Dec 06, 2017 09:19 UTC

Suratus Sajdah, Aya ta 15-19 (Kashi na 754)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samun tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun ayoyi ta 15 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

إِنَّمَا يُؤْمِنُ بِآيَاتِنَا الَّذِينَ إِذَا ذُكِّرُوا بِهَا خَرُّوا سُجَّدًا وَسَبَّحُوا بِحَمْدِ رَبِّهِمْ وَهُمْ لَا يَسْتَكْبِرُونَ
 

15-Hakika ba masu bada gaskiya da ayoyinmu sai wadanda idan aka yi musu wa'azi da su za su fadi suna masu sujjada su kuma yi tasbihi da yabon Ubangijinsu, kuma su ba sa yin girman kai.

Da dama daga cikin mutane suna da'awar Imani, amma kuma a mu'amalar da kalamansu sun sha babbam, wato sun kasance masu da'awar Imani,amma ayyukansu sun yi hanun riga da fadar Alkur'ani, masu da'awar Imani, bas a sajjada da Allah, amma game da mutane  suna kaskantar da kawunansu, kuma ba sa bin umarnin Ubangiji, amma game da mutane suna girmama su, kuma suna sayar da mutuncinsu.

Wannan aya ta fara da (innama) wacce take bayyani a kan kebbanta, ma'ana kadai da kadai wadanda suka kebanta da irin wadannan siffofi sune muminai na gaskiya, wasunsu kuma masu da'awar Imanin karya ne.

Daga cikin kebabbun siffofin muminin gaskiya, meka kai da kuma sallamawa game da kur'ani da kalaman ubangiji, ta yadda duk lokacin da ya ji kiran alkur'ani zai sallama ya kuma yi godiya da tasbihi ga Ubangij, ko kuma duk lokacin da ayoyin alkur'ani suka tunatar da su, ba tare da wata tantama ba suke amincewa, bas a yin dagawa da girman kai, a bangare guda kuma su masu godiyar ni'imar Ubangiji ne, bas a dora laifin matsalolinsu da wahalhalun rayuwa da suke fuskanta a kan Allah madaukakin sarki, domin shi mai tsarki game da duk wani ragi ko nakasi a game da kula al'amuran hallitu.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

1-Sujada ga Allah , tasbihi da kuma yin godiya ga Allah, na daga cikin alamomin mumini na gaskiya, musulmin da ba ya tsayar da salla, a hakikanin gaskiya bai kai ga darajar Imani ba.

2-mafi kyawan ambato yayin sujada, yin tasbihi da kuma yin godiya ga Ubangiji masa(Subhana Rabbiyar a'ala wa bi hamdihi).

3-Sujada nada kima ne a yayin da babu dagawa, kirman kai da alfari cikin ta.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na 16 da na 17 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

تَتَجَافَىٰ جُنُوبُهُمْ عَنِ الْمَضَاجِعِ يَدْعُونَ رَبَّهُمْ خَوْفًا وَطَمَعًا وَمِمَّا رَزَقْنَاهُمْ يُنفِقُونَ

 

16-Kirajansu suna nesantar wuraren kwanciya, suna bauta wa Ubangijinsu, suna masu tsoro da kuma kwadayi,kuma suna ciyarwa daga abin da Muka arzuta su.

 

فَلَا تَعْلَمُ نَفْسٌ مَّا أُخْفِيَ لَهُم مِّن قُرَّةِ أَعْيُنٍ جَزَاءً بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ

 

17-Kuma ba wani rai da zai san abin da aka boye masa na abubuwa da za su sanyaya masa rai don sakawa game da abin da suka kasance suna aikatawa.

Ayar da ya gabata, ta yi ishara game da tawaru'u da kuma Kankan da kai ga Allah ta'ala da kuma kalamansa.wadannan ayoyi kuwa sun ambato wasu daga cikin kebabbun siffofi na masu Imani, sun ce, masu Imani na gaskiya ba wai kawai suna tsai da salla ta wajibi ba ne kawai, saidai a tsakiyar dare yayin da kowa ke barci, suke tashi daga wuraren kwanansu, su shagaltu da sallar nafila gami da munajati da Ubangiji, mafi kyawan lokaci na ganawa da ubangiji da meka bukatu shi ne tsakiyar dare,saboda a wannan lokaci, Mutum ya huta kuma ya nisantu daga duk wani matsalolin rayuwa da tunani, a yayin da mutum ya tattara zuciyarsa wuri daya zai iya ganawa da mahaliccinsa, tsakiyar dare lokaci ne da ya dace mutum ya nemi gfarar Ubangijinsa bisa lafin da yayi cikin yini, ya bayyana fatansa ga ubangijinsa na yafiya da gafara, ya kuma zubar da hawayensa a game tsoron fadawa cikin azabar Allah, ya hada zuciyarsa da tausayi da jin kanubangiji.

Shakka babu, duk wanda ya gyara alakarsa da Ubangiji, alakar dake tsakaninsa da bayin Allah za ta yi kyau, Bawa ya kasance daidai iyawarsa yana magance matsalar mabukata, kuma abinda Allah  ya bashi, yana infaki ga bayin Allah.

Ci gaban ayoyin na bayyani ne game da kyakkyawan sakamako na wadannan mutane, wadannan da suka nisanta daga riya da kuna nuna kai, cikin soyayya da alaka, suke bautawa Allah, kuma suke biyan bukatun bayinsa, su nada ladan da babu wanda zai iya tunaninsa, a hakikanin gaskiya,bayan Ubangiji babu wanda ya san ladan da aka tanadar musu.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

1-Muminin gaskiya ba ya ganin kansa a matsayin wanda ya amintu daga fishin ubangiji, kuma ba ya yanke kauna daga samun rahamar Ubangiji, shi har kulun a tsakiya yake cikin tsoron fishin Ubangiji, da kuma fatan samun rahamar Ubangiji.

2-Tashi tsakiyar dare, domin karatun Alkur'ani, sallar nafila, ganawa da ubangiji da munajati, na daga cikin alamomi na muminin gaskiya.

3-domin samun lad aba tare da hisabi ba, ya kamata mutum ya jurewa tashin tsakiyar dare ya sallaci nafilfilu ya kuma nemi gafarar Ubangijinsa, tare da munajati a gare shi.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na 18 da na 19 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

أَفَمَن كَانَ مُؤْمِنًا كَمَن كَانَ فَاسِقًا لَّا يَسْتَوُونَ

 

18- Yanzu wanda ya zamanto mumini, ya zama kamar wanda ya kasance fasiki? Ai ba za su zama daidai ba.

 

أَمَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ فَلَهُمْ جَنَّاتُ الْمَأْوَىٰ نُزُلًا بِمَا كَانُوا يَعْمَلُونَ

 

19-Amma wadanda suka bada gaskiya suka kuma yi aiki na gari, to suna da (sakamakon) aljannoni na makoma, (wannan) gara ce saboda abinda suka kasance suna aikatawa.

A ci gaban ayoyin da suka gabata, wadannan ayoyi na kwatanta masu  Imani na gaskiya da masu da'awar karya na Imani, suna masu cewa: za  ka ga  karshen aikin ko wani bangare dga cikin su, wadanda suka meka kai game da umarnin ubangiji, da kuma wadanda suke da'awar Imani, amma a aikace ba za bin umarnin Allah, wani irin karshe ne da su, har abada ba za su kasance daya ba a wajen Allah.

Ci gaban ayoyin na cewa: akwai wuri a cikin Aljanna da Allah madaukakin sarki ya shirya domin karbar bayinsa na gari da masu aikin alheri, kuma kowanne mumini daidai kwalkwadon aikinsa zai samu wannan matsayi a cikin aljanna.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda biyu kamar haka:

1-A yayin kiran mutane zuwa Imani ga Allah, ana iya amfani da kwatamta rayuwar muminai na gaskiya da masu sabo da fasikai, saboda mutane su gane abubuwa na kyarai, da marassa kyau daga wadannan bangarori biyu, kuma su yankewa kansu hukunci.

2-Imani da aiki ba a rabe suke ba, Aljanna kuma sakamakon aikin mutane ne, ba wai da'awar Imani ba.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

Tags