Apr 17, 2017 11:18 UTC

Suratul Ankabut, 01-07 (717)

Bismillahi rahamani Rahim,

Jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

**********************************

To madallah masu saurare za mu fara shirin nay au ne tare da sauraren karatun ayoyi na 8 da 9 a cikin suratul Ankabut:

وَوَصَّيْنَا الإِنسَانَ بِوَالِدَيْهِ حُسْنًا وَإِن جَاهَدَاكَ لِتُشْرِكَ بِي مَا لَيْسَ لَكَ بِهِ عِلْمٌ فَلا تُطِعْهُمَا إِلَيَّ مَرْجِعُكُمْ فَأُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

8- Kuma Mun yi wa mutum wasiya da kyautata wa iyayensa,idan kuma suka yake ka kan ka yi shirka da Ni game da abin da b aka da sani a kansa, to kada ka bi su. Wurina ne makomarku kawai,sannan zan ba ku labarin  irin abin da kuka kasance kuna aikatawa.

وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُدْخِلَنَّهُمْ فِي الصَّالِحِينَ

9- Wadanda kuma suka ba da gaskiya suka yi ayyuka nagari lallai ba shakka za mu shigar da su cikin salihai.

 A lokacin da addinin musulunci ta bayyana a yankin Makka da Madina,wasu gungu daga matasa sun yi imani da annabin rahama wanda ya zo da wannan addini na shiriya da tsira inda wadannan matasa suka daina bautawa gumaka amma uwayensu maza da mata sun ci gaba da bautawa gumaka da bukatar yayansu da su canja wannnan mataki da suka dauka na imani da Manzon Allah (SWA). Wasu ma uwayensa mata har yajin kin cin abinci suka yi wajen matsawa yayansu bin umarninsu amma bas u ci nasara ban a hana yayansu yin riko da addinin musulunci. To wadannan ayoyi suna Magana ne kai tsaye da wadannan matasa da duk wani da yake rayuwa  uwayensa ko yan uwansa kafire masu shirka  da cewa; idan wani ya sami kansa wani daga cikin yan gidansu musamman babansa ko ma'aifiyarsa  kafirai ne kuma yana rayuwa tare da su da matsa masa dole sai ya bi addinin da suke yi kar ya kuskura ya bi soyuwa da kauna dake tsakanin da da ma'aifansa ko yan uwantaka da neman yardarm ma'aifansa ya sabawa Mahaliccinsa . Ya ci gaba da kyautatawa ma'aifansa da girmama su kamar yadda shari'a ta ce amma ba zai yi masu da'a ba a lamari da ya shafi shirka da sabawa Allah wanda ya halicce mu baki daya mu da su.

Ci gaban ayoyin na bayani ne ga dukan mutanen gida kama daga yaya da uwayensu da cewa;duk wani aiki da za ku aikata a wannan duniya yana nan a rubuce kuma dole ko bajima ko badade za mu amsa duk wani aiki da muka aikata.  A ranar tashin kiyama makusantan bayun Allah na gari salihan bayu su ne ma'abuta imani wadanda suka aikata ayyukan alheri.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:girmamawa da kyautatawa Uwaye wani lamari ne da ya daskare a cokar mutum bay a raubuwa babu wani banbanci a tsakani su musulmi ne ko kafirai dole a girmama su da yi masu hidima da kyautata masu matukar babu shirka cikinsa.

Na biyu:Kira zuwa ga yin shirka a gaskiya kira ne zuwa ga aikin jahiliya maras dalili saboda shirka ba ta da tushe na hankali da aiki mai dawwama.

Na uku:Yayanmu idan sun balaga nada yancin zabin hanyar da ta dace da su babu tilastawa .

Yanzu za mu saurari ayoyi na 10 da 11 a cikin wannan sura ta ankabut:

وَمِنَ النَّاسِ مَن يَقُولُ آمَنَّا بِاللَّهِ فَإِذَا أُوذِيَ فِي اللَّهِ جَعَلَ فِتْنَةَ النَّاسِ كَعَذَابِ اللَّهِ وَلَئِن جَاءَ نَصْرٌ مِّن رَّبِّكَ لَيَقُولُنَّ إِنَّا كُنَّا مَعَكُمْ أَوَلَيْسَ اللَّهُ بِأَعْلَمَ بِمَا فِي صُدُورِ الْعَالَمِينَ

10- Kuma akwai wasu mutane masu cewa: Mun ba da gaskiya da Allah ,sannan idan aka cuce su a kan hanyar Allah sai sukan dauki fitinar mutane kamar azabar Allah,wallahi kuwa idan wata nasara ta zo daga Ubangijinka, sai sukan ce:Hakika mun kasance tare da ku. Yanzu Allah ba Shi ya fi kowa sanin abin da ke cikin zukatan talikai ba?.

وَلَيَعْلَمَنَّ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا وَلَيَعْلَمَنَّ الْمُنَافِقِينَ

11- Wallahi kuma Allah Yana sane da wadanda suka ba da gaskiya ,Yana kuma sane da munafikai.

Wadannan ayoyi ci gaban ayoyin da muka saurara a sama amma wani bangare na muminai da suke rayuwa cikin jin dadi da wadata sun yi imani amma duk lokacin da wata matsala ta fuskance su ko yan uwansu muminai sais u kauraece masu  da kasa jurewa wannan matsala  ko taimakawa sauran yan uwansu muminai amma da zarar wannan matsala ta kawar , wadata ta komowa muminai  sai su nuna suna tare da ma'abuta imani da cewa: mu a kullum a ko'ina muna tare da ku kuma wannan nasara ma tare mu ka yi da ku. Ci gaban ayar na cewa: Allah Masani ne kan duk wani abu da mutum ya boye ko ya bayyana kuma ya san wane ne zai iya ci gaba da imaninsa ko da zai rasa ransa wane ne kuma ba zai iya jurewa matsala komin kankantarta domin kare imaninsa.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:Wani imaninsu a baki ne kawai bai ratsa zucci ba domin imani na gaskiya na jurewa duk wata matsala da kunci.

Na biyu:Kare imani da ci gaba da kasancewa cikin ma'abuta imani yana bukatar juriya da hakuri da nacewa.

Na Uku: Munafikai mutane masu neman wata dama  ta cimma burinsu duk inda ta yi ruwa rijiya.

********************************
Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 12 da 13 a cikin wannan sura ta Ankabut:

وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لِلَّذِينَ آمَنُوا اتَّبِعُوا سَبِيلَنَا وَلْنَحْمِلْ خَطَايَاكُمْ وَمَا هُم بِحَامِلِينَ مِنْ خَطَايَاهُم مِّن شَيْءٍ إِنَّهُمْ لَكَاذِبُونَ

12-  Kuma wadanda suka kafirta suka ce da wadanda suka ba da gaskiya: Ku bi tafarkinmu, Mu kuma lallai za mu dauke muku kurakuranku,alhali kuwa su ba za su iya  dauke wani abu na kurakuransu ba .hakika su dai makaryata ne.

وَلَيَحْمِلُنَّ أَثْقَالَهُمْ وَأَثْقَالا مَّعَ أَثْقَالِهِمْ وَلَيُسْأَلُنَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ عَمَّا كَانُوا يَفْتَرُونَ

13- Wallai kuma lallai za su dauki zunubansu da kuma wasu zunuban tare fa zunubansu,kuma Wallahi lallai za a tambaye su a ranar alkiyama game da abin da suka kasance suna kirkira.

 

Mushrika na kokarin ganin sun canjawa muminai akidarsu daga imani su koma suna riko da shirka don haka wannan ayar ke cewa: Suna cewa wadanda suka yi imani cewa; ko komo ku yi riko da hanyar uwaye da kakanninmu ku daina bin Manzon Allah da ya zo sabon addini. Idan wannan aiki bas abo ba ne babu wani abu da zai same mu mu da ku ,idan kuwa sabo ne  za mu jibanci sabonku babu wani abu da zai same ku. Ci gaban ayar na cewa; Suna raya ne kana bin da suke raya saboda azaba da sakamako baki daya suna hannun Allah ne , ba hannunsa ba,Su ba za su iya hana a azabtar da wadanda suka aikata sabo da banna ko su yafe masu kuma idan wani ya yaudaru da wannan Magana ta rashin hankali da tushe ya bar imani yayi riko da kafirci to zai gamu da azabar Allah a gobe kiyama da azabtar da su baki daya a wannan rana .

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda uku:

Na farko:Makiya bas u daina cutar da muminai ne ba wani lokaci su cutar da su da Magana ,ko azabtarwa ,wani lokaci da kage da karya da kokarin ganin sun bar imani sun koma kafirci da shirka.

Na biyu:A duniyar musulunci babu wani da ke jubantar leifin wani ba ko da ya raya cewa leifinka na dauka,wannan Magana ce maras tushe.

Na uku:Amma duk wani da ke batar da wani yana da kamasho a cikin sabonsa da duk wani sabo da zai aikata a rayuwarsa matukar ba su tuba ba.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..