karamin Sani kukumi-Mine ne Manufar halittarmu
Shirin da kan bijoro da wata tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Jama’a masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ne, shirin da kan bijoro da wata tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata .mun zabi wadannan ababe guda biyu ne domin aiki da wasiyar shugaban Hallitu (S.W.S) wacce maliman musulunci suka rawaito a cikin littatafansu masu albarka, inda Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ke cewa:(na barmu ku nauyaya biyu, Littafin Allah da kuma iyalan gidana kebabbu,idan kuka yi riko da su ba za ku bata ba har abada, domin masani mai tausayi ya bani labarin cewa ba za su rabu ba har abada har sai sun sameni a bakin koki(wato kokin Alkausara) za mu gani yaya biyayyaku za ta kasance a garesu.
tambayarmu ta Yau ita ce minene Manufar halittarmu? kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai.
Musuc************************************************
masu saurare,domin amsar wannan tambaya za su koma cikin Kur'ani mai kirma da kuma tafarkin iyalan gidansa domin jin irin amsar da za mu samu.
da farko za mu fara da littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki, a cikin Suratu Zariyat daga Aya ta 56 zuwa ta 58 Allah madaukakin sarki na cewa:(Ban kuwa Halicci Mutum da Aljan ba sai don su bauta min.
Ba na neman wani arziki a wurinsu kuma Ba na neman Su ciyar da ni
Hakika Allah shi ne Mai yawan arzutawa ma'abocin tsananin karfi.)
har ila yau a cikin Suratu Mulk Aya ta farko da ta biyu Allah madaukakin sarki na cewa:(wanda mulki yake hannunsa Ya daukaka, kuma shi mai iko ne bisa dukkan komai.
wanda ya halicci mutuwa da rayuwa don Ya jarraba ku,(ya ga) waye a cikinku ya fi kyakkyawan aiki, shi kuwa Mabuwayi ne Mai yawan gafara ne)
shugabanin shiriya tsarkaka sun ruwaito hadisin kudisi daga kakansu Mustapa (s,w,s) daga ubangiji madaukakin sarki ya ce (hakika na kasance wata Taska boyayya , da na so bayyanar da kaina, sai na halicci halittu domin su bayyanar da ni).
Masu saurare bari mu koma bangaren shugabanin shiriya iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka domin jin irin amsar da za mu samu dangane da wannan tambaya.a cikin littafin Ilalu Shara'I'I na Sheik Saduk (R A ) an ruwaito wani hadsi daga shugabanmu Imam Sadik(a.s) ya ce (Imam Husan dan Ali amincin Allah ya tabbata a garesu ya fito wayen Sahabansa ya ce Ya Ku mutane Hakika Allah madaukakin sarki ya halicci bayi domin su sanshi idan kuma suka sanshi sais u bauta masa, idan kuma suka bauta masa sun wadato daga bautar waninsa. wani Mutune daga cikin sahabansa ya meke ya ce Ya ce Ya Dan Ma'aikin Allah na sadaukar maka ma'aifana yaya ne sanin Allah? sai Imam (a.s) ya ce sanin mutanan ko wani lokaci na shugabansu wanda ya wajabta a yi masa da'a da biyayya.)
har ila yau a cikin Littafin na Shara'I'I an ruwaito wani hadisi daga Muhamad bn Amarat ya ce na tambayi Imam Sadik (a.s) saboda da mi Allah ya halicci hallitu?Sai Imam (a.s) ya ce da ni, Hakika Allah madaukakin sarki bai halicci hallitu ba don wasa, kuma bai bar su ba hakanan sakaka ba, ba shakka ya halicce su domin bayyana kudurarsa, kuma ya kallafa masu biyyayarsa,to wajibi ne su amsa kiran sa, bai hallici su kuma domin su amfane shi da wani abu, ko kuma kare masa wata cutarwa ba, hakika ya halicce su ne domin amfanarsu kuma ya shiryar das u zuwa rayuwa ta har abada).
Musuc**************************************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, shek Saduk(r.a) ya ce wani Mutune ya zo wajen Imam Sadik (a.s) ya ce masa Ya Babban Abdullah wani abu mai ban al'ajabi an halicce mu ne kawai saboda dan wani lokaci a duniya bayan mun mutu abinsemu shi kenan . sai Imam (a.s) ya ce ya kai dan uwana ba a halicce mu dan dan wani lokaci hakika an halicce mu ne domin rayuwa ta har abada domin mutuwa kaura ce daga wani rayuwar duniya zuwa rayuwar Lahira).
a cikin Littafin Ilalul shara'I'I na shek saduk an ruwaito wani hadisi daga Abi Basir ya ce na tambayi Aba Abdullah Sadik (a.s)dangane da kauli Allah madaukakin sarki (Ban halicci Mutun da aljan ba sai don su bauta min) Suratu Zariyat aya ta 56
sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa ya halicce su domin ya umarce su da Ibada. Abu Basir ya ci gaba da cewa to minene ma'anar ayoyi (kuma da Ubangijinku Ya So da Lallai ya mayar da Mutane Al'umma daya, ba kuwa za su bar sassabawa ba a tsakaninsu. sai wanda Ubangijinka yayi wa rahama, a kan haka kwa ya halicce su,kuma Kalmar ubangijinka ta tabbata cewa lallai zan cika Jahannama da Aljanu da Mutane baki daya). Suratu Hud Aya ta 118 da kuma ta 119.
sai Imam (a.s) ya ce masa ya halicce su domin su yi aiyukan da rahamarsa ta wajabta a garesu, sai a yi masu Rahama.
a cikin Tafsiru Sa'alabi an ruwaito wani Hadisi daga Imam Sadik (a.s) inda a cikin sa aka tambayi Imam dangane da ma'anar kaolin Allah madaukakin sarki (Ko kuna tsammani ne Mun Halicce ku ne da Wasa, kuma ba za a dawo da ku gare ba?) sai Imam (a.s) ya ce hakika Allah ya kasance mai kyautatwa tun kafin ya halicci halittu, sai Allah ya so bayyana kyautatawarsa ga halittu kuma ya kasance wadatacce daga garesu,bai halicce su ba domin su amfane shi da komai ba,ko kuma su kare shi daga wata cutarwa ba, ya halicce su ya kyautata masu ta hanyar aiko masu da Mazzani domin su bayyana masu karya da gaskiya duk wanda ya kyautata a saka masa da Aljanna, wanda kuma ya saba a saka masa da wuta.)
masu idan muka yi nazari kan wadannan nasossi masu albarka za mu fahimci cewa hakika an halicce mu ne domin mu samu rabo mai girma da rayuwa dawamammiya gami da kyautatawa da kuma rahamarsa mai girma.
Musuc**********************************************
hitham