Apr 19, 2017 12:38 UTC

Suratul Ankabut, 56-61 (727)

Bismillahi rahamani Rahim ,jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

*******************MUSIC****************

To madallah yanzu kuma za mu fara shirin na yau ne da sauraren karatun ayoyi na 56 da 57 a cikin wannan sura ta Ankabut:

 

يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ أَرْضِي وَاسِعَةٌ فَإِيَّايَ فَاعْبُدُونِ

 

56- Ya ku bayina wadanda suka ba da gaskiya hakika kasata yalwatacciya ce ,Ni kadai za ku bauta wa.

 

كُلُّ نَفْسٍ ذَائِقَةُ الْمَوْتِ ثُمَّ إِلَيْنَا تُرْجَعُونَ

 

57- Kowanne rai zai dandani mutuwa ,sannan wurinmu za a komar da ku.

Daya daga cikin umarni na hikima da da jan hankali a musulunci shin ne yin gudun hijira domin kare imani da mutunci tun farkon bayyanar musulunci da musulmi suka fuskanci takurawa da tsanani daga mushrikan Makka kuma hakan yana hana musulmi gudanar da rayuwa da harkokinsu na addini cikin walwala ba matsi da takurawa.Saboda haka manzon rahama tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayn gidansa tsarkaka da kuma mumunai na hakika na farkon musulunci suka yi hijira daga makka zuwa Madina da tarewa a wannan birni na imani.Wannan ayar wata doka ce ta bai daya da ke cewa;kar mutum ya sarfa da wani gari ko wani yanki matukar ba zai iya aiwatar da addininsa a wannan gari ko wannan yanki to ya bar shi ya tafi inda yafi shi gurin da zai samu yancin addini na rayuwa mai tsafta ta gari. Kar mutum ya sarkafa da wani gari ko yanki da ci gaba da rayuwa cikin takurawa da tsanani a kullum ya kasance ya sa a kansa da tunaninsa ita kanta wannan duniya rayuwa a cikinta mai karewa ce. Kar ya zamanto burinsa a wannan duniya tara dukiya  da kare dukiyar ko wani mikami da yake da shin a zahiri mai karewa.Idan mutum  ya kasance mai tunani da wannan nasiha da imanin lahira it ace madawwama  to har abada ba za sarkafa da wannan duniya fiye da yadda ya dace kuma zai aikata abubuwan da suka dace ne.

Daga cikin wannan aya za mu ilmantu da abubwa da guda hudu kamar haka:

Na farko: wajen zabar gurin da za mu rayuwa a kullum mu rika la'akari da imaninmu da kuma mutuncinmu kar mu yi wasa da wannan lamari.

Na biyu: Hijira domin kare addini  na daya daga cikin nauyin da ya rataya kan ma'abuta imani.

Na uku:Wadanda ke aikata saboda ayyukan da bas u dace ba saboda sarkafa da wani gari ko yanki to ba su da wani uziri a ranar kiyama.

Na hudu: mutuwa za ta riski kowa kuma tana zuwa ne ba tare da yin shawara ba sai dai haka kwacam don haka mu yi tanadin abin da zai amfane mu bayan mutuwa.

Yanzu kuma za mu saurari karatun aya ta 58 da 59  kamar haka:

 

وَالَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَنُبَوِّئَنَّهُم مِّنَ الْجَنَّةِ غُرَفًا تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَارُ خَالِدِينَ فِيهَا نِعْمَ أَجْرُ الْعَامِلِينَ

 

58- Wadanda kuma suka ba da gaskiya suka yi aiki nagari ,lallai za Mu zaunar da su cikin manya-manya gidaje a Aljanna wadanda koramu za su rika gudana ta karkashinsu suna madawwama a cikinsu. Madalla da ladan masu kyakkyawan aiki.

 

الَّذِينَ صَبَرُوا وَعَلَى رَبِّهِمْ يَتَوَكَّلُونَ

 

59- Su ne wadanda suka yi hakuri kuma ga Ubangijinsu kawai suka dogara.

A cikin wadannan ayoyi Allah madaukakin sarki yayi wa wadanda suka yi gudun hijira  da hakuri da duk wani tsanani da takurawa da kunci da barin garinsu na aifuwa  domin kare imaninsu  alkawali da gidan aljanna da ruwa ke gudana a karkashinsu da kuma ni'imomi iri-iri maras karewa. Wadannan ayoyi na nuni da wasu abubuwa na musamman guda uku da ma'abuta imani suka kebantu da su kamar haka:aiki,hakuri da kuma tawakkali.

Abin lura a nan da kuma tunatarwa shi ne duk wani imani ba ya tare da aiki tsabtacecce bas hi da wani amfani da karho. Shi kuma aiki da bay a tare da hakuri ba zai kai ga nasara bah aka shi ma hakurin da bay a tare da tawakkali da Allah  bay a dawwama da ci gaba tabbas.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa guda uku kamar haka:

Na farko:Sharadin samin shiga aljanna da samin ni'imomin aljanni akwai imani da aiki na gari.

Na biyu:Abubuwan da muminai suka rasa a wannan duniya a dalilin kare imaninsu za su same shi ne a gobe kiyama da Allah yayi masu tanadi.

Na uku:Hakuri da juriya su ne mabudin nasara da ciyo kan dukan matsaloli da isa da daukaka a dukan bangarori na rayuwa. A fili yake ma'abuta imani a kullum suna fuskantar tsangwama da takurawa da cin fuska da mutunci daga makiya amma a kullum suke hakuri da neman taimakon Allah.

*******************************

To madallah kuma yanzu  za mu saurari karatun aya ta 60 kamar haka:

 

وَكَأَيِّن مِن دَابَّةٍ لا تَحْمِلُ رِزْقَهَا اللَّهُ يَرْزُقُهَا وَإِيَّاكُمْ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ

 

60- Da yawa kuma daga dabbobi bas a dauke da arzikinsu, Allah ne yake arzuta su tare da ku. Allah kuwa Shi ne Mai ji Masani.

Wannan ayar ci gaban ayar da ta gabace ta ne da ke Magana kan yin hijirar ma'abuta imani domin kare imaninsu da bautawa Allah ba tsangwama da cewa; abubuwan da kuka rasa a kasar kafirai da suka takura maku ,kun yi asarar ayyukanku da dukiyoyinku  da sauran abubuwa na rayuwa da kunci da matsaloli kar ku damu da su  ,idan ya kama ku yi hijira ku yi kuma ku sani Allah madaukakin sarki mai arzitawa da isar da arziki da wadata ga kowa ,Shi ne dai Allan da ke bawa kowa arzikinsa a cikin sammai da kassai ba tare da wata matsala ba kuma ba zai manta da ku ba ,Kuma hatta dabbar da ba ta da karfi da iko samin abinci a tsakiyar sahara yana isar mata da abincinta da yi mata tanadinsa a kullum  kuma babu wata rana da za ta rasa wannan abinci da kwana da yunwa.To shi ma mutum mai karfi da iya nemawa kansa abinci da yin iyakacin kokarinsa abinci da arzikinsa yana hannun Allah ne kuma Shi ke ciyar da shi a kullum rana ta Allah. Idan jurewa barin garinku da yankinku da rasa ayyukanku saboda yin hijira don Allah  to tabbas za ku samu alheri da arziki daga Allah tamkar ba ku taba yin asara ba a baya.Amma idan  mutum ya gwammacewa za ma a gari da yankin kafirai  da masu shirka  da mika wuya ga zalunci da danniya da dagutu to ba zai iya gyara gab aba lamari ne mai wuya kuma zai iya asarar komi wato dukiya da kuma imaninsa  da ruhin addini domin shi kafirci da shirka da zalunci na fitar da mutum daga kasancewarsa ta mutum  da mutuntuka.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:Masu hijira don neman yardarm Allah da kuma kan hanyar Allah bai kamata bas u ji tsoran asarar abin da za su yi asara na dukiya ko hakan ya hana su yin gudun hijirar.

Na biyu:mutum mumini a kullun na tafiyar da lamuransa ne kan tawakkali da Allah ba tare da tsoron arzikinsa ya yanke ba ko kasa a guiwa wajen zartar da nauyin da ya rataya kansa.

Na uku:Allah wanda ya halicce mu  shi ne mai arzita mu a kullum har gobe.

Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 61 a cikin wannan sura ta Ankabut:

 

وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّنْ خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضَ وَسَخَّرَ الشَّمْسَ وَالْقَمَرَ لَيَقُولُنَّ اللَّهُ فَأَنَّى يُؤْفَكُونَ

 

61- Wallahi da zaka tambaye su: Wane ne ya halicci sammai da kassai,ya kuma hore rana da wata? To lallai za su ce: Allah ne .To ta yaya aka karkatar da su daga kadaita Shi?.

Mushrikan da ke rayuwa a birnin makka da ke bautawa gumaka sun yi imani da Allah ne ya halicce ce amma tafiyar da lamuran rayuwarsu ya mikawa rana da wata da su ma ta hanyar gumakan da suke bautawa ke zartarwa.Abin mamaki sun amince da imanin Allah ne ya halicce su amma bas u amince da shi ne zartarwa da ganinsa a matsayin rabbi kuma a bin da suke nufi a nan a wautarsu arziki da talauci ba ya karkashin kulawar Allah babu hannun Allah a cikin wannan lamari. Wani abin mamaki a wannan zamani da muke rayuwa akwai wasu mutane da ke da irin wannan tunani na amincewa da Allah a matsayin wanda ya halicce su amma bas u bas hi hakkinsa yadda ya kamata da dogaro da Shi a matsayin mai arzitawa da yin dokokin da za a bi a samu rayuwa mai inganci duniya da lahira  kuma bas u bin dokokinsa da umarninsa. Irin wannan gungu na mutane sun yi imanin mutum shi ne  ke da hakkin tafiyar da rayuwarsa ba tare da yayi dogaro da Allah  ko bukatar ya taimaka masa ba kuma suna zartar da abin da suka ga dama karkashin son ransu.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:a a lamari na tattaunawa da kafirai ko mushrikai mu fara da abubuwan Iitikadi da muka yi daidaito da su kamar yadda mushrikan Makka da musulmi baki dayansu sun amince da Allah ne Mahalicci.

Na biyu:Kaucewa hanyar gaskiya madaidaiciya na daya daga cikin abubuwa masu hadari da yi wa rayuwa barazana kuma amincewa da Allah Shi ne Mahalicci amma kuma a ki amincewa da Shi ne mai tafiyar da lamura wani bangare ne babba na kaucewa hanya da tabewa.

 

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..