Apr 17, 2017 12:32 UTC

Suratul Ankabut, 24-26 (720)

Bismillahi rahamani Rahim,

jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

***********************************

To madallah za mu fara shirin na yau ne da sauraren karatun aya ta24 a cikin wannan sura ta ankabut:

فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلاَّ أَن قَالُوا اقْتُلُوهُ أَوْ حَرِّقُوهُ فَأَنجَاهُ اللَّهُ مِنَ النَّارِ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ

24- Sannan ba wani jawabi da ya fito daga bakin  mutanensa sai cewar: ku kasha shi ko kuma ku kone shi, Sai Allah Ya tserar da shi daga wutar . Ba shakka a game da wannan lallai akwai ayoyin ga mutanen da suke ba da gaskiya.

A cikin wannan sura ta ankabut bayan kawo bayani kan al'ummar annabi Nuhu (AS)  sai muka fara bayani da annabi Irahima (AS) da al'ummarsa da dalilan da ya gabatar masu da yadda ya kirayi mushrikai zuwa ga kadaita Allah da bauta da kuma abubuwan da za su wakana bayan mutuwa  to amma duk da wannan bayanai masu gamsarwa mutanan annabi Ibrahima (AS) sai suka aikata sabanin hankali da cewa; bayan sun kasa bada hujja kan bayanai na hankali  da hujjoji a bayyanai sai suka riki hanyar gallazawa da barazana kamar yadda a yau ma masu girman kai na duniya  da nuna danniya da zalunci a duniya ke aiwatarwa . wasu suka bada shawarar a konar da shi a wuta yayinda wasu kuma suka bada shawarar a kasha shi kai tsaye sais u rabu da damuwarsa.

Kamar yadda ayoyi na 68 zuwa 70 a cikin suratun ambiya suka yi nuni  daga karshe sun yanke shawarar  cinna wuta mai karfin gaske da jefa annabi Ibrahima (AS) a cikinta da majojawa don haka wannan ayar ke ci gaba da cewa; Suna kulla makircin aiwatar da kisa kan manzon Allah (AS) amma Allah ya tsiratar da manzonsa kamar yadda ya zo a cikin wasu ayoyin kur'ani  Allah ya umarci wutar da ta zama mai sanhi da bay a cutarwa  da zama salama ga Annabi Ibrahima (AS) . Wannan babban darasi da abin koyi da Karin imani ga ma'abuta imani da kara mika wuya ga kudurar Allah kan komi su kara nisantuwa da duk wata kudura ta zahiri da ta abin duniya.

A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku:

Na farko:a kullum hankali da tuinanin makiya addini shi ne hanyar cutarwa,azabtarwa ko kasha ma'abuta imani ,Kuma bas u yin riko da hanyar fahimta da gane gaskiya sai hanyar kare matsayi da mulki da dukiyarsu kawai kash ,tabewa ta kai tabewa.

Na biyu: Karamcin muminai bas hi ne zai sa su mika wuya ga zalunci da danniya ba.Misali Annabi Ibrahima (AS) Shi kadai ne amma bai sa ya daina fadawa kafirai da mushrikai gaskiya ba.

Na uku: Irada da kudurar Allah ta saman komi da yanayi da dabi'a  domi Shi ne Mahaliccinsu Dabi'ar wuta kuna amma da Allah ya so sai ta zama mai sanyi da salama ga annabi Ibrahima (AS).

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 25:

وَقَالَ إِنَّمَا اتَّخَذْتُم مِّن دُونِ اللَّهِ أَوْثَانًا مَّوَدَّةَ بَيْنِكُمْ فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا ثُمَّ يَوْمَ الْقِيَامَةِ يَكْفُرُ بَعْضُكُم بِبَعْضٍ وَيَلْعَنُ بَعْضُكُم بَعْضًا وَمَأْوَاكُمُ النَّارُ وَمَا لَكُم مِّن نَّاصِرِينَ

25- Kuma yace da su : Hakika baa bin da kuka rika wanin Allah sai gumaka kawai don kauna da take tsakaninku a rayiwar duniya,sannan ranar alkiyama wasunku za su kafirce wa wasu,kuma wasunku za su la'anci wasu,makomarku kuma wuta ce, ba ku kuwa da wasu mataimaka.

Annabi Ibrahima (AS) bayan Allah ya tsiratar da shi daga wannan wuta da makircin makiyan Allah bai daina kiran mushrikai zuwa ga kadaita Allah da bauta ba sai ma abin da ya ci gaba da daura ayar tambaya kan gumakan da suke bautawa . Idan muka yi dubi a cikin tarihi za mu ga kowace kabila da takama da jiji da kai kan gumkin da suke bautawa kuma a gurinsu alama ce da kasantuwar wannan kabila ko yayanta da matsayinta a tsakanin jama'a.Mutanan wannan kabila ta hanyar bautawa wannan gumki da suka sassaka da hannunsu  suna kara samar da hadin kai da kusanci a tsakaninsu bugu da kari a mahangarsu sun yi riko da akidar uwaye da kakannninsu da kuma girmama su da bautawa abin da suka bautawa. Sai Annabi Ibrahima (AS) y ace masu: Wanna tsari da riko na bautawa abin da uwaye da kakannunku suka bauta da samar da hadin kai da kusanci a tsakaninku da kauna a tsakaninku to a ranar kiyama za ku kasance a warwatse a wannan rana da lokaci kowane daya daga cikinku zai yi kokarin daura wad an uwansa laifin sabon da ya aikata na bautawa gumaka kuma kowane daya daga cikinku zai tsinewa  na sama da shi  ,jagorori da shugabannin mutananku da kabilarku da suka batar da ku. Daga karshe daga kasa har sama babba da karami babu wanda zai amince a daura masa ko ya dauki nauyin batar da kabilarsa.Sai zargin juna da daura juna laifi na bautawa gumaka cewa me yasa b aka yi tunani da kanka b aka bi  hanyar yin riko da hanyar iyaye da kakannu da ke cikin bata.

A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:Hadin kai da kusanci al'umma dole ya kasance karkashin lamari na hankali da tabbaci ba kamar bautar gumaka ba ko tabewa da fadawa tarkon shaidan ba.

Na biyu:Tunani da hankali dole su kasance sun sabawa son rai da kauna ta mutum ko bin iyaye da kakannnu.

Na uku:Masu kaunar juna a wannan duniya kan lamari da ya sabawa hankali a gobe kiyama za su zamanto makiyan juna da kyamar juna.

****************************
Daga karshe a cikin shirin na mu nay au masu saurare za mu saurari karatun aya ta 26 a cikin suratun Ankabut:

فَآمَنَ لَهُ لُوطٌ وَقَالَ إِنِّي مُهَاجِرٌ إِلَى رَبِّي إِنَّهُ هُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ

26- Sai Ludu ya gaskata shi, (Sai Ibrahimu) kuma ya ce: Hakika ni mai yin hijira  ne zuwa ga (umarnin) Ubangijina, hakika Shi Mabuwani ne  Mai hikima.

Annabi Ibrahima (AS) bayan da ya tsira daga wannan babbar wuta da Namrud ya jefa shi cikinta ,amma Allah yak are shi da fitowa lamin lafiya,mutum na farko da yay i imani da shi  da kasancewa tare da shi ,shi ne Lud (as) wanda daga bisani Allah y aba shi matsayin manonsa daisar da sakon shari'ar da Annabi Ibrahima (AS) ya zo da ita a tsakanin mutane. Annabi Ibrahima (AS0 bayan da ya ga duk da wannan babbar mu'ujiza a mai girma karara amma ba bubu wanda yayi imani da shi,sai ya sanar da  niyarsa ta yin gudun hijira na barin wannan gari nasa da na uwayensa  zuwa wani gari na daban da kiran mutane zuwa ga kadaita Allah da bauta don allah da neman yardarsa. Wanna gudun hijira har ila yau za ta say a tsira daga azabtarwar mutanansa kuma zai sami damar ci gaba da isar da wannan nauyi da ya rataya a wuyansa na kiran mutane zuwa ga kadaita Allah da bauta. Haka Manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa yayi hijira daga makka zuwa Madina domin kubuta daga takurawar Mushrikan Makka da ke takura masa da wadanda suka yi imani da shi  sai kuma isar da wannan sako na shiriya zuwa ga mutanen Madina.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu :

Na farko: Manzonni da Annabawan allah ba kamar sarakuna ne masu son kare matsayi da mulkinsu ta kowa ce hanay ko kokarin fadada mulkinsu ba , sai dai kokarin yada addinin Allah  da karfafa juna su waliyan Allah kamar yadda Annabi Lud (AS) yayi na karfafa Annabi Ibrahima (AS) da yin imani da shi da taimaka masa a wannan hanya ta kiran mutane zuwa ga kadaita Allah da bauta.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..