Karamin Sani Kukumi-Tsira Daga mumunar Rayuwa
Shirin dake gabatar da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Alkur'ani da kuma hadisan iyalan gidan Ma'aikin Allah tdarkaka
Masu saurare Assalama aleikum barka da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shiri na Karamin sani Kukumi shirin dake kowar da mu hakikanin rayuwar musulinci a cikin kur’ani mai kirma. Ba shakka ko wani dan adam a rayuwarsa yana bukatar rayuwa mai kyau, kamar yadda fitirar ko wani mahaluki ta ke kyamar mumunar rayuwa wacce take tattare da bacin rai gami da bakin ciki kuma yana ko wani dan adam iya kokarinsa wajen ganin ya kaucewa irin wannan rayuwa . To yaya ne za mu tsira daga irin wannan mumunan rayuwa? Hakika tunani mai kyau ya shiryar da mu cewa mahalicin Dan Adam wato Allah madaukakin sarki shine masanin hakikanin rayuwa mai kyau wacce ta dace ga Dan Adam ba a nan rayuwarmu ta Duniya kawai ba, har ma a rayuwar lahira wacce itace madawamiyar rayuwa, kazalika mahalacci mai tausayi wanda Ni’imarsa ta daukaka shine mai ikon tserar da bayinsa ga mumunar rayuwar wacce take tattare da bakin ciki gamida baci rai, ba anan duniya kawai ba har ma ga mumunar rayuwar lahira tare da Azabarta, da fatan Allah madaukakin sarki ya karemu daga mumunar rayuwar lahira baki daya.
Musuc***************************************************
A Alkur’ani mai kirma cikin suratu Nahl mai albarka Aya ta 97, Allah madaukakin sarki na cewa (( wanda ya yi kyakkyawan aiki Namiji ne ko Mace alhali yana mumuni, to lallai za mu raya shi cikin ingantacciyar rayuwa, kuma za Mu saka musu ladansu da mafi kayn abin da suka kasance suna aikatawa.))
A wannan Aya za mu fahimci cewa a kwai rukuni guda biyu a musulinci wadanda sune musabbabin samun rabauta ga Dan Adam wajen cimma rayuwa mai kyau a Duniya da lahira, na farko imani da kyakyawar akida sai kuma na biyunsa shine aiki mai kyau.
Wannan ita ce hanya ta samun hakikanin rabauta ga ko wani dan Adam Namuji ne ko Mace, duk wanda yayi Imani kuma yayi aiki managarci, hakika ya rabauta da rayuwa mai kyau.
A cikin littafin AlMizan fi Tafsiri kur'an kalkashin Ayar da ta gabata Allama Tabattabayi(Rahamar Allah ta tabbata a gareshi ) ya bayyana cewa Hakika Allah madaukakin sarki ya yi tanadi mai kyau ga mumunai wadanda suka aikata aiyuka masu kyau kuma wannan Aya tayi albishir ga Mata, domin Allah madaukakin sarki bai banbantasu ba da Maza wajen karbar imaninsu ba, kazalika bai banban ta su ba wajen karbar aiyukansu ba na gari ba. Domin wadannan abubuwa guda biyu shine asalin samun rabauta na rayuwa mai kyau a Duniya da Lahira. Wanda kuma hakan ya sha babban da da’awar masu bautar gumaka da kuma Ahlul Kitab Yahudu da Nasara wadanda suke haramtawa Mata duk wani jin dadi na Addini kuma suka babbantasu da Maza wajen aiyukan bauta, sannan suka ajjesu a wani karamin matsayi ta yadda babu yadda za su yi su kamo Mazaje wajen bauta kuma a kulun za su dawama ne a wannan matsayi na matsi da danniya.
Musuc*************************************************
Masu saurare Alkur'ani mai tsarki ya koyar da mu yadda za mu samu managarciyar rayuwa wacce ta ginu bisa rukuni guda biyu Imani da aiki mai kyau kamar yadda Ayar da ta gabata ta bayyana mana.wannan rukuni guda biyu suke kara sanya ko wani mumuni karfin guwa wajen zurfafa tunaninsa yayin da yake karansa Alkur'ani mai girma domin yin tunani ga Ayoyin Kur'ani mai tsarki na haskaka zukata tare da sanya su cikin nutsuwa ,kuma hakan na daga cikin hanyoyin samun managarciyar rayuwa kamar yadda hadisai da dama suka bayyana.
A cikin Littafin kafi na sikatu islam kulaini an rawaito hadisi daga shugabanmu Imam Aliyu bn Husaini Assajad (a.s) na cewa (da duk wanda ke tsakanin gabas da yamma zai koma ga mahalicinsa ba, ba na samu kadaici ba matukar akwai Alkur'ani tare da ni).
A cikin littafin Fikhu Rida (a.s) an rawaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s) na cewa ( duk wanda ya karanta Suratu Muzamil a cikin sallarsa ta Isha ko kuma a karshen Dare to ranar wannan yini da daransa za su kasance masa sheda wajen mahalicinsa kuma Allah zai raya shi bisa rayuwa mai kyau idan kuma aka tashi amsar ransa za'a karbe cikin karamci.
Har ila yau a cikin littafin Sawabul A'amal na sheik Saduk an rawaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) na cewa ( duk wanda ya karanto suratu Mudassir a cikin Sallar sa ta farilla, hakki ne ga Allah madaukakin sarki ya sanya shi cikin Al'ummar Manzon Allah Muhamad tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sannan har abada ba zai ga wulakanci ba a rayuwarsa ta Duniya idan Allah ya yarda.
Masu saurare duk wanda ya rasa wannan rukuni guda biyu wato Imani da aiki mai kyau a rayuwarsa, hakika ya rasa rayuwa mai kyau, kuma zai samu kansa cikin kaskanci duhun zuciya da kuma matsaltsalu kala-kala wadanda za su sanya shi cikin wulakancecciyar rayuwa a duniya da lahira. Kamar yadda kur'ani mai tsarki ke mana ishara da hakan, a cikin suratu Taha aya ta 124 Allah madaukakin sarki na cewa ( wanda kuma ya bijere wa Alkur'ani to hakika zai yi rayuwa mai kunci kuma mu tashe shi makaho ranar Alkiyama) Allah madaukakin sarki ya kiyamu da kuncin rayuwa domin Albarkar Alkur'ani da kuma dukkanin Annabawansa tsarkaka.
Musuc*****************************************************
Masu saurare daga karshe za mu rufe shirin da Addu'ar shgabanmu Iman Aliyu bn Husain zainu Abidin (a.s)(( ya ubangiji ka sanyamu daga cikin wadanda ka tsawaita rayuwarsu,kuma ka kyautata aiyukansu, ka cika Ni'imarka a garesu, kuma ka yarda da su, ka raya su da managarciyar rayuwa wacce ka dawwamar da ita cikin fara'a da farin ciki kuma ka daukaka su sannan ka cika rayuwar su ya mafi jin kan masu jin kai.