Apr 17, 2017 13:03 UTC

Suratul Ankabut, 36-40 (723)

Bismillahi rahamani Rahim,

Jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

***********************************

To Madallah masu saurare za mu fara shirin nay au ne da sauraren karatun aya ta 36 da 37 a cikin wannan sura ta Ankabut:

 

وَإِلَى مَدْيَنَ أَخَاهُمْ شُعَيْبًا فَقَالَ يَا قَوْمِ اعْبُدُوا اللَّهَ وَارْجُوا الْيَوْمَ الآخِرَ وَلا تَعْثَوْا فِي الأَرْضِ مُفْسِدِينَ

 

36- Mun kuma aika wa mutanen Madayana dan uwansu Shu'aibu, sai yace: Ya ku mutanena,ku bauta wa Allah,kuma ku ji tsoron ranar lahira,kuma kada ku rika yin lalata a bayan kasa kuna barna.

 

فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَتْهُمُ الرَّجْفَةُ فَأَصْبَحُوا فِي دَارِهِمْ جَاثِمِينَ

 

37- Sai suka karya  shi,sannan girgizar kasa ta kama su ,suka wayi gari duddurkashe a mace cikin gidajansu.

A cikin shirin da ya gabata mun yi bayani ne kan makomar mutanan annabi Lud (AS) da yadda karshensu ya munana biyo bayan ayyukan assha da banna da suka aikata a doran kasa ,to wadannan ayoyi da muka saurara suna bayani ne kan sakon da aka turo annabi Shaibu (AS) da cewa: Shi ma annabi Shuaibu (AS) kamar sauran annabawa da manzonnin da suka gabata ya kirayi mutanansa zuwa ga gadaita Allah da bauta shi kadai da yin imani da ranar tashin kiyama da cewa; sabo da sabawa dokoki da umarnin Allah yana haddasa fasadi da tabewa a doran kasa haka yana haddasa zalunci da rashin adalci da rugujewar tsarin zamantakewar jama'a.Amma kash kamar sauran al'ummomin da suka gabata su ma mutanan annabi shuaibu (AS) sun karyata wannan kira da manzon Allah  da bijirewa wannan wa'azi da kashedi na manzon Allah (AS) wanda ya damu da kuma kokarin yin gyara a cikin al'ummarasa amma sai suka bijire kash. Kur'ani na cewa: Makomarsu karyatawa da aikata sabo fuskantar fushi da azabar Allah a wannan duniya inda girgizar kasa ta riske su da hallakar da su.

A cikin wannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Taudihi na kadaita allah da bauta da amincewa da tashin kiya na kan gaba a kiran Annabawa.

Na biyu:Manzonni na kiran mutanansu zuwa ga shiriya cikin kauna da tausayi nay an uwantaka ba ta hanyar nuna fifiko da girma ba.

Na uku: Aikata sabo da fasadi na haddasa fushin Allah da gaggauta sabkar azaba daga Allah.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 38 a cikin wannan suta ta ankabut:

 

وَعَادًا وَثَمُودَ وَقَد تَّبَيَّنَ لَكُم مِّن مَّسَاكِنِهِمْ وَزَيَّنَ لَهُمُ الشَّيْطَانُ أَعْمَالَهُمْ فَصَدَّهُمْ عَنِ السَّبِيلِ وَكَانُوا مُسْتَبْصِرِينَ

 

38- Kuma Mun hallaka Adawa da samudawa,hakika abin da ya faru a gare su kuma ganin sa a fili a gidajensu,kuma Shaidan ya kawata musu ayyukansu sannan ya kange su daga hanya madaidaiciya ,sun kuma kasance da hankalinsu.

Wannan ayar tana bayani ne kan makomar mutanan adawa da samudawa da aka aiko masu manzonnin allah Annabi Hud da annabi Salihu (AS) wadanda aka daukarawa nauyin shiryar da su ,amma a maimakon su amsa kiran shiriya na wadannan manzonni sai suka karyata da nuna bakar adawa da bijirewa da sabawa duk wani umarni na Allah da manzannin suka zo da shi.

Kur'ani na Magana ne kai tsaye da mutanan Makka da cewa; su samudawa da adawa wadannan kabilu biyu sun gamu da fushin Allah inda aka ruguza gidajensu da garuruwansu da suke kudu da kuduncin Makka a nan kan hanyar Sham da Yamen .Kuma kullum kuna ganin makowarsu a ziyarce-ziyarcenku da kuke yi amma me ya sa ba ku daukan darasi kana bin da ya faru da su. Ci gaban ayar na cewa dalilin da ya sa wadannan al'ummomi biyu suka abku a cikin wannan azaba da fushi na Allah  shi ne bin shaidan  da rungumar dadin duniya bayan sun fahimta da sanin duk wasu alamomi na gaskiya  da fitira a kiran da manzonni suka yi masu kuma suna da zabin zabar bin kiran gaskiya amma suka ki da zabarn sabo da bata da yin riko da hanyar shaidan.

Daga cikin wannan ayar za mu fahimci abubuwa biyu kamar haka:

Na farko: Abubuwan da suka faru a tsawon tarihi ya zama darasi a gare mu da rayuwarmu da kuma kare kan mu daga fadawa tarkon da suka fada mummuna.

Na biyu:Aikin shaidan ne kyayatar da mummunan aiki dole mutum ya kasance mai aiki da hankalinsa da fitirar da Allah y aba shin a aiki da hanakali wajen kaucewa tarkon shaidan  kamar jiji da kai da takama da dukiya mai karewa da saka mutum cikin bata da tabewa duniya da lahira.

****************************

Daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 39 da 40 a cikin suratul Ankabut:

 

وَقَارُونَ وَفِرْعَوْنَ وَهَامَانَ وَلَقَدْ جَاءَهُم مُّوسَى بِالْبَيِّنَاتِ فَاسْتَكْبَرُوا فِي الأَرْضِ وَمَا كَانُوا سَابِقِينَ

 

39- Kuma Mun hallaka karuna da Fir'auna da Hamana,hakika kuma Musa ya zo musu da ayoyi mabayyana,sai suka yi girman kai a bayan kasa,ba su kuma kasance masu guje wa azaba ba.

 

فَكُلا أَخَذْنَا بِذَنبِهِ فَمِنْهُم مَّنْ أَرْسَلْنَا عَلَيْهِ حَاصِبًا وَمِنْهُم مَّنْ أَخَذَتْهُ الصَّيْحَةُ وَمِنْهُم مَّنْ خَسَفْنَا بِهِ الأَرْضَ وَمِنْهُم مَّنْ أَغْرَقْنَا وَمَا كَانَ اللَّهُ لِيَظْلِمَهُمْ وَلَكِن كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ

 

40- Kowanne dayansu Mun kama shi da laifinsa;daga cikinsu akwai wadanda muka aiko wa da duwatsu,akwai kuma wadanda tsawa ta kama su,kuma akwai wadanda Muka kifar da su cikin kasa,akwai kuma wadanda Muka nutsar a ruwa .Allah kuma bai kasance Yana zaluntar su ba,sai dai kawai kansu suke zalinta.

Wannan ayoyi da muka saurara suna bayani kan makomar masu girman kai da jiji da kai a tsawon tarihi da yadda karshensu ya munana kamar Karuna da fir'auna da hamana. Shi Karuna yawan dukiya da arzikin da allah ya ba shi ne ya sanya masa girman kai da dagawa. Shi ma fir'auna karfin mulki da iko ya sa yana ganin kansa saman kowa da daukaka kansa kan kowa da fifita kansa ta hanyar girman kai to shi ma haka wazirinsa Hamana ya bi sahun mai gidansa fir'auna ta wannan girman kai da ji da karfin iko da taimaka masa a aika-aikarsa. Annabi Musa (AS) yayi kokarin fadakarwa da shiryar da wadannan mutane uku t hanyar wa'azi da kafa masu hujjoji amma sun ki karbar gaskiya da yin riko da hanya madaidaiciya sai ma suka rungumi hanyar yin fito na fito da annabi musa da yin watsi da sakon da Allah ya turo shi da shi don shiryar da jama'a. Amma yaya makomarsu ta kasance ,cikin ikon,kasa ta bude Karuna ya fada cikin ya hallaka aka bisne,haka shi ma fir'auna da hamana ya hallaka da nutsewa a cikin ruwan maliya. Ci gaban ayoyin na bayani ne kan nau'i-nau-in azabar Allah a wannan duniya kamar yadda ya zo wasu ayoyin kur'ani an hallakar da Adawa da azabar dufana na tsawon mako guda ba dare  ba rana da hallakar da su baki daya. Suma Samudawa an aiko masu da tsawa da girgizar kasa da hallakar da su da babagowar ruwa da hallakar da su baki daya tun a wannan duniya.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko:Karshen girman kai hallaka ne kuma karfin iko da dukiya ba za su iya tsiratar da mutum ba daga wannan hallaka.

Na biyu:karfin Allah ya sama da komi da kowa ,abin da ya kamata duk wani mai adawa da gaskiya ya san da haka.

Na uku: Azabar Allah na fuskantar kafirai da masu sabo ta fuskoki daban daban da hanyoyi daban daban.

Na hudu: Makomar kowane mutum na karkashin irin aikin da ya aikata ne.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..