Apr 19, 2017 12:19 UTC

Suratul Ankabut, 50-55 (726)

Bismillahi rahamani Rahim.

Jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

**********************************

To madallah masu saurare za mu fara shirin na yau da sauraren aya ta 50 da 51 a cikin nsuratul Ankabut:

 

وَقَالُوا لَوْلا أُنزِلَ عَلَيْهِ آيَاتٌ مِّن رَّبِّهِ قُلْ إِنَّمَا الآيَاتُ عِندَ اللَّهِ وَإِنَّمَا أَنَا نَذِيرٌ مُّبِينٌ

 

50- Suka kuma ce: me ya hana a saukar masa da wasu ayoyi daga Ubangijin nasa? Kace da su: Hakika ayoyi dai suna wurin Allah ne ,ni kuwa ba kowa ba ne face mai mabayyanin gargadi.

 

أَوَلَمْ يَكْفِهِمْ أَنَّا أَنزَلْنَا عَلَيْكَ الْكِتَابَ يُتْلَى عَلَيْهِمْ إِنَّ فِي ذَلِكَ لَرَحْمَةً وَذِكْرَى لِقَوْمٍ يُؤْمِنُونَ

 

51- Yanzu bai ishe su ba cewa: Mun saukar maka da Littafi da ake karanta  musu shi? Ba shakka a game da wannan lallai akwai rahama da kuma gargadi ga mutanen da suke ba da gaskiya.

A cikin shirin da ya gabata a makon jiya mun fara da bayani kan alamomin mu'ujizar Kur'ani mai girma da gaskiyar sakon da aka turo manzon Rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa da shi .To wadannan ayoyina cewa: duk da wadannan mu'ujiza da Manzon rahamha (SWA) da kur'ani suka zo da su amma kafirai ta hanyar fakewa da karya da jayayya sai suka ce me ya Muhammadu bai zo da mu'ujizaozi daidai da mu'ujizozin Musa Da isa ba ?.Me ya sa bay a zo mana da abin da mu muka bukata ba? Me ya sa bai zo mana da ruwa na gudana a tsakiyar sahara ba?. Me ya sa bai zo mana da wata wasika rubutacciya da wajen Allah ba?

To amsa a gaskiya sub a mutane ne masu neman gaskiya da karbare gaskiya domin yin imani da it aba kamar yadda da dama daga cikin al'ummomin da suka gabata duk da sun ga mu'ujizozin annabi Musa da Annabi Isa (AS)  da na sauran annabawa da manzonnin da suka gabata (AS) amma suka ki yin imani da su.

Allah Madaukakin sarki ya sabkawa da annabin rahama (SWA) da Alkur'ani a matsayin Mu'ujiza kuma Mushrikai da Kafirai sun yi iyakacin kokarinsu na musantawa da karyatawa amma sun kasa hatta su kawo daidai da sura guda irin na surorinAlkur'ani sun kasa amma sun ki yin imani to me suke so kuma da ya wuce wannan mu'ujiza ta Kur'ani. Babban nauyin da ya rataya kan Manzonni shi ne shiryar da mutane da fadakar da su ta hanyoyin kashedi da bushara da suka yi daidai da hankali da tunani da fidirar mutum. Ba abin da ya saba da hankali kamar sihiri da bokanci ko saddabaru da yayi daidai da was an yara a taru a sha kallo a waste.Kafirai da masu jayayya na bukatar mu'ujiza ta zahirin rayuwa mai saukin rushewa da rashin tasiri na hakika.Alhali shi Kur'ani mu;ujizarsa ta ma'anawiya dawamammiya da ke tafiya kafada da kafada da addinin musulunci. Wannan  littafi da ya kai kololuwar ilimi ya zo mana ne ta hanayr mutuman da bai yi karatu a wajen wani ba amma da lutifin allah ya koyar da kowa da zama malamin kowane mahaluki a tsawon tarihu har zuwa tashin kiyama wannan ita wata babbar mu'ujiza ce ko ka so ko ka ki.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:Mu;ujizar annabin karshen zamani it ace bayani da sako rubutacce da babu wani zai iya kawo irinsa har duniya ta tashi.

Na biyu: Kur'ani littafi ne kamilalle gamshasshe d ake biyan bukatar mutum ta ma'anawiya da amsa duk wata bukata ta mutum a tsawon tarihi.

Na uku:Kur'ani na hana mutuim daga fadawa bata da sha'afa  kuma yay i mana iso ga rahama da lutifin Allah maras karewa.

Yanzu kuma za mu saurari karatun ayoyi na 52 da 53 a cikin wannan sura ta Ankabut:

 

قُلْ كَفَى بِاللَّهِ بَيْنِي وَبَيْنَكُمْ شَهِيدًا يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَالَّذِينَ آمَنُوا بِالْبَاطِلِ وَكَفَرُوا بِاللَّهِ أُوْلَئِكَ هُمُ الْخَاسِرُونَ

 

52- Kace da su Allah Ya isa shaida tsakanina da ku, Ya san abin da yake cikin sammai da kassai. Wadanda kuwa suka ba da gaskiya da barna suka kuma kafirce wa Allah,wadannan su ne tababbu.

 

وَيَسْتَعْجِلُونَكَ بِالْعَذَابِ وَلَوْلا أَجَلٌ مُّسَمًّى لَجَاءَهُمُ الْعَذَابُ وَلَيَأْتِيَنَّهُم بَغْتَةً وَهُمْ لا يَشْعُرُونَ

 

53- Suna kuma neman ka da gaggauto musu da azaba ,ba don kuwa akwai lokaci na musamman da aka tanada ba, da lallai azabar ta zo musu. Kuma lallai za ta zo musu ne ba zato ba tsammani,alhali bas a iya sanin lokacin.

Wadannan ayoyi na shaidawa manzon Rahama (SWA) cewa: idan Kafirai na karyata sakon shiriya da ka zo da shi kar ka yi sako-sako da wannan sako  saboda Allah wanda ya aiko ka da wannan sako yana ganin irin kokarin da ka key i na shiriyar da su kuma Allah yana taimaka maka kan hakan   kuma yana tare da kai kuma Ka shaidawa Kafirai cewa: idan Ni karya nake yin i ba manzon allah ba ne kuma duk abin da na ke fada rayawa ne kawai nake yi. Allah mai gani ne kuma masani ne kan komi haka duk aiki da nake aikatawa yana gani da masaniya to zai azabtar da ni . Ci gaban ayar na cewa; Kafiraio masu bakar jayayya sai suka ce: idan gaskiya ka ke fad aka sa Allah ya sabkar mana da azaba ,Shin sun manta Allah a wannan duniya yana bawa mutane wata dama  da lokaci kayyadadde na su zabi hanyar shiriya ko bata kafin ya sabkar masu da azaba kuma wannan wani lutifi ne na Allah na ba mu wannan zabi.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:Wani lokaci takaicin jayayyar kafirai da bakar adawarsu kan addini da yin imani da sakon shiriya na cusa rauni a zukatan ma'abuta imani to amma da ke Allah na gani kana bin da ke faruwa kuma makomar kafirai ta munana.

Na biyu:allah ya gaskatawa da jinjiwa Manzonsa kan kokarin da yake yi da kuma isar da sakonsa daidai babu kasawa.

Na uku:Ita azabar Allah ta na zuwa ne daidai da lokaci kayyadadde babu jinkiri ko gaggawa cikin lamarin kuma karkashin kudura da iradar allah ba bukatar mu ba mu mutane.

*********************************

To madallah daga karshe masu saurare za mu saurari karatun ayoyi na 54 da 55 a cikin wannan sura ta ankabut:

 

يَسْتَعْجِلُونَكَ بِالْعَذَابِ وَإِنَّ جَهَنَّمَ لَمُحِيطَةٌ بِالْكَافِرِينَ

 

54- Suna kuma neman ka da gaggauto musu da azaba alhali kuwa jahannama lallai mai kewaye kafurai ce.

 

يَوْمَ يَغْشَاهُمُ الْعَذَابُ مِن فَوْقِهِمْ وَمِن تَحْتِ أَرْجُلِهِمْ وَيَقُولُ ذُوقُوا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ

 

55- A ranar da azaba za ta lullube su ta samansu da ta karkashin kafafuwansu,kuma Allah Ya ce da su: Ku dandani abin da kuka kasance kuna aikatawa.

Wadannan ayoyi kamar ayoyin da suka gab ace su ne kan bukatar rashin hankali da tunani na Kafirai da ke bukatar a gaggauta sabkar masu da azaba inda wadannan ayoyi ke cewa; Me ya sa suke gaggayua babu wani dalili ? alhali hatta a wannan hali da suke ciki,suna rayuwa ne cikin jahannama ba tare da sun la'ankarta ba.Jahannamar zalunci da rashin adalci,jahannamar yaki da zubar da jinni,jahannamar rashin tsaro da kwanciyar hankali da nucuwa ,jahannamar fargaba da tashin hankali  da rashin tabbas da dai sauransu.

Su suna zaton azaba  kawai Dufana  da ambaliyar ruwa da girgizar kasa ne. Ku sani mummunan ayyukan da kuke aikatawa sune sakamakon kumci da matsalolin rayuwa  da tsanani da kuke fuskanta a daidaiku da kuma rayuwar jama'a wannan ma wani nau'I ne na azaba a wannan duniya da sakamakon na ayyukan da muke aikatawa. Kafin kafirai su je lahira su tarda mummunan azaba da aka yi masu tanadi kuma babub wata hanya ta kubuta daga cikinta ko a sausauta masu.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:Allah ya jinkirta azabatar da hallakar da kafirai domin bas u damar yin tuba amma kash bas u amfanuwa da wannan damar.

Na biyu:duk wani aiki yana fuska biyu badini da zahiri kuma a gobe kiyama ne zahirinsa zai bayyana ko mai kyau ku mummuna.

 

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..