Dec 06, 2017 09:13 UTC

Suratus Sajdah, Aya ta 10-14 (Kashi na 753)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samun tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun ayoyi na 10 da na 11 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

وَقَالُوا أَإِذَا ضَلَلْنَا فِي الْأَرْضِ أَإِنَّا لَفِي خَلْقٍ جَدِيدٍ بَلْ هُم بِلِقَاءِ رَبِّهِمْ كَافِرُونَ

 

10-Suka kuma ce:"Yanzu idan muka zagwanye a cikin kasa, ashe za a sake sabunta halittarmu?A'a, su dai suna kafircewa ne da saduwa da Ubangijinsu.

 


 قُلْ يَتَوَفَّاكُم مَّلَكُ الْمَوْتِ الَّذِي وُكِّلَ بِكُمْ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُمْ تُرْجَعُونَ 

 

11-Ka ce(da su) "Mala'ikan mutuwa ne wanda aka wakilta muku zai karbi ranku sannan kuma ga Uabangijinku za a komar da ku.

A cikin shirin da ya gabata an yi bayyanin yanayin halittar mutum, wadannan ayoyi kuwa na ishara ne game da mutuwar mutum tana cewa masu inkarin ranar alkiyama na cewa idan mutum yam utu aka sanya shi cikin kasa, dukkanin sassan jikinsa suka zagwanye, kafin tashin alkiyama babu abinda zai yi saura daga asarinsa kuma a ce za a tayar da shi a bashi wata sabuwar rayuwa!

Game da amsar su wato munkiran tashin kiyama, Ubangiji madaukakin sarki ya ce: abinda ake bisnewa cikin kasa ya kuma zama wani abu na daban ba jikin mutum ba ne kawai,amma ruhun mutum a yayin rayuwa ake ba shi, a yayin mutuwa kuwa,mala'ika suke karbewa daga gare shi, wannan ruhi, a ranar alkiyama ya kan hadewa da wani jiki makamancin wanda yayi rayuwa da shi a Duniya, da wannan tsari ne mutum yake sake rayuwa, kuma kasance a ranar tashin alkiyama.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda biyu kamar haka:

1-Tashin Kiyama:a hakikanin gaskiya abinda mushrikai suke inkari da kuma kokonto kansa : shi ne tayar da gangar jikin matattu.

2-Hakikanin Mutum Ruhu ne ba gangar jiki ba,domin haka idan wani bangare na gangar jikin mutum ya kushe, kamar ido ko kafa, mutum ba ya jin cewa wani bangare hakikaninsa ya kushe.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 12 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

وَلَوْ تَرَىٰ إِذِ الْمُجْرِمُونَ نَاكِسُو رُءُوسِهِمْ عِندَ رَبِّهِمْ رَبَّنَا أَبْصَرْنَا وَسَمِعْنَا فَارْجِعْنَا نَعْمَلْ صَالِحًا إِنَّا مُوقِنُونَ
 

 

12-Da kuwa za ka ga lokacin da kafurai suke sunkuye da kawunansu a wurin Ubangijinsu(suna cewa):"Ya Ubangijinmu, mun gani mun kuma ji, to Ka mayar da mu(duniya), za mu yi aiki na gari, hakika mu masu sakankancewa ne.

Ayar da ta gabata,tayi bayyani game da inkarin mushrikai na ranar tashin alkiyama, wannan aya kuwa tana hidabi ga Annabi da muminai tana mai cewa:ina ma ka ga lokacin da mushrikai suka sunkuyar da kansu a ranar tashin kiyama suna fatan a dawo da su Duniya, a yayin kuma da ba za a amince da bukatunsu ba, yayin da suka ga Aljanna, suka ga kuma wuta tana ruri, sai su sanar da cewa Ya Ubangijinmu ba za mu sake inkari da ranar kiyama ba, domin mun gani da idanunmu, mun samu tabbaci da yakini.saidai kash wannan amincewa da suka yi ya zo da jinkiri, domin a wannan lokaci ba zai amfanar da su ba.

Shin a duniya bas u saurari kalaman Annabawa da mursalai ba, kuma ba su ga mu'ujizar da suka zo da shi ba? Me ya sanya suke suka rufe ido kuma suka juya game da hakan? Shin ba su yi tsamanin cewa kalaman da suka fada musu gaskiya ne? shin su nada dalilan na hankali da ya sanya suka yi watsi da kalamansu?ko kuma saboda cimma bukatun ransu ne suka yi inkari maganganun na ma'aika domin a tunanin su, su kasance cikin 'yanci , su kuma yi rayuwa mai kyau.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

1-Kiyama, ranar kunya da kaico ne na masu taurine kai da kafirai, kamar yadda a Duniya suke kaskantar da muminai suna kiransu wawaye.

2-Muminai  hasashen su a wannan duniya kuma, yakini da tabbaci game da ranar Lahira, Aljanna da kuma wuta, amma kafirai kunuwansu da idanuwansu za su bude a ranar tashin kiyama su samu yakini da tabbaci, saboda ranar kiyama , rana ce ta bayyana gaskiya, da kuma budewar idanu da kuma idanu.

3-Abin da zai amfanar da ranar tashin kiyama, kuma yayi sanadiyar ceto, shi ne aiki na gari da na alheri.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya na 13 da na 14 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

وَلَوْ شِئْنَا لَآتَيْنَا كُلَّ نَفْسٍ هُدَاهَا وَلَـٰكِنْ حَقَّ الْقَوْلُ مِنِّي لَأَمْلَأَنَّ جَهَنَّمَ مِنَ الْجِنَّةِ وَالنَّاسِ أَجْمَعِينَ
 

 

13-Idan kuwa da Mun so, lallai da Mun bai wa kowane rai shiriyarsa, sai dai kuma maganta ta tabbata cewa, lallai zan cike jahannama da aljanu da mutane gaba daya.

 

فَذُوقُوا بِمَا نَسِيتُمْ لِقَاءَ يَوْمِكُمْ هَـٰذَا إِنَّا نَسِينَاكُمْ وَذُوقُوا عَذَابَ الْخُلْدِ بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

 

14-Sai (a ce da su):" ku dandani (azabar) mantawar da kuka yi na saduwa da wannan rana taku, Hakika Mu ma Mun yi watsi da ku,kuma ku dandani azaba mai dorewa saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa.

Wannan ayoyi suna tabbaci ne game da zabin shiriya da Ubangiji ya baiwa mutane sun ce: Ubangiji ya horewa mutane dalilai na shiriya, kama daga aiki Annabawa, Litattafan shiriya, hankali da kuma fitira, dukkanin wadannan abubuwa an hadawa Mutane domin shiriya, to amma dangane da karbar shiriyar ko rashin karbarsa, mutum ya nada zabi, Ubangiji madaukakin sarki da mala'ikunsa bas a tilastawa mutane waken karbar Imani,ko da yake  a bayyane yake ba ko wani mutum ba ne zai karbi shiriyar Ubangiji, wadanda suka fada cikin bata suka kuma zabi hanyar shaidan za a sanya su a cikin wuta.

A bangare guda kuma Annabawa kamar malimai suke, da suke baiwa dalibansu dukkanin darasin da ya dace, to amma babu wanda zai tilasta musu karantawa ko hardance karantun, kuma a bayyane yake daga cikin dalibai, rago, za a kore shi a karshen shekara, kuma a wannan Duniya, ba zai samu abubuwan more rayuwa da dama ba.

Wasu daga cikin mutane na cewa: ta yaya Allah mai rahama zai kona bayinsa da wuta? Wannaan aya na mayar da martani game da irin wannan gurbataccen tunani tana mai cewa:wannan rahama da jin kai na Ubangiji tana tare da bawa har zuwa lokacin da shi kansa Bawan bai haramtawa kansa ita ba,wato rahamar Ubangiji tana tare da bawan da ya yi sabo kuma ya nemi gafarar Ubangijinsa, saboda shi Allah mai rahama mai jin kai ne, amma mutuman da yake sabo kuma ba ya tunanin nadama da tuba, ya ci gaba a kan sabonsa har ya koma ga Allah ba zai tsira daga azabar Ubangiji ba.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda hudu kamar haka:

1-amincewa da shiriyar Ubangiji zabi ne, ba tilas, domin Imani da aka tilastawa mutum bas hi da wani kima.

2-wanzuwar rahamar Ubangiji, ba za ta hana fishinsa ba a kan kafirai ,mushrikai da azzalimai.

3-Allah madaukakin sarki ba zai taba mantawa da bawansa ba, face shi bawan ya so ya manta da shi.

4-mantuwa game da ranar tashin kiyama,  madogarar masu sabo ne, kuma ayyukankafirai, wanda hakan ke yin sanadiyar fadawa cikin azaba mai tsanani.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

Tags