Apr 19, 2017 13:23 UTC

Suratul Ankabut, 67-69 (729)

Bismillahi rahamani Rahim.

Jama'a masu sauraren barkarmu da warhaka da kuma sake saduwa da ku a cikin wannan shiri na hannunka mai sanda da a cikinsa muke faraway da sauraren karatun ayoyin kur'ani mai girma kana daga bisani mu kawo fassara da irin nasihohin da ke cikinsu,da fatar Allah y aba mu karfin guiwar aiki da su da samin tsira dunuya da lahira amin summa amin.Kuma a yau ma kamar yadda kuka saba ji ni ne Tidjani malam Lawali Damagaram zan kasance tare da ku daga farko har zuwa karshen shirin nay au da yardar Allah madaukakin sarki.

***********************************

To madallah masu saurare za mu fara shirin nay au ne da sauraren aya ta 67 a cikin ayoyin karshe'karshe a cikin wannan sura ta ankabut.

 

أَوَلَمْ يَرَوْا أَنَّا جَعَلْنَا حَرَمًا آمِنًا وَيُتَخَطَّفُ النَّاسُ مِنْ حَوْلِهِمْ أَفَبِالْبَاطِلِ يُؤْمِنُونَ وَبِنِعْمَةِ اللَّهِ يَكْفُرُونَ

 

67- Yanzu ba su ga cewa Mu Muka sanya musu Harami amintacce ba,alhali kuwa ana ta fauce mutane a kewayensa? Shin yanzu sa rika ba da gaskiya da bata su kuma rika kafirce wa ni'imar Allah?.

A lokacin da laraba ke cikin jahilci da yake-yake a tsakanin kabilu ,wasu an kasha su wasu kuma an kama su  da cin su a yaki da maida su bayu.Sai Allah madaukakin sarki y aba wa birnin Makka aminci da tsaro da kowa ke girmama wannan gari kuma babu wani da ke da jarumtar kai wa wannan gari hari. Babban lamari da ya faru da kowa ya shiga cikin hayyacinsa da taitayinsa shi ne abin da ya faru inda babbar runduna da jarumai karkashin jagorancin Abrahama a kan giwa babba suka nemi kai wa wannan birnin na Makka hari.Amma cikin ikon Allah da kudurarsa da muijizarsa ya aiko da wasu tsintsaye daga sama suka kai wa maharan da ke cikin rundunara Abrahama hari da hallakar da su. Wannan ayar tana Magana ne kai tsaye da mushrikan Makka da cewa;duk da Allah yay i maku wannan ni'ima babba da baku aminci da rayuwa cikin aminci da tsaro to me ya sa kuke bautawa gumaka ne a maimakon ku yi imani da Allah abin bautawa da gaskiya shi kadai ba tare da abokin tarayya ba? Shin wannan aiki na ku ba kafircewa ni'imar Allah ba ne ?.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko:tsaro daya daga cikin manyan ni'imomin Allah ne kuma dole mu gode masa da wannan ni'ima da yayi mana da nisanta daga kafircewa ni'ima.

Na biyu:tunatarwa da mutane da ni'imomin Allah kansa kira ne zuwa ga kadaita Allah da bauta.

Yanzu kuma lokaci ne na sauraren karatun aya ta 68 a cikin wannan sura ta ankabut:

 

وَمَنْ أَظْلَمُ مِمَّنِ افْتَرَى عَلَى اللَّهِ كَذِبًا أَوْ كَذَّبَ بِالْحَقِّ لَمَّا جَاءَهُ أَلَيْسَ فِي جَهَنَّمَ مَثْوًى لِّلْكَافِرِينَ

 

68- Ba wanda ya fi zalunci kamar wanda ya kaga wa Allah karya ko kuma ya karyata gaskiya lokacin da ta zo masa.Yanzu ashe babu mazaunar kafurai cikin jahannama? ( Ba shakka akwai).

A bias al'ada ta dan adam  zalunci ya shafi tauyewa mutane hakkinsu a rayuwa ta zamantakewa kamar wani mutum ya cuci dan uwansa da tauye masa hakkinsa. Amma a al'adda da koyarwa ta addini bayan tauye wa wani hakkinsa zalunci ne haka kuma yi wa gumaka da wanin Allah ba Allah ba bauta wani nauyi ne babba na zalunci na danganta wani Allah da Allah a bauta saboda ya hada wani da Allah a bauta zalunci ne da tauye hakkin mahalicci. Haka ma wani ya karyata manzonnin Allah da annaba da kiran su da makaryata ko karyata sakon da suka zo da shi ya zalunci manzon ko annabin Allah saboda a maimakon godewa kokarin da yayi na nuna hanya ta samin tsira duniya da lahira ga mutane kuma a maimakon godewa wannan babbar ni'ima sai a kafirce masu da karya ta to wannan babban zalunci ne. Abu ne a fili karara idan zalunci kan dan uwanka mutum zalunci ne to ina ga zalunci kan mahalicci da manzonninsa an yi masa babban tanadi na azaba mai radadi a lahira.Sai dai wani hamzari ba gudu ba  ita shirka iri iri ce kuma  babban shirka bautawa gumaka da bautawa son rai wasu kuwa kudi suke bautawa da dai sauransu. To mumuni yayio hattara da lura kar ya fada tarkon shaidan na rungumar wasu abubuwa ba Allah a kullum ya kasance mai tsarkin zucciya da niya.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa biyu kamar haka:

Na farko: Babban zalunci mafi muni shi ne zalunci na al'adu na karyata maganar gaskiya a maimakon yin riko da gaskiya .

Na biyu:yin kari a cikin lamari da ya shafi addini da sanya son rai da kirkirawa Allah wani na abu kan karya to wannan babban zalunci ne.

****************************
Daga karshe za mu saurari karatun aya ta 69 a cikin wannan sura ta ankabut:

 

وَالَّذِينَ جَاهَدُوا فِينَا لَنَهْدِيَنَّهُمْ سُبُلَنَا وَإِنَّ اللَّهَ لَمَعَ الْمُحْسِنِينَ

 

69- Wadanda kuma suka yi jihadi saboda Mu Wallahi za Mu shiryar da su hanyoyinmu. Kuma hakika Allah Yana tare da masu kyautatawa.

Wannan aya da muka saurara it ace aya ta karshe daga cikin jerin ayoyin da ke cikin wannan sura ta ankabut kuma tana bayani ne kan jihadi da masu jihadin kan tafarkin Allah  kuma jihadin ya hada jihadi kan makiya allah da addinin allah da mazonsa  da kuma jihadi na kokarin fadada addinin Allah da kaukaka shi. A al'ada ta addinin musulunci shi jihadi ya hada jihadi kan makiya da ake kira da jihadi na zahiri sai kuma jihadi na boye na tsarkake zucciyarsa. Shi mutum mumuni dole yay i gwagwarmaya da makiya addinin Allah  kuma a shirye yake a kullum ya sadaukar da rai da rayuwarsa kan wannan tafarki haka lamarin yake a jihadi ya shafi tsarkake zucciya da niyarsa  daga ayyuka na haramun da suka sabawa shari'a yana gwagwarmaya da su da hana kansa bin son rai da zucciya. Abin da wannan ayar ke jinjinawa kansa shi ne jihadi kan tafarkin Allah  da neman yardarm Allah ko kan makiya addini ne da daukaka addini  amma burins aba samin matsayi da shuhura ba ko dukiya a wannan duniya ta hanyar yaki ba .Saboda hakaabin da yafi jihadi muhimmanci shi ne Ikhlasi da tsarkin zucciya da niya don Allah. Idan babu ikhlasi rasa rai a filinm dag aba shi da wani matsayi ko daraja face ma asara ce mutum yayi da tabewa. Idan jihadi  da duk wani kokari kan hanyar Allah .Kamar yadda Allah ke fada a cikin wannan ayar yayi masa alkawalin shiryar da shi da kuma alkawalin taimaka masa.Abu ne da kowa ya sani idan mutum yana son isa ga burinsa sai ya jurewa matsaloli masu yawa da jarrabawa iri iri da himma kana bin da ya sag a da kuma sanin abin da yake son cimmawa. Karkashin haka ne ma Allah yayi alkawalin taimaka mana wajen fahimtar wannan hana da kuma yin galaba kan matsalolin da za mu fuskanta.

Daga cikin wannan ayar za mu ilmantu da abubuwa uku kamar haka:

Na farlko:Allah yana taimakawa kowa  amma kuma mutane masu ikhlasi yana taimaka masu ne taimako na musamman da shiryar da su.

Na biyu: duk wani aiki da za mu yi mu sanya kyakkyawar niya  to Allah zai taimaka mana isa ga burinmu kuma yana tare da mu a kullum.

Na uku:idan mutum ya mika wuya tsakaninsa da Allah kan wani aiki da himma kan gaskiya to Allah ba zai daina taimaka masa har zuwa da cimma nasara da burinsa .

To Masu saurare da kuma wannan ne muka kawo karshen wannan shiri na yau sai mu kasance a mako mai zuwa da yardarm Allah inda za ku ji mu da wani sabon shirin amma kafin lokacin a madadin dukan wadanda suka taimaka a cikin shirin har ya kamala,Ni Tidjani malam Lawali Damagaram da na shirya kuma na gabatar na ke cewa: wassalam…..

 

Tags