Apr 19, 2017 13:10 UTC

Suratul Ankabut, 62-66 (728)

Bismillahi rahamani Rahim.

Jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke farawa da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin na yau da yardar Allah madaukakin sarki.

**********************************

To Madallah masu saurare a yau za mu fara shirin namu tare da sauraren karatun aya ta 62 a cikin suratul ankabut:

 

اللَّهُ يَبْسُطُ الرِّزْقَ لِمَن يَشَاء مِنْ عِبَادِهِ وَيَقْدِرُ لَهُ إِنَّ اللَّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ

 

62- Allah Yana shimfida arziki ga wanda Ya so daga bayinsa, ya kuma kuntata masa. Hakika Allah Masanin komai ne.

A cikin shirin da ya gabata mun yi nuni da cewa musulmin farko muminai na hakika a farkon bayyanar addinin musulunci a birnin Makka sun fuskanci tsananin takurawa da matsaloli barkatai iri-iri daga mushrikai kuma sun shafe shekaru kan takunkumin karya tattalin arziki da hana saye da sayarwa kansu. A cikin wannan mummunan hali ne wasu daga cikinsu ba a shirye suke bas u yi gudun hijira zuwa madina sun zabi zama a gidajensu a wannan gari nasu. Don haka wannan aya ke cewa; Duk tsanani da kumci da matsaloli na rayuwa kun ci gaba da riko da imani da addinin Allah kuma babu wani abu da ya canja kan imaninku sai ma abin da ya ci gaba to amma yana da kyau ku sani Allah ne mai arzitawa kuma arzikin kowa da komi yana hannunsa.Idan ya kama kowa baki daya yayi hijira  to lazumi ne ku bar gidajenku da wannan gari na ku domin yin hijira zuwa Madina.

To daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:kokari da tashi fadin neman abin sanyawa  gab akin salati wani nauyi ne da ya rataya kanmu amma kuma shi arziki na allah ne ba zabinmu ba  m,Allah ne ke rabawa bayunsa cikin hikimarsa.

Na biyu: Mutane mun bambanta a junanmu a fuskoki da daman a arziki da kokari da himma da ni'imomin wannan duniya  kamar yadda muka bambanta a tunani da hankali amma kuma mun hadu a cikin abubuwa da daman a zamantakewa.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun ayoyi na 63 da 64 a cikin suratul Ankabut:

 

وَلَئِن سَأَلْتَهُم مَّن نَّزَّلَ مِنَ السَّمَاء مَاء فَأَحْيَا بِهِ الأَرْضَ مِن بَعْدِ مَوْتِهَا لَيَقُولُنَّ اللَّهُ قُلِ الْحَمْدُ لِلَّهِ بَلْ أَكْثَرُهُمْ لا يَعْقِلُونَ

 

63- Wallahi da za ka tambaye su Wane ne ya saukar da ruwa daga sama,sannan ya raya kasa da shi bayan mutuwarta? Ba shakka za su ce: Allah ne. Kace da su: Alhmadu lillahi,a'a yawancinsu dai bas a hankalta.

 

وَمَا هَذِهِ الْحَيَاةُ الدُّنْيَا إِلاَّ لَهْوٌ وَلَعِبٌ وَإِنَّ الدَّارَ الآخِرَةَ لَهِيَ الْحَيَوَانُ لَوْ كَانُوا يَعْلَمُونَ

 

64- Kuma wannan rayuwar duniyar ba komai b ace face nishadi da wasa,kuma hakika rayuwar gidan lahira it ace rayuwa in da sun kasance sun sani.

Abu ne ko lamari a fili da kowa yayi imani da shi ba shakka cewa:rayuwa da arziki na mutum da sabkar da ruwa daga sama suna hannun Allah  kuma idan wani yanki ko wata kasa  ta yi shekaru ko wani lokaci mai tsawo ba tare da sabkar ruwan sama ba za a yi fari da duk wasu tsirre su mutu haka dabbobi ma sun rasa ruwan sha da tsiyawar da za su ci  su ma mutane su fuskanci yunwa da karamcin abinci .Kan haka wadannan ayoyi ke cewa: Hatta su kansu Mushrikai nada imanin sabkar da ruwa yana hannu da ikon Allah ne amma a maimakon Allah sais u rungumi gumaka a matsayin masu tasiri a rayuwarsu amma bin mamaki yaya za'a yi mutum ma'abucin imani za su rika nuna tsoro da fargaba a lamari da ya shafi arziki ko tsoran yin hijira kan hanyar Allah.

Shin bas u sani ba ne ita kanta rayuwa da arziki na hakika an yi tanadinsa ne a Lahira kuma wannan duniya duk yawan arziki da mukami da jin dadin da ke cikinta tamkar wani wasa da a taba a tashi a waste. Kamar yadda yaro karami ke wasa da kayan wasansa irin na yara iri-iri da nuna jin dadinsa ta wannan hanyar. Su kuma manya da wasu abubuwa wadanda suka fi haka kamar Mota  da gida da kamfanoni, Haka lamarin yake idan ka lura wani an yi shi sarki,wani waziri,wani kuwa dokta a gefensa wani maras lafiya,wata an yi ta uwa da kuma danta a tare da ita haka lamarin rayuwar duniya yake tafiya har zuwa lokacin da wannan rayuwa za ta zo karshe da tashin kiyama ,Wani ya rayu rayuwa mai tsafta da inganci da kowa ke girmama shi a wannan rayuwa tun daga yarinta,da samartaka da girmansa da kuma tsufansa har zuwa ranar da zai mutu domin kwanakin da Allah ya yanke masa ya kawo karshe. A gobe kiyama kowa zai fahimci gaskiya da babu kwankwanto cikinta ranar da kowa zai yi rayuwarsa ta hakika ,a wannan rana ina sarakuna masu rayawa da nuna dagawa a tsawon tahiri? Ina komandan komandodi Azzalumi da nuna karfinsa a yake-yake a tsawon tarihi? To a wannan rana kowa daya yake babu wani bambanci da fifiko zai wanda yayi aikin kware a wannan duniya karkashin umarni da neman yardarm Allah da manzonsa da limaman gidan tsarki kuma wanda ya saba hakan ya tabe duniya da lahira tabbas.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa hudu kamar haka:

Na farko: Sani da fahimtar akwai allah mahalicci lamari ne da kowa ya amince da shi sai wanda zunufi  da kaucewa hanya ya lullube basirasa da fadawa tarkon shaidan da bata.

Na biyu:Yawancin mutane sun shagaltar da kawunasu da gangan ba a shirye suke bas u koma kan hanya madaidaiciya.

Na uku:Shagala da lahira  da kin karbar gaskiya ya kai mutum ga rungumar duniya ido rufe da rayuwa ta zahiri.

Na hudu: Rayuwa ta gaskiya a lahira take gurin da kowa zai sami matsayinsa na hakika da yayi daidai da shi da ayyukan da ya aikata ba tare d an tauyewa kowa hakinsa ba.

****************************************

To madallah daga karshe kuma za mu saurari

 

فَإِذَا رَكِبُوا فِي الْفُلْكِ دَعَوُا اللَّهَ مُخْلِصِينَ لَهُ الدِّينَ فَلَمَّا نَجَّاهُمْ إِلَى الْبَرِّ إِذَا هُمْ يُشْرِكُونَ

 

65- Sannan idan suka hau jiragen ruwa sukan roki Allah suna masu tsarkake addini a gare Shi,to lokacin da Ya tserar da su zuwa gaci sai gas u suna yin shirka.

 

لِيَكْفُرُوا بِمَا آتَيْنَاهُمْ وَلِيَتَمَتَّعُوا فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ

 

66- Don sun kafirce wa abin da Muka bas u,kuma don su ji dadi.To da sannu za su sani.

Wadannan ayoyin ci gaban ayoyin da suka bata ne da key i wa mutum bayani na fadakar da shi sanin Allah wanda ya halicce shi  da nuna masa hanyoyi madaidaita  ta hanyar nuna masa alamomi na kudura da iradar Allah a sammai da kassai inda ayoyin suka tunatar da shi cewa:lokacin da ya fuskanci hadari kuma babu wani ko wasu da za su taimaka masa da fidda tsammahani  da wa yake komawa da yin dogoro ne ? A lokacin da jirgin ruwa yake kokarin nutsewa da shi  wa yake neman ya taimaka masa ne ? a daidai lokacin da jirgin sama ke kokarin fadowa da su da samin matsala a sararin samaniya  a gurin wa yake neman taimako ne? To ba gurin Kowa ne zai nemi taimako sai a gurin Allah mahalici mai kudura da iradar da zai iya cetonmu a duk wani hali da yanayi da muka samu kanmu a ciki kuma ya tsiratar da mu daga mutuwar da babu makawa.. Mutum a rayuwa ta yau da kullum yana dogaro ne kan abubuwa masu rauni  da na zahiri kamar aboki ya taimaka masa da magance masa matsalarsa da mantawa da neman taimako a gurin Allah amma lokacin da ya fuskanci babban hadari sai kuma ya koma gurin Allah ya taimaka masa da mantawa da sauran da a baya yake neman taimakonsu.Amma abin mamaki ga  mutum da zarar Allah ya kubutar da shi  sai ya manta da daya Allah ne ya taimaka masa da kubutar da shi sai ya koma rayuwarsa irin ta baya da jin dadin rayuwar duniya zalla ba tare da ya tuna da Allah da jin tsoransa ko ranar kiyama na zuwa. Hatta ya godewa Allah da ya halitta masa da wadatar da shi da wadannan ni'imomi ba yayi kaiconsa.

Daga cikin wadannan ayoyi za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farko:guguwar shagalta na batar da mutum da fidirarsa amma manyan hadura da fuskantar bala'I babba na maido shi ga hanya madaidaiciya da komawa ga Allah Mahalicci.

Na biyu:Addu'a ta gaskiya da ikhlasi karbabbiya ce a kullum ko da kuwa kafiri ne mutum Allah zai karba masa.

Na uku:Yin shirka ga Allah wani nau'I ne na kafirci da rashin godewa Allah da kaucewa hanyar tauhidi.

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags