Apr 19, 2017 11:56 UTC

Suratul Ankabut, 46-49 (725)

Bismillahi rahamani Rahim.

Jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

***********************************

To madallah masu saurare za mu fara shirin nay au ne tare da sauraren karatun aya ta 46 a cikin suratul Ankabut kamar haka:

 

وَلا تُجَادِلُوا أَهْلَ الْكِتَابِ إِلاَّ بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ إِلاَّ الَّذِينَ ظَلَمُوا مِنْهُمْ وَقُولُوا آمَنَّا بِالَّذِي أُنزِلَ إِلَيْنَا وَأُنزِلَ إِلَيْكُمْ وَإِلَهُنَا وَإِلَهُكُمْ وَاحِدٌ وَنَحْنُ لَهُ مُسْلِمُونَ

 

46- Kuma kada ku yi jayayya da ma'abota littafi Yahudawa da Nassara sai ta hanyar da ta fi kyau,sai dai wadanda suka yi zalunci daga cikinsu,kuma ku ce: Mun ba da gaskiya da abinda ka saukar mana,da kuma Ubangijinmu da Ubangijinku daya ne,kuma mu masu mika wuya ne dare shi.

A cikin ayoyin da suka kagata a cikin shirye-shiryen daa suka gabata suna bayani ne kan yadda kafirai da mushrikai ke musanta da karyata maganar bautawa Allah daya abin bauta da gaskiya.Amma wannan ayar ta zo da wani batu na hanyar da ya kamata mu tattauna da kalubalantar ma'abuta littafi kamar kiristoci da yahudawa.Da farko a wani gimshiki Ayar ta shaida mana cewa;idan za mu tattauna da ma'abuta littafi da farko kuma kasance masu girmama su a cikin ladabin Magana da amfani da kalmomi na ladabi da nuna kusanci .Sai kuma anfani da hujjoji na hankali da dalili da hujjoji masu karfi kuma kar mu nuna masu mu muna sama da su domin hakan zai hana Magana da jawabin da za mu yi masu ya ratsa jiki da zucciyarsu kuma ya zama shimge tsakaninmu da wadanda ke neman fahimtar gaskiya daga cikinsu. Sai dai yawancin lokaci masu tattauna da kalubalantar juna bas u girmama juna da aiki da ka'idar girmama juna don haka wani lokaci kar girmama wanda ake tattauna da shi ya kai ku ga kaskanci a gaban mai girman kai da jiji da kai da zubar da mutuncinku a gaban jama'a.

Ci gaban ayarya umartar mu da lura da mushrikai a tsakanin sauran addinai da Allah ya turo da cewa: da farko mu yi kokarin fara tattauanarwar da su da abubuwa da muka hade gurin guda da su kamar imani da Allah  da littafen da aka sabko  da bukatar su da mu da su baki daya mu mika wuya ga Allah da kuma dokokinSa.

Daga wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: idan muna tattaunawa da wadanda ba musulmi ba kar mu yi amfani da kalmomin cin mutunci da kaskantar da su,mu yi amfani da hujoji da maganganu na hankali da nufin shiryarwa da kawo sulhu da canji kuma wannan hatta da sauran yan uwanmu musulmi haka ya kamata mu yi.

Na biyu: masanyar ra'ayi  da tattaunawa ta neman gyara a tsakanin da sauran ma'abuta addinai hatta mushrikai abu ne mai kyau da addinin musulunci ya umarce mu da shi.

Na uku: Imani da Allah da manzonninsa bai wadatar ba,dole sai mun mika wuya da umarninsu da kuma yi masu biyayya ta gaskiya.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 47 a cikin wannan sura ta ankabut:

 

وَكَذَلِكَ أَنزَلْنَا إِلَيْكَ الْكِتَابَ فَالَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يُؤْمِنُونَ بِهِ وَمِنْ هَؤُلاء مَن يُؤْمِنُ بِهِ وَمَا يَجْحَدُ بِآيَاتِنَا إِلاَّ الْكَافِرُونَ

 

47- Kamar haka kuwa Muka saukar maka da Alkur'ani.Hakika wadanda Muka bai wa littafi a gabaninka sun aba da gaskiya da mutan Makka akwai masu ba da gaskiya da shi, ba kuwa mai musun ayoyinmu sai kafirai.

Kamar yadda Allah madaukakin sarki ya sabkar da littafin attaura da injila da Annabi Musa da Annabi Isa (AS) haka ya sabkar da littafin alkur'ani mai girma ga Annabin Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka har ila yau Allah ya sabkar da littafai ga sauran annabawa da manzonni dukansu maganar Allah ce. Don haka babu wani sabani ko karo da juna  saboda tushensu guda ne Shi ne Allah kuma umarni guda ne ,kamar yadda dukan musulmi suka yi imani da sauran littafai da aka sabkarwa Annabawa da manzonni (AS) haka musulmi suma shokin sauran mabiya addinai sun yi imani da littafinmu Alkur'ani mai girma da girmama Shi dalili koyarwar Kur'ani tushe da mahanga day ace da ta sauran littafen annabawa da manzonnin da suka gabata.

Ci gaban ayar na cewa: ba wai kawai ma'abuta littafi ba hatta daga  cikin Mushrikai da masu bautar gumaka da ke neman sanin gaskiya zai yi imani da Kur'ani da addinin musulunci amma shi kafiri mai tsananin jayayya  da kin karbar gaskiya bayan ya fahimta ba a shirye yak e ba ya yi imani da karbar gaskiyar da ke a fili karara .Kuma ya sani yin hakan ba zai cutar da kur'ani da komi ba tabbas domin yayi daidai misali n mutum da ya sanya labule babba mai duhu a gaban tagar gidansa ya hana hasken rana ya shigo gidansa da dakinsa .wannan aiki nasa ba zai cutar da girman rana da haskenta ba sai dai ya haramtawa kansa samin hasken rana da zai amfane shi a karan kansa.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu;

Na farko:Kur'ani yana kira da umurtarmu da girmama sauran littafai da aka aikowa sauran annabawa da manzonnin da suka gabata (AS)

Na biyu: Mutum a kullum ya kasance mai kishi da girmama addininsa da sauran addini kuma ta haka shi ma sai a girmama nashi addinin.

*****************************

To madallah daga karshe za mu saurari karatun ayoyi na 48 da 49 a cikin suratul Ankabut:

 

وَمَا كُنتَ تَتْلُو مِن قَبْلِهِ مِن كِتَابٍ وَلا تَخُطُّهُ بِيَمِينِكَ إِذًا لّارْتَابَ الْمُبْطِلُونَ

 

48- Ba ka zamanto kuma kana karanta wani littafi kafin sa ba wato Alkur'ani, baka kuma rubuta shi da hannunka da kuwa haka ya faru to sai mabarnata su yi kokwanto.

 

بَلْ هُوَ آيَاتٌ بَيِّنَاتٌ فِي صُدُورِ الَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ وَمَا يَجْحَدُ بِآيَاتِنَا إِلاَّ الظَّالِمُونَ

 

49- A'a ,shi dai Alkur'ani ayoyi ne mabayyana da suke cikin zukatan wadanda aka bai wa ilimi. Ba kuwa mai yin musun ayoyinmu sai azzalumai.

Wannan aya ta 48 kamar sauran ayoyin kur'ani ta bayyana a fili karara babu kwankwato ciki kur'ani gaskiya ne daga Allah yake kamar sauran littafan da Allah ya aiko annaba da su da cewa: annabin Rahama wanda ya zo mana da wannan addini na musulunci da littafin kur'ani kafin a sabkar asa da wannan littafi  bai yi karatu a gurin wani malami ko zuwa makaranta da yin karance-karance babu wani littafi ko da daya da ya karanta ko yayi rubutu,kuma wadanda ke kokarin karyata abin da ya zo da shi sun san da haka da sanya shaku cikin zukatansu da cewa wannan littafi na kur'ani ya kumshi abubuwan da sauran littafai suka zo da sun a amma karya yake yin a cewa Shi manzo ne daga Allah. Amma Shi mutum ne da bai yi karatu ko rubutu ba a gurin wani amma kuma ya zo da littafi mai girma da kololuwa ta ilimi da sani da babu wani balarabe  a zamaninsa da ya zo da wani lamari irin naSa kuma littafin kur'ani ya kumshi dalilai na mu'ujiza .Ci gaban ayar na cewa; duk wani dalili na hankali da ilimi sun gamshi da fahimta a cikin alkur'ani amma suka ki yin imani da shi saboda tsananin kiyayya da kafirci.

Daga cikin wadannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko: Karkashin hikima da iradar allah sai ka samu mutane da bas u yi dogon karatu ba sun shiryu da samin tsira da dacewa da rayuwa a wannan duniya da ma lahira,wani lokaci kuwa ga mutum da dogon karatu da ilimi mai zurfi amma ya tabe duniya da lahira don haka mu nemi shiriya da taimakon Allah ya haskaka mana rayuwa duniya da lahira.

Na biyu: Dole mu kasance masu takatsantsa kar mu fada tarkon makiya  da amfani da  hanayar da ba ta dace ba.

Na uku:Wadanda suka kasance ma'abuta ilimi  da masani ta hakika  suna fahimta da amincewa da alkur'ani.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..