Suratul Ankabut, 19-23 (719)
Suratul Ankabut, 19-23 (719)
Bismillahi rahamani Rahim,
Jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah ya ba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.
***********************************
To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau tare da sauraren karatun aya ta 19 da 20 a cikin suratul Ankabut:
أَوَلَمْ يَرَوْا كَيْفَ يُبْدِئُ اللَّهُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ إِنَّ ذَلِكَ عَلَى اللَّهِ يَسِيرٌ
19- Yanzu ba su ga yadda Allah Yake farar halitta ba, sannan Shi ne kuma zai mayar da ita? Hakika wannan mai sauki ne a wurin Allah.
قُلْ سِيرُوا فِي الأَرْضِ فَانظُرُوا كَيْفَ بَدَأَ الْخَلْقَ ثُمَّ اللَّهُ يُنشِئُ النَّشْأَةَ الآخِرَةَ إِنَّ اللَّهَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ
20- Ka ce : Ku yi tafiya a bayan kasa sannan ku duba ku ga yadda Allah Ya farar da halittu,Sannan Allah ne Zai sake samar da su samarwa karshe. Hakika Allah Mai iko ne a kan komai.
A cikin shirin da ya gabata kunji tattaunawa da ta wakana tsakanin Annabi Ibrahima (AS) da mushrikai daga cikin al'ummarsa da yadda Annabi Ibrahima ya kirayi al'ummarsa su daina bautawa gumaka da neman bukatunsu a gare su kuma wannan ayoyi da muka saurara sun zo ne a tsakiyar wannan tattaunawa da hakan ke nuni da yadda mushrika ba a shirye suke bas u karbi kiran gaskiya da shiriya su wadannan mushrikai na zamanin annabi Ibrahima ne ko nan a zamanin manzon rahama da tsira ne Muhammad (SWA) duk daya suke. Wadannan ayoyi na kiran mushrikai da su yi aiki da hankalinsu da tunaninsu da yin nazari kan halittu dfa sake tayar da su su fahimci Allah da ya halicce su tun farko yafi sauki a gare Shi ya sake tayar da su da ita kanta wannan duniya da sauran duniyoyi da abubuwan da ke cikinsu mai iko ne kansu da komi saboda haka sake tayar da mutane wani lamari ne mai sauki kuma tabbatacce.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda hudu kamar haka:
Na farko: Kur'ani littafi ne da ke kiran dukan mutane ga tunanin da zai kai mu ga risker gaskiya da shiriya.
Na biyu:Halitta tushe ne na ilimi da kudurar Allah marar karewa ta samar da rayuwa da mutuwa ga halittu.
Na uku:A addinin musulunci ziyara da bulaguro da yawace-yawace burinsa fahimta da nazari a cikin dabi'a domin gano gaskiya kuma ta hanyar halttu a sani da fahimtar girma da matsayin Allan da ya halicci komi da kowa ,don haka addini ke jaddada yin bulaguro.
Na hudu:Babban dalili na tabbatar abkuwar tashin kiyama ,Nuna karfi da ikon Allah a gaban halittunsa da kuma tabbatar da adalcinsa a gaban kowa.
To yanzu kuma za mu saurari karatun ayayo na 21 da 22 a cikin wannan sura ta ankabut:
يُعَذِّبُ مَن يَشَاء وَيَرْحَمُ مَن يَشَاء وَإِلَيْهِ تُقْلَبُونَ
21- Yana azabtar da wanda Ya so,Yana kuma jin kan wanda Ya so;kuma wurinsa kawai za a komar da ku.
وَمَا أَنتُم بِمُعْجِزِينَ فِي الأَرْضِ وَلا فِي السَّمَاء وَمَا لَكُم مِّن دُونِ اللَّهِ مِن وَلِيٍّ وَلا نَصِيرٍ
22- Kuma ku ba za ku gagara ba a kasa ko kuma a sama,kuma ba ku da wani majibinci ko mataimaki in ba Allah.
Ayoyin da suka gabaci wadannan suna bayani ne kan kudurar Allah na sake tayar da halittu bayan mutuwa to wadannan ayoyi da muka saurara na cewa;Wannan duiniya gidan aiki ne da kokri da karkashin imani da gaskiya sabanin gidan lahira wanda gida ne na ganin sakayya da sakamakon aikin da muka aikata a wannan duniya mai kyau ko akasainsa.Duk abin da mutum ya shibka a wannan gona ta duniya to shi ne zai girbe a ranar lahira. Kuma babban abin lura a nan shi ne alkali a wannan kotu ta Kiyama Shi ne Allah wanda ya sani da masaniya kan duk wani aiki da muka aikata a wannan duniya komin kankantarsa hatta niyarmu kan aiki da muka aikata ko ba mu aikata ba kuma azaba da sakayya ta alheri suna hannunsa haka kuma yafewa da rahama duk nasa ne Allah sa muna cikin wadanda za su riski rahama da yaewarsa da kuma lutifinsa duniya da lahira.
Kar wani ya kuskura yayi tunani ko hassashen cewa a wannan duniya ko a lahira wani abu za a manta da ya aikata babu wani abu da ilimi da kudurar Allah ba su san shi ba a cikin sammai da kassai kuma kowa da komi yana rayuwa ne da motsi karkashin hukumcin Allah.
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:
Na farko:Rahama da azabar Allah tare suke tafiya ta inda wadanda suka aikata alheri za su yi fatar gamuwa da rahamarsa kamar yadda wadanda suka aikata banna za su gamu da azabarsa karkashin adalcinsa.
Na biyu: Kudura da iradar Allah kan bayunsa suna tafiya ne karkshin adalci da hikimarsa kamar yadda ayoyin kur'ani da dama suka tabbatar.
Na uku: Bukatta da son mutum har abada ba za su iya yin galaba kan bukata da kudurar Allah ba komin karfi da mulki ko dukiya ko nasaba da mutum ke takama da buga kaba da su.
************************
Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 23 a cikin suratun Ankabut:
وَالَّذِينَ كَفَرُوا بِآيَاتِ اللَّهِ وَلِقَائِهِ أُوْلَئِكَ يَئِسُوا مِن رَّحْمَتِي وَأُولَئِكَ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ
23- Wadanda kuma suka kafirce da ayoyin Allah da kuma gamuwa da Shi, wadannan sun debe kauna daga rahamata,kuma wadannan suna da azaba mai radadi.
Ayoyin da suka gabata suna bayani ne kan abubuwan da za su wakana a ranar kiyama inda wani gungu azaba da fushin Allah zai riske shi yayin da wani gungu na muminai rahama da lutifin Allah za su lullube su to wannan ayar da muka saurara tana Magana ne da wanda suka debe kauna da rahamar allah da cewa; duk wanda ya ga ayoyin Allah a fili a cikin tsarin rayuwa da halitta ko ya ga ayoyin Allah a cikin kur'ani mai girma amma tsananin kafirci da jayayya suka say a karyata to ya sani tabbas a ranar tashin kiyama zai gamu da fushi da azabar Allah mai radadi kuma babu wata dama ko kadan ta yafe masa saboda ya karya tsarin rayuwa da halitta tun farko da kuma wanna rana ta kiyama .
Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da fahimtar abubuwa biyu:
Na farko: Rahamar Allah tana da fadin gaske kuma ba ta da iyaka tana iya risker kowa idan yana bukata da kuma ya kudurta niya mai kyau ko aiki mai kyau amma kafiri ko mai musantawa ya toshe duk wata hanya ta gamuwa da rahamar Allah matukar bai tuba ba.
Na biyu: gungun da bas hi da rabo a cikin rahamar Allah da kuma shi kansa ya debe kauna daga rahamar Allah ,su ne kafirai Da fatar Allah ya kiyashe mu da kafirci da kuma debe kauna daga rahamar Allah da fatar samin karshe na alheri.
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..