Apr 17, 2017 12:51 UTC

Suratul Ankabut, 31-35 (722)

Bismillahi rahamani Rahim,

jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na mu na yau tare da sauraren karatun ayoyi na 31 da 32 a cikin suratun ankabut:

وَلَمَّا جَاءَتْ رُسُلُنَا إِبْرَاهِيمَ بِالْبُشْرَى قَالُوا إِنَّا مُهْلِكُو أَهْلِ هَذِهِ الْقَرْيَةِ إِنَّ أَهْلَهَا كَانُوا ظَالِمِينَ

 

31- Lokacin kuwa da manzanninmu suka zo wa  Ibrahimu da albishir,sai suka ce: Hakika mu masu hallaka mutanen wannan alkarya ne,hakika mutanenta sun kasance azzalumai.

قَالَ إِنَّ فِيهَا لُوطًا قَالُوا نَحْنُ أَعْلَمُ بِمَن فِيهَا لَنُنَجِّيَنَّهُ وَأَهْلَهُ إِلاَّ امْرَأَتَهُ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ
 

32- Sai Ibrahimu yace: Hakika a cikinta akwai Ludu.Sai suka ce: Mu muka fi sanin wadanda suke cikinta,ba shakka za mu tserar da shi tare da iyalinsa,sai matarsa  kawai da ta kasance cikin wanzazzu da za a hallaka.

A shirin da ya gabata kun yadda mutanen annabi lud (AS) da suka yi fice a fasadi da banna a doran kasa kuma bas u boyewa a maimakon su saurari jawabi da kiran gaskiya na annabi Lud (AS) sai suka kara tabka wani babban laifi  na yin izgili  da zargin annabin Allah da sunan makaryaci.Amma Annabi Lud (AS) wannan bai sa shi ba yin kasa a guiwa ko nuna kasawa da mika wuya da matsin lamba da barazanar da suke yi mas aba sai ma abin da ya ci gaba tare da bukatar Mai duka Allah madaukakin sarki da ya taimaka mashi ya ci nasara kan wadannan mutane fasike mabannata a doran kasa. Wadannan ayoyi da muka saurara na cewa; Allah madaukakin sarki ya aika malaiku zuwa ga annabi Ibrahim (AS) domin bas hi albishir da zai sami da  a wannan shekaru nasa na tsuha da kuma dayan labarin ya shafi azabar da za a sabkarwa mutanen annabi Lud(A) wanda yana isar da sakon Manzonci ne karkashin shari'ar Annabi Ibrahim (AS) a wannan yanki kuma Allah ya amsa addu'ar annabi Lud (AS) kan mutanansa wadanda suka yi fice a fasikanci babu wata alamar yin tuba. Kur'ani na cewa;Annabi Ibrahima (AS) da jin wannan labara na sabkar azaba daga Allah sai ya shiga damuwar halin da annabi Lud (AS) zai shiga musamman ganin yadda yana rayuwa ne a wannan gari da azabar Allah za ta sabka.Ganin haka sai Mala'ikun da Allah ya turo suka amsa masa da cewa: Karkashin sunnar Allah ,ba mu azabartar da waliyan Allah na gari tare da mabannata kuma wadanda suka sabawa dokokin Allah da aikata banna a doran kasa azabar ke shafa. Za mu tsiratar da muminai daga cikinsu sai matar annabi Lud da ta kasance cikin kafirai mabannata duk da cewa ta rayu a gidan annabtaka amma ba ta yi aikin da za ta tsira da rai da rayuwarta ba daga wannan azaba.

Daga wadannan ayoyi za mu ilmanu da abubuwa hudu kamar haka;

Na farko:Mala'ikun Allah sune masu lura da lamarin da ke gudana kamar yadda suna bayar da albishir da labarin sabkar rahama haka kuma suna zuwa da kashedi na sabkar azaba ko wani laba'I da fushin Allah.

Na biyu:kaucewa hanya ta gaskiya wajen biyan bukata ta gariza zalunci ne a karan kansa ,kuma zalunci ne kan iyalai haka zalunci ne da zamantakewar jama'a.

Na Uku: Idan zalunci a tsakanin jama'a ya yadu da mamaye ko'ina ,al'umma na kara kusantar hallaka ne.

Na hudu: Uwaye da yayansu kowa nada hakki da yancin zabar hanyar da ya ga ta dace da shi ,kamar yadda matar annabi Lud (AS) ta zabi kafirci da ganin sakamakonsa.

*****************************************

To madallah za mu ci gaba da shirin nay au tare da sauraren aya ta 33 zuwa 35 a cikin wannan sura ta ankabut:

 

وَلَمَّا أَن جَاءَتْ رُسُلُنَا لُوطًا سِيءَ بِهِمْ وَضَاقَ بِهِمْ ذَرْعًا وَقَالُوا لا تَخَفْ وَلا تَحْزَنْ إِنَّا مُنَجُّوكَ وَأَهْلَكَ إِلاَّ امْرَأَتَكَ كَانَتْ مِنَ الْغَابِرِينَ

 

33- Lokacin  kuma da manzanninmu suka zo wa Ludu,sai yayi bakin ciki da zuwansu,zuciyarsa kuma ta kuntata saboda su, sai suka ce da shi: kada ka ji tsoro,kuma kada ka damu,hakika Mu masu tserar da kai ne tare da iyalinka,sai matarka kawai da ta kasance cikin wanzazzu da za a hallaka.

إِنَّا مُنزِلُونَ عَلَى أَهْلِ هَذِهِ الْقَرْيَةِ رِجْزًا مِّنَ السَّمَاء بِمَا كَانُوا يَفْسُقُونَ

 

34- Hakika mu masu saukar da azaba mai tsanani ne daga sama a kan mutanen wannan alkaryar saboda abin da suka kasance suna aikatawa na fasikanci.

 

وَلَقَد تَّرَكْنَا مِنْهَا آيَةً بَيِّنَةً لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ

35- Hakika Mu Mun bar aya bayyananniya game da ita alkaryar ga mutanen da suke hankalta.

Karkashin wadannan ayoyi Annabi Ludu (AS) bai gane malaikun da Allah yab turo mas aba saboda sun yi shigar matasa masu fuska mai kyau  don haka ya ji tsoron wadannan baki nasa  su fuskanci takurawa da wulakanci daga fasikan mutanansa da suka gurbata da aikata banna a doran kasa.Kan haka ya shiga damuwa da tsoro gashi kuma babu abin da zai iya da zai hana mutanan aikata banna  kuma cin mutuncin bakinsa wani cin mutunci ne a gare shi. Ganin haka da wannan hali da yake ciki sai mala'iku suka ba shi masaniya da kwantar masa da hankali ya samu nucuwa ta cutuwar fasikan mutanansa ba za ta riske su.Saboda wadannan mutane fasikai nan ba da jimawa azaba da fushin Allah za sa same su hatta bulbidinsu ba za su yi saura ba sai dai bilbidin gidajensu da samu zama darasi ga sauran al'ummomi a nan gaba. Karkashin wadannan ayoyi nacewa da ci gaba da aikata sabo da banna da yada ta a tsakanin jama'a lamari ne mai matukar hadarin gaske. Kuma ba wai na shafar wasu mutane ne yan tsuraru su kadai ba a'a yana shafar dukan rayuwar jama'a da makomarsu ne musamman idan azabar ta sabka na shafar kowa ne sai wanda allah ya kebe da zama darasi ga sauran. Karkashin wasu ayoyin kur'ani da farko Allah ya fara da girgisa wannan gari girgizar kasa mai karfin gaske  daga bisani kuma aka yi masu da ruwan duwatsu na azaba inda duwatsu da kasa suka rufe su da ransu tamkar gawarwaki.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu:

Na farko: Idan al'umma ta gurbata da sabo akwai yuyuwar wannan fasadi ya yadu a ko'ina idan lamarin ya kai haka hatta gidan mutanan kirki  ba su cikin tsaro domin damuwa da fargaba kan makomar yayasu za ta mamaye zucciya da tunaninsu.

Na biyu: Kare mutunci bako na kan wuyan mai gida ne kuma dole ne a lura da kare mutuncinsa.

Na uku: Mumini yana da kishin addininsa kuma duk inda ya ga kaucewa hanya da fasadi yana fada da shi ba wai ya kama hannu y ace ba ruwansa ba kana bin da yake faruwa ke zai faru.

Na hudu: matsayin wani bay a karewa da ba wa waninsa mutunci da daukaka kowa aikinsa ne zai fushe shi misali; matar lud (AS) zaman da ta yi da mijinta bai amfane ta da komi ba a lokacin sabkar azaba saboda mummunan aikinta kamar yadda matar fir'auna ta sami tsira da kusanci da Allah saboda imani da aikinta na kirki kuma zama da fir'auna bai cutar da imani da aikinta da komi ba sai ma daukaka.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..