da komi daidai da kwayar zarra. Amma rahama da lutifin Allah na lullube duk wani wanda yayi imani da aiki da dokokin allah da yin riko da addinin Allah da ciyar da addinin Allah gaba ko taimakawa musulmi da bin dokoki da tafarkin manzon rahama wanda ya zo mana da addinin shiriya tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka.
Daga cikin wannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:
Na farko: Mu sani jihadi da gwagwarmaya da wannan aya ke Magana ba kawai jihadi da takoki kan makiya ba a'a duk wani nauyi na jihadi da kokari da himma a ayyukan alheri da hana kanmu aikata sabo da zalunci ako makirci ko dakile makircin makiya a bangarori kamar siyasa,tattalin arziki da al'adu dukan wannan nau'I ne na jihadi da zai amfani musulmi da musulunci.
Na biyu: Idan muka kokarta a hanyar Allah,Allah zai yafe mana sauran korakuran da muka aikata da saka mana da alheri matukar muka tsarkake zukatanmu da kyautata niyarmu ta alheri.
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..