Dec 06, 2017 09:38 UTC

Suratus Sajdah, Aya ta 26-30 (Kashi na 756)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samun tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau ne tare da sauraren karatun aya ta 26 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

أَوَلَمْ يَهْدِ لَهُمْ كَمْ أَهْلَكْنَا مِن قَبْلِهِم مِّنَ الْقُرُونِ يَمْشُونَ فِي مَسَاكِنِهِمْ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ ۖ أَفَلَا يَسْمَعُونَ
 

 

26-Yanzu ba zai zama hanyar shiriya ba a gare su cewa, Mun hallakar da al'ummu masu yawa a gabaninsu wadanda suke ta zirga-zirga cikin gidajensu. Hakika a game da wannan lallai akwai ayoyi, to me ya sa ba sa sauraro ne?

A shirin da ya gabata, ubangiji yayi alkawarin daukawa wadanda aka zalinta  fansa daga azzalimai, wannan aya kuma na cewa shin domin shiriyarku ba bai isheku ba abinda kuka gani da abinda kuka ji na cewa da dama daga cikin cikin mutanan da suka gabata masu sabo, sun hallaka, kuma ku yanzu kuke sanya kafa a inda suka sanya? Kufen da muka bari na al'ummar adawa da samudawa dake tsakanin Makka da Madina bai ishe ku darasi ba? Garin da baya wasu mutane masu tsananin karfi da dukiya suka rayu cikinsa, amma saboda sabo, zalinci da fasadin su a doron kasa muka hallaka su? A bayyana cewa a yayin da 'yan kasuwar larabawa ke ficewa ta wannan kufai, ruguzazzun gidajen na yin kara tare da kiran mutane su dauki darasi game a abinda ya faru da su, to amma babu wanda yake saurare da kunan basira.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda hudu kamar haka:

1-wuraren tarihi masu kima na mutanen da suka gabata, a maimakon daukar fim da hoto a wurin, kamata yayi wurin ya kasance na daukan darasi game da mutanan da suka yi rayuwa wurin suka kuma wuce.

2-Abinda ya fice, fitila ne na hanyar masu zuwa, da sharadin mutum ya buda idanunsa da kunuwansa ya karanci abubuwan da suka wakana a baya kuma dauki darasi game da abinda ya gabatan.

3-idan kunne mai ji ne, shakka babu ruguzazzun gidajen da aka bari zai kasance masa masu dauke da sako.

4-Kiyaye abubuwan tarihi, domin daukan darasi daga wadanda suka gabata da kuma abubuwan da suka gabata a baya wajibi ne.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 27 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّا نَسُوقُ الْمَاءَ إِلَى الْأَرْضِ الْجُرُزِ فَنُخْرِجُ بِهِ زَرْعًا تَأْكُلُ مِنْهُ أَنْعَامُهُمْ وَأَنفُسُهُمْ ۖ أَفَلَا يُبْصِرُونَ
 

 

27-Ko kuwa ba sa gani cewa Mu Muke koro ruwa zuwa ga kekashasshiyar Kasa, sannan Mu fitar da tsirai da shi, wadanda dabbobinsu  da su kansu suke ci daga gare shi? To me ya sa ba sa lura ne?

A ci gaban ayar da ta gabata da take bayyani game karfin Ubanigiji a kan azzalimai, wannan aya tana ishara ne game da tausayi gami da rahama maras iyaka ta Ubangiji game da halittu tana mai cewa: shin ba kwa ganin yadda Ubangiji yake saukar da ruwansa daga sama, ya kuma raya busassiyar kasa, daga cikinta kuma tsirai da shibkokin da kuka yi ya fito, kasa tayi koriya shar, ku samu abinci da za ku ci da dabbobinku?

A hakika, idan aka yi la'aki da yanayin kasa, wani wuri tudu ne, wani kuma gangare ne, wasu kasashen tsaunuka, babu yadda za a yi ruwan kogi da teku ya isa ko ina a doron kasa, kuma da dama dag cikin ruwan wani kogi ko kuma ma ta teku, sartsi gare shi ba zai shayu ba. Mayar da ruwan teku zuwa sirace da Rana ke yi ta mayar da shi zuwa gajimare ko hadari da umarnin Ubangiji, wannan matsala an magance ta, da wannan tsari, ta hanyar kadawar iska, ya zama ruwa, ya kuma raya kekasasshiyar kasa, tsirai su fito domin samun abincin da za ku ci ku da dabbobinku, abin fada a nan shiri, duk wani sarci na ruwan teku zai kutse ta wannan hanya, ruwan ya zama mai dadi wanda zai zamato abin sha ga Mutanan doron kasa,wannan babbar ni'ima da kowa ya ganta a zahiri, saidai kuma da dama daga cikin mutane ba sa lura da hakan, a yayin da wannan tsari na dabi'a, na da mahimanci game da ci gaban rayuwar dukkanin halittu na doron kasa.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

1-Dabi'ar kore shar da tsabtace wuraren mutane da na dabbobi, na daga mahiman aji na sanin Ubangiji, da sharadin cewa daliban wannan aji na da niyar neman sani da ilimi.

2-canzawar siracen maliya ko tekun zuwa gajimare, da kuma saukar ruwa a yankunan dake nesa da teku ba arashi ba ne, saidai iradar Ubangiji mai hikima ne.

3-Saukar ruwan sama, da kuma fitowar tsirai daga cikin kasa, na daga cikin ayoyi da kuma alamomin ubangiji, kuma bai kamata mu kalli wannan lamari a matsayin abu mai sauki.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na 28 zuwa na 30 a cikin wannan sura ta sajadati:

 

وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَـٰذَا الْفَتْحُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ

 

 28-Suna kuma cewa: "Yaushe ne ranar wannan hukuncin idan kun kasance masu gaskiya.

 

قُلْ يَوْمَ الْفَتْحِ لَا يَنفَعُ الَّذِينَ كَفَرُوا إِيمَانُهُمْ وَلَا هُمْ يُنظَرُونَ

 

29-Ka ce:"Ranar hukuncin wadanda suka kafirce imaninsu ba zai amfane sub a, kuma ba ma za a saurare su ba"

 

فَأَعْرِضْ عَنْهُمْ وَانتَظِرْ إِنَّهُم مُّنتَظِرُونَ

 

30-Ka rabu da su, ka kuma saurara, hakika su ma masu sauraro ne.

Wadannan ayoyi su ne karshen surar Sajadati, a ci gaban ayoyin da suka gabata suna cewa a yayin da kafirai da mushrikai sun Annabi ya na cewa gaskiya za ta yi galaba a kan karya da kuma irin alkawarin da aka yiwa masu Imani, sai suke yiwa Annabi ba'a da izgili suna cewa wannan alkawarin da kake yi kana cewa: Ubangiji zai dauki fansa daga mushrikai bayan ya cika musu hujja ya kuma hallaka su, wni lokaci ne hakan zai kasance?   Wannan azaba da kake yin alakwarinta a nan Duniya, wani lokaci za ta tabbatu?

A matsayin amsa, Allah madaukakin sarki yana fadar cewa: wannan rana na nan tafe, to amma kada ku yi tsamanin cewa a wannan rana za a karbi imaninku kuma za a sake baku wata dama, a wannan rana babu wata dama da komowa duniya domin cike gibin ayyuka na alheri ko kuma yin Imani.

Aya ta karshe ta bayar da umarnin cewa ka nisanci  irin wadannan mutane masu taurin kai  da sun fahimci gaskiya kuma suna yin haka da nufin izgilanci da ba'a, kace musu su jira har lokacin da Allah zai yi hukunci tsakaninmu da ku.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

1-wani lokaci, gabatar da tambaya, ta ba nufin neman gaskiya, saidai ana tambayar ne domin ba'a da izgili.

2-Imani a yayin matsuwa ba shi da kima, domin yana dauke zabi da kuma iradar mutum.

3-A yayin da kafa dalili da wa'azai ba zai yi amfani  ba, wajibi ne a nisanta da masu kaucewa hanya.

****************Musuc*************************

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags