Suratul Ankabut, 41-45 (724)
Suratul Ankabut, 41-45 (724)
Bismillahi rahamani Rahim,
Jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.
***********************************
To madallah masu saurare barka da sake saduwa kuma a yau za mu fara shirin ne da sauraren aya ta 41 da 42 a cikin suratl Ankabut:
مَثَلُ الَّذِينَ اتَّخَذُوا مِن دُونِ اللَّهِ أَوْلِيَاء كَمَثَلِ الْعَنكَبُوتِ اتَّخَذَتْ بَيْتًا وَإِنَّ أَوْهَنَ الْبُيُوتِ لَبَيْتُ الْعَنكَبُوتِ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ
41- Misalin wadanda suka riki wasu iyayen giji ba Allah ba,kamar misalign gizogizo ne da ya saka gida,hakika kuwa lallai gidan gizogizo shi ya fi kowanne gida rauni,da sun kasance suna ganewa.
إِنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا يَدْعُونَ مِن دُونِهِ مِن شَيْءٍ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ
42- Hakika Allah Yana sane da kowane abu da suka bauta wa wanda Shi ba. Kuma Shi ne Mabuwayi Mai hikima.
A cikin shirye-shiryen da suka gabata mun yi magkonni muna bayani kan mummunan makomar wadanda suka bijirewa kiran shiriya na manzonnin Allah (AS) da aka turo masu da kuma kafircewar da suka yi inda ta kai su,to wadannan ayoyi da muka saurara da take dauke da sunan wannan sura ta ankabut ita tana bayani ne kan makomar wadanda suka ki amsa kiran manzonnin Allah a baya da kuma a nan gaba da aka kwatamta matsayi da halin kafirai da gidan tautau da cewa: duk wani ko wadanda suka riki wanin Allah ba Allah a matsayin abin bauta komin karfin ikonsa da mulkinsa kamar fir'auna a gaban kudura da iradar Allah shi ba komi ba ne tamkar gidan tautau ne da yafi komi rauni domin hatta iska mai laushi tana rusa gidan tautau to wadanda ke bautawa wanin Allah da dogaro da shi a gaskiya tamkar sun yi dogaro ne da gidan tautau da duk wanda ya dogara da shi bas hi da tabbas da nucuwa a rayuwa a yanayi na tsanani da kumci na rayuwa.
Idan Mushrikai suna da masani da tsinkayen nesa abin da suke dogaro da shi a bauta yafi gidan tautau rauni kuma sun yi a asarar abin dogaro kuma da sun sani da ba su riki wani abu ko wata halitta abin bauta domin daga karshe kowa da komi za a koma ga Mahalicci mai duka mai komi.
A cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar:
Na farko;daya daga cikin hanyoyin da kur'ani ke bi wajen wa'azi akwai bada misali na fadakarwa da abubuwa na hakika da muke ani a zahiri a rayuwarmu.
Na biyu: duk gini da aka gina da imani shi ne yafi karfi da karfo da ginuwa amma shi ginin da aka gina da shirka to rushasshe ne ba dawwama.
Na uku: Duk wani abu da z aka yi dogaro da shi ba allah ba tamkar ka yi dogaro ne da gidan tautau mafi rauni don haka ka dogara da Allah Shi ne tabbas.
Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 43 da 44 a cikin wannan sura ta ankabut:
وَتِلْكَ الأَمْثَالُ نَضْرِبُهَا لِلنَّاسِ وَمَا يَعْقِلُهَا إِلاَّ الْعَالِمُونَ
43- Wadancan misalan Muna buga su ne ga mutane,ba kuwa wanda yake hankaltar s sai malamai kawai.
خَلَقَ اللَّهُ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ بِالْحَقِّ إِنَّ فِي ذَلِكَ لآيَةً لِّلْمُؤْمِنِينَ
44- Allah Ya halicci sammai da kassai da gaskiya .Hakika a game da wannan lallai akwai aya ga muminai.
A wadannan ayoyin ana bayani ne da muhimmancin misalan da alkur'ani ke amfani da su da cewa;kar ku yi zaton wadannan misalai masu sauki ne da rashin amfani ,ku sani suma maganar Allah ce domin fahimtar da mu da fayyace mana hakikar imani da kafirci.Idan wadannan misalai a gurin yawacin mutane masu sauki ne amma a gurin masana suna kollon abin cikin surfin tunani da nazari da kima ta ilimi.Kuma duk wani abu na nazari da tsari yana jan hankalin masana kuma masu hankali da aiki da tunani na girmama shi tabbas. Ci gaban ayar na jaddadawa ne kan Halittun Allah da cewa; Allah abin bauta ba da tarayya ba Shi ne ya halicci komi da kowa ,kuma Shi ne mabuwayi mai hikima. Babu wani abu da ya halitta sai cikin tsari da hikima da anfani kuma kan gaskiya.Ma'abuta imani sun san da wannan lamari sani na hakika amma su mushrikai da kafirai ba a shirye suke ban a su fahimci wannan lamari na gaskiya.
Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:
Na farko:Misalai da ke cikin kur'ani sun kumshi surfin ilimi da tsari kuma masana ne kai fahimtar hakan.
Na biyu:Wannan duniya an halicce ta ne kan buri da tsari ba wai kawai haka kwatsam ta samar da kanta ba.
Na uku:Mushrikai da kafirai na da iyaka wajen fahimtar abubuwan mamaki na halitta amma su ma'abuta imani suna isa ne zuwa ga Allan da ya halicci duk wani abu a wannan duniya da sauran duniyoyi.
***************************
Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 45 a cikin wannan sura ta ankabut.
اتْلُ مَا أُوحِيَ إِلَيْكَ مِنَ الْكِتَابِ وَأَقِمِ الصَّلاةَ إِنَّ الصَّلاةَ تَنْهَى عَنِ الْفَحْشَاء وَالْمُنكَرِ وَلَذِكْرُ اللَّهِ أَكْبَرُ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا تَصْنَعُونَ
45- Ka karanta abin da ake yo maka wahayinsa na alkur'ani ,ka kuma tsai da salla,hakika salla tana hana alfasha da kuma abin ki.Kuma hakika ambaton Allah shi ne mafi girma ,kuma Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa.
Wannan aya tana Magana ne kai tsaye da Manzon Rahama (SWA) amma maganar bas hi kadai ta shafa ba ma'ana ta shafi duk wani ma'abucin imani.Allah yayi Magana ne kai tsaye da manzonsa domin jan hankalin mumunai fiye kuma su maida hankali kan muhimmancin lamari da kyau. A cikin wannan ayar ayyuka biyu masu muhimmanci aka umarce mu,na farko karatun kur'ani na biyu kuwa tsaida sallah.Kuma lamari ne da ke a fili a dabi'ance ci gaba da aiki da wadannan ayyuka biyu tasirinsu zai bayyana a rayuwarmu. Kuma yin sako-sako da su alama ce ta raunin imani saboda Kur'ani da tsaida sallah abubuwa biyu ne da ke kara karfin imani musamman karatun kur'ani idan ya hadu da yin nazari da tunani a cikin ayoyin Allah yafi tasiri da karfafa imani.
Ita kanta tsaida sallah a rana raka'o'I 17 ne na sallolin wajibi idan aka yi su yadda ya kamata tare da nucuwar zucci , na nisanta mutum daga aikata sabo da ayyukan assha.Daga cikin fa'idodin sallah na tsarkake zucciya da ruhin mutum daga gurbata. Wannan kadan ke nan daga falalar sallah domin mafi muhimmanci mai tsaida sallah a kullum yana tare da ambaton Allah da ni'imominsa kuma samin wannan matsayi wata babbar martaba da daukaka ce.
A cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa hudu:
Na farko:Karatun kur'ani da tsaida sallah suna sahun gaba a tsarin tarbiya a musulunci kuma wannan hanyar ce waliyan allah ke anfani wajen kusanci da Allah.
Na biyu:Kur'ani shi ke bayani kan falsafar wasu hukumce-hukumcen addini kamar sallah da ke nisantya mutum daga aikata sabo da tsarkake masa ruhi da kara kusantar da shi da Allah.
Na uku: Aikata ayyukan masu kyau kamar karatun Kur'ani da tsaida Sallah a dabi'ance na nisantar da mutum daga ayyukan maras kyau a rayuwa da addini.
Na hudu: Sallah nada matsayi mai girma wajen gyaran mutum da al'umma.
To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..