Matakan kariya daga yaduwar cutar Zika
Mar 06, 2016 16:56 UTC
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta kaddamar dokar ta-baci domin dakile yaduwar Cutar Zika da ta fi yin illa ga jarirai wadanda ake haifuwa da karamin kai.
Zika dake haddasa haihuwar Jarirai da Nakasa na cigaba da Yaduwa a Latin Amurka da Yankunan Turai.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta yi gargadi ga kasashe kan kaucewa karbar gudunmuwar jinni daga mutanen da suka fito daga balaguro a kasashen da ke fama da cutar Zika.
A ci gaba da shirin yau ma muna tare da Dr Sabo Ahamed kwararen likita kana mai koyar da aikin likita a jami'ar Jos dake birnin Jos a taraya Najeriya
Tags