Apr 17, 2017 12:42 UTC

Suratul Ankabut, 27-30 (721)

Bismillahi rahamani Rahim,

Jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

***********************************

To madallah masu saurare za mu fara shirinmu nay au tare da sauraren karatun aya ta 27 a cikin suratul Ankabut:

وَوَهَبْنَا لَهُ إِسْحَاقَ وَيَعْقُوبَ وَجَعَلْنَا فِي ذُرِّيَّتِهِ النُّبُوَّةَ وَالْكِتَابَ وَآتَيْنَاهُ أَجْرَهُ فِي الدُّنْيَا وَإِنَّهُ فِي الآخِرَةِ لَمِنَ الصَّالِحِينَ

27- Muka kuma yi masa baiwa da (dansa) ishaka da kuma jikansa Yakubu, Muka kuma sanya annabta da saukar da littattafai cikin zuriyarsa,Muka kuma bas hi ladansa a duniya,kuma a lahira ba shakka yana daga salihai.

A cikin shirin da ya gabat a jumulce mun kawo bayani ne kan tarihi annabi Ibrahima (AS) to wannan ayar da muka saurara cikin ayoyin da suka gaba ne da ke cewa:bayan da Annabi Ibrahima (AS) yayi gudun hijira domin ci gaba da wannan aiki na manzonci na kiran mutane zuwa ga kadaita Allah da bauta  sai allah y aba shi wata babbar kauna da arzita shi da da tsarkakke  da zai ci gaba da yin riko da hanyarsa ta kadaita Allah da bauta kuma cikin  rahama da lutifin Allah mai kyauta  ya bawa wannan da na Ibrahima matsayin annabci don ci gaba da haskaka hanayr imani a tsakanin mutanansa da al'ummarsa. Kamar su Ishak da dansa Yakubu da dansa Yusuf da kuma Musa da Haruna da Suleimanu (AS) da dukan zuriyar annabi Ibrahima (AS) da suka yi riko da tafarkin Allah da isar da sakon Allah madaukakin sarki. Wannan matsayi da daukaka da kyauta daga Allah ta hada duniya da lahira ma'ana sunada matsayi da daraja  a wannan duniya haka sunada a ranar lahira kuma shi da dan albarka yana haskaka kansa ya kuma haskaka ma'aifansa kuma ko bayan mutuwa ba za a manta da shi ba.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Samin da salihi mai albarka wata kyauta ce babba daga Allah.

Na biyu: Daya daga cikin kyauta da Allah ke bawa bayunsa a wannan duniya wata sakayya ce ta Allah wa wannan duniya ga bayunsa salihai na gari.

Na Uku:Sabanin  ahangar tababbu da ke hada duniya da lahira a matsayi guda a'a a koyarwa ta addinin musulunci mutum ya aikata alheri da rayuwar lahira a daidai lokaci guda kuma kar yay i watsi da rayuwar wannan duniya ma'ana ya rayu rayuwa mai ingancci da tsabta.

To yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 28 da 29 a cikin suratun Ankabut:

وَلُوطًا إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ إِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ مَا سَبَقَكُم بِهَا مِنْ أَحَدٍ مِّنَ الْعَالَمِينَ

28- Kuma ka tuna Ludu lokacin da y ace da mutanensa: Hakika ku kuna zai ke wa mummunan aiki wand aba wani mutum guda daga talikai da ya rigae ku aikata shi.

 

أَئِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ وَتَقْطَعُونَ السَّبِيلَ وَتَأْتُونَ فِي نَادِيكُمُ الْمُنكَرَ فَمَا كَانَ جَوَابَ قَوْمِهِ إِلاَّ أَن قَالُوا ائْتِنَا بِعَذَابِ اللَّهِ إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ

 

29- Yanzu kwa rika zai ke wamaza,ku kuma rika tsare hanya kuna yin fashi,kuma kuna aikata abin ki a cikin majalisinku? Ba wani jawabi da ya fito daga bakin mutanensa sai cewa suka yi: To ka zo mana da azabar Allah idan ka kasance cikin masa gaskiya.

Bayan Annabi Ibrahima (AS) wadannan ayoyi na bayani ne kan takaitaccen tarihi da abubuwan da suka wakana tsakanin annabi Lud (AS) da mutanansa kuma Annabi Lud (AS) yayi lokaci guda da annabi Ibrahima (AS) yayi ta kokarin shiryar da mutanasa da kiransu zuwa ga kadaita Allah da bauta amma ba wai kawai mutanansa sun bijirewa wannan kira na gaskiya sai ma suka yi barazanar kasha shi ko tilasta masa yin gudun hijira matukar ya ci gaba da wannan jawabai nasa na su bar aikin da suke aikatawa. To wadannan ayoyi da muka saurara suna nuni da mafi munin banna da aiki da mutum ke aikata wanda ko dabbobi a tsakaninsu ba a gani suna aikata da cewa;Manzon Allah ,annabi Lud (AS)a kullum ba dare ba rana yana tunatar da mutanansa munin aikin da suke aikatawa na saduwa a tsakanin yan jinsi daya inda maza bas u damu da matansu na aure ba da hakan ke barazana ga yaduwar jinsin mutum da daina haifuwa  kuma wannan aiki ya sabawa dabi'a ta rayuwa ta saduwa tsakanin namiji da mace hatta dabbobi masu bin gariza ba su aikata wannan mummunan aiki.

Mutanan Annabi Lud (AS) ba wai suna aikata wannan aiki na sabo a boye ba hatta wanda yake aikata luwadi a boye suna hukumta shi suna alfahari da aikata wannan banna a bayyanai da kara cusa wannan banna da yada ta a tsakanin  jama'a da gurbata zamantakewa. Ci gaban ayar na cewa: Su bas u sauraren irin galgadin da annabi Lud (AS) key i masu kuma ba a shirye suke bas u gyara sai ma suke yi masa izgili da wa annabi Lud (AS) cewa; idan Allanka yana fushi da wannan aiki da muke aikatarawa kuma zai iya sabkar mana da azaba to k ace masa ya sabkar mana da azaba a wannan duniya da hallakar da mu inji su. A nan abin da suke nufi ta wata mahangar  suna cewa annabi Lud (AS)  kana bin da kake rayawa  na manzonnci karya kake yi  wa iyazu billahi kuma kar ka dame mu kan aikin da muke aikatawa.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyar kamar haka;

Na farko:Jagororin addini bayan kiran mutane zuwa ga kadaita Allah da bauta  sai kuma sun yi fito na fito da gwagwarmaya da fasadi a tsakanin jama'a da kokarin tsarkake jama'a daga fasadi.

Na biyu; idan fasadi yayi kanta a tsakanin jama'a bai dace k ace ba kira da kyaukyawa da hanni ga mummuna bay a tasiri ko mai ya sa z aka damu kanka wannan bai dace ba.

Na uku:Manzonnin Allah na karfafa mana zuwa ga aikata gariza kan hanyar da ta dace kamar aure a dabra guda suna fada da fasadina gariza irin ta dabbobi.

Na hudu: idan banna da sabo bai bayyana a tsakanin jama'a a fili karara sai a ci gaba da fadakarwa a daidaiku amma idan kuma lmarin ya gurbata  ba a jin kumyar aikata sabo to ya wajaba kan kowa ya tsayi tsaye a kalubalanci wannan matsala.

Na biyar: aikata sabo na saduwa a tsakanin yan jinsi daya da wasu kasashen turai ke ganin yanci ne babu wani addini da ya amince da hakan kuma abin da annabawa da manzonni suka yaka dole muma mu yaki wannan lamari na gurbata al'umma.

*************************

قَالَ رَبِّ انصُرْنِي عَلَى الْقَوْمِ الْمُفْسِدِينَ

30- Sai Ludu yace: Ya Ubangijina ,Ka taimake ni kan mutanen nan mabarnata.


Lokacin da mutanan annabin Lud (AS) suka zarge shi da karya da karyata kiran shiriya da ya zo masu da shi da sakon manzonci  sai ya nemi taimakon allah  domin ya tabbatar masu da gaskiyarsa ba karya yake ba da zo masu da mu'ujizar  da zai sa su yarda da manzoncinsa ko hakan zai sa su ankarta da karbar gaskiya da kuma rusa karya da sabon da suke aikatawa da kuma suke takama da wannan sabo da suke aikatawa bas u ganin muninsa sai ma ganin munin aikata kyakkyawa. Su mutane ne fasikai  da suka yi nisa a aikata sabo da banna  ,su ne mutanan da suka kauce wa hanya madaidaiciya ,idan wani mutuman kirki mai tsarki ya tunatar da su sais u yi masa izgili da muzanta shi.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu;

Na farko: a koyarwa irin ta addinin musulunci saduwar yan jinsi daya wani nau'I ne na fasadi a doran kasa duk wanda aka kama ana yi masa hukumci mai tsanani .

Na biyu: a kokarin kawo karshen fasadi a tsakanin jama'a dule mutane baki daya wajen yakar wannan lamari da neman taimakon Allah da ya taimaka mana wajen ganin baya da karshen wannan lamari.

 

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..