Apr 17, 2017 12:03 UTC

Suratul Ankabut, 14-18 (718)

Bismillahi rahamanir Rahim.

Jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

***********************************

To madallah za mu fara shirin nay au ne da sauraren karatun aya ta 14 da 15 a cikin wannan suratul Ankabut:

وَلَقَدْ أَرْسَلْنَا نُوحًا إِلَى قَوْمِهِ فَلَبِثَ فِيهِمْ أَلْفَ سَنَةٍ إِلاَّ خَمْسِينَ عَامًا فَأَخَذَهُمُ الطُّوفَانُ وَهُمْ ظَالِمُونَ

14- Kuma hakika Mun aiko Nuhu zuwa ga mutannensa,sai ya zauna cikinsu shekara dubu ba hamsin,sannan ruwan Dufana ya kama su,a halin suna kafurai.

فَأَنجَيْنَاهُ وَأَصْحَابَ السَّفِينَةِ وَجَعَلْنَاهَا آيَةً لِّلْعَالَمِينَ

15- Sai Muka tserar da shi tare da mutanen jirgin ruwa,Muka kuma sanya shi (jirgin) aya ga talikai.

Wadannan ayoyi da sauran ayoyin d suka gabace su suna Magana nekan makomar al'ummomin annabawan da suka gabata kamar al'ummomin annabin Nuhu,Ibrahim da Musa (AS) amma aka hallakar da su saboda sun ki bada imani da Annabi Nuhu(AS).Karkashin wadannan ayoyi Annabi Nuhu (AS) ya rayu kusan shekaru dubu yana kiran al'ummarsa zuwa ga kadaita Allah da bauta da yin imani  ba dare ba rana yana fadakar da su amma sai yan kadan da bas u fice a kilga su da yatsa ba suka yi imani da wannan kira nasa na shiriya  amma mafi yawa na al'ummar da yake kokarin shiryar da su da kiran su zuwa ga kadaita Allah da bauta sun kafirce da nuna bakar kiyayya.Saboda haka ne Allah ya sabkar masu da azaba ta ruwan dufana da hallakar da duk wani kafiri a dabra daya ya tsiratar da wadanda suka yi imani domin zama darasi ga sauran al'ummomi masu zuwa irinmu da sanin duk al'ummar da ta shinfida zalunci da kafirci a doran kasa makomarta hallaka ne duniya da lahira.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Imani ko kafirci nada alaka da hallaka ko tsirar al'umma a duniya.

Na biyu: A mahangar kur'ani da dalili na kur'ani rayuwa sama da shekaru dubu abu ne mai yuyuwa  don haka tsawon rain a Imam Mahdi (AS) wanda daga aifuwarsa zuwa yanzu kimanin shekaru dubu da dari biyu abu ne mai yuyuwa daga Allah ba mamaki.

Na uku: a lamari da ya shafi yada addini ana bukatar hakuri da tsayin daka da nacewa ba tare da mun damu da wadanda za su yarda da abin da muke fadi ko yawansu ba.

To yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 16 da 17 a cikin wannan sura ta Ankabut kamar haka;

وَإِبْرَاهِيمَ إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَاتَّقُوهُ ذَلِكُمْ خَيْرٌ لَّكُمْ إِن كُنتُمْ تَعْلَمُونَ

16- Kuma ka tuna Ibrahimu lokacin da y ace da mutanensa: ku bauta wa Allah,kuma ku ji tsoron Sa. Wannan shi ya fi muku alhairi in kun kasance kun san hakan.

إِنَّمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ أَوْثَانًا وَتَخْلُقُونَ إِفْكًا إِنَّ الَّذِينَ تَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ لا يَمْلِكُونَ لَكُمْ رِزْقًا فَابْتَغُوا عِندَ اللَّهِ الرِّزْقَ وَاعْبُدُوهُ وَاشْكُرُوا لَهُ إِلَيْهِ تُرْجَعُونَ

17- Hakika abin da kuke bauta w aba Allah  ba gumaka ne kawai,kuma kuna kirkirar karya ne. Hakika wadanda kuke bauta w aba Allah ba, ba su mallaki wani arzikinku ba,sai ku nemi arziki a wurin Allah,kuma ku bauta masa,ku kuma gode masa,gare Shi ne kawai za a komar da ku.

Bayan Annabi Nuhu (AS) sai annabi Ibrahima na biyu daga cikin manzonni Ulul Azm  da ya kirayi al'ummarsa da su komo daga rakiyar bautar gumaka da fadakar da su kan babu wani amfani ko cutarwa daga wadannan gumaka da suka sassaka da hannunsu ,su riki bautawa Allah  Shi kadai  wand aba a hada Shi da wani abin bauta da cewa;idan don kare ku daga talauci ko samin arziki kuke bautawa Gumaka to ku sani wadannan gumaka bas u tasiri a rayuwarku ku biya maku bukatu ko cutar da ku. Amma Shi Allah Wanda ya halicce ku Shi ne mai Ni'imartar da ku da arziktar da ku ko kun bauta masa ko ba ku bauta masa  kuma ku bautawa wanda yak e arzikta ku a wannan duniya da kuma saka maku a gobe kiya da gidan aljanna.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:Yin ibada da yin hamdala matukar babu tsoran Allah wato Takawa da kaucewa aikata sabo ba ta da wani amfani da tasiri.

Na biyu:Wadanda ke ganin wasu ba allah na tasiri a rayuwarsu ta abin duniya to sun fada cikin wani nau'I na shirka tabbas.

Na uku: addini kamar yadda yake kiranmu zuwa ga yin wani kokari da zai kai mu ga gacci a rayuwa da samin sauki da walwala a rayuwar mu ta Madda ,haka kuma yake kiran mu zuwa ga godewa Allah kan wannan ni'ima da ita ma godiya ga Allah wata ibada ce mai girma da kara daukakarmu,

*****************************

To madallah yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 18 a cikin wannan sura ta Ankabut:

وَإِن تُكَذِّبُوا فَقَدْ كَذَّبَ أُمَمٌ مِّن قَبْلِكُمْ وَمَا عَلَى الرَّسُولِ إِلاَّ الْبَلاغُ الْمُبِينُ

18- Idan kuma kuka karyata,to hakika da ma wasu al'ummun da suke gabaninku sun karyata,baa bin da yake kan Manzo sai isar da sako mabayyani.

A wannan ayar annabi Ibrahima (AS) yana Magana kai tsaye da masu bautawa gumaka da cewa;ban a zaton dukan mutane za su yi imani da addinin allah  saboda tarihi ya tabbatar da hakan kan al'ummomin da suka gabace ku wadanda suka karyata annabawa da manzonni da dama da aka aiko masu don shiryar da su. Nauyi da ya rataya kaina kamar sauran annabawa da manzonnin Allah (AS) shi ne isar da sako na kiran mutane zuwa ga kadaita Allah da bauta ,ya rage ga mutane su amince da wannan kira ko su bijire ya rage nasu. Ni dai na san na isar da sakon da aka turo ni da shi kuma kan haka ne za a tambaye nib a kafircin mutane ne ba da bai shafe ni ba.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko;Manzonnin Allah (AS) bas u matsayawa al'umma yin imani kawai himmarsu isar da sako ga al'umma.

Na biyu:Muminai kar su yi zaton sauran mutane ma za su zama kamarsu wajen yin imani da Allah idan su isar da s=nauyin yada addini sun isar da sako ba ruwansu da kafircin kafirai.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..