Mar 06, 2016 18:15 UTC
  • karamin Sani kukumi-yaya za mu bautawa Allah

shirin da kan bijoro da wata tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah da tafarkin Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka


Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ne, shirin da kan  bijoro da wata tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, tambayarmu ta Yau ita ce yaya za mu bautawa Allah madaukakin sarki domin mu cimma gurin da aka halicemu saboda shi kuma mu samu kyakyawan rayuwa ta har abada? kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari abinda aka yi mana tanadi a kan faifai.


 


Musuc**********************************************


 


Masu saurare kamar yadda muka saba, za mu fara da Littafin Allah wato Alkur’ani mai tsarki domin amsar tambayar ta mu ta yau, a cikin Suratu Bayyinat Aya ta 5 Allah madaukakin sarki na cewa:(Ba a kuma umarce su ba sai don su bauta wa Allah suna masu tsarkake addini gare shi, masu kaucewa bata, su kuma tsayar da salla kuma su bada zakka, wannan kuwa shine addini mikekke (na gaskiya).


A cikin Suratu Taha Aya ta 132 Allah madaukakin sarki na cewa:(ka kuma umarci iyanlinka da (tsai da) salla kuma da dawwama a kanta ba ma neman wani arziki daga gareka, Mu ne muke arzuta ka.kuma kyakyawan karshe yana ga masu tsoron Allah )


A cikin Suratu Gafir Aya ta 60 Allah madaukakin sarki na cewa:(Ku roki ni zan amsa muku, hakika wadanda suka yi girman kai, game da bauta min da sannu za su shiga Jahannama a wulakance).


Har ila cikin wannan sura Aya ta 65 zuwa ta 66 Allah maukakin sarki na cewa:(shi rayayye ne, babu wani abin bautawa sai shi,sai ku bauta masa  kuma masu tsarkake addini a gare shi. Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai* Ka ce hakika ni an hana ni in bautawa wadanda kuke  bautawa koma bayan Allah  a lokacin da ayoyi mabayyana suka zo min daga Ubangiji na, an kuma umarce ni da in mika wuya (ma’ana in musulinta) ga Allah Ubangijin talikai)


A karshen aya ta 7 cikin suratu Hashr Allah madaukakin sarki na cewa:(kuma abin da Manzo ya zo muku da shi sai ku dauke shi (ko kuma ku rike shi) kuma abinda ya hane ku sai ku hanu, ku kuma ji tsoron Allah, hakika Allah mai tsananin Ukuba ne)


Bayan wadannan ayoyi masu albarka, bari mu koma hadisan iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka domin samun amsar tambayar shirin na mu na yau wato yaya za mu bautawa Allah madaukakin sarki?


A cikin littafin Al’Ihtijaj an ruwaito wani hadisi, inda a cikinsa aka ce wani Zindiki ya tambayi shugabanmu Imam Sadik (a.s) a kan wata illa ce Allah madaukakin sarki ya halici halittu alhali shi ba shi da wata bukata  a gare su kuma bai zame masa tilas ba ya halice su, kuma bai halitta ba a danganta masa wasa ga halitar mu ba? sai Imam (a.s) ya amsa wannan Shubha da cewa hakika Allah madaukakin sarki ya halici halitu ne domin bayyana hikimar sa da wanzar da iliminsa da kuma tabbatar da renonsa a kan tallikai.Sai wannan Zindikin ya ci gaba da tambayar Imam (a.s) to mi nene yasa bai takaita a wannan gida ba (wato gidan duniya) ya sanya shi gidan sakamako da na Ukuba?sai Imam (a.s) ya ce  hakika wannan gida wato gidan Duniya gurin  jarabbawa ne, gidan aiki ne, gidan nema sakamako ne mai kyau ko maras kyau, kuma gidan neman rahamar ubangiji ne, Allah madaukakin sarki yayi haka domin ya jarabba bayinsa? Domin haka wannan gidan ba zai kasance ba gidan sakamako).


 


 


************MUSUC******************


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da riwayar ibn Hajar Askalani wacce ya ruwaito cikin littafinsa mai suna Sawa’ikul Muhrika ya ce daya daga cikin manyan maluman sunna ya ga Imam Hasan Askari (a.s) a wata riwayar kwa an ce ya ga Imam Muhamad Jawad (a.s) yayin da yake karami yana tsaye yana kallon kananen yara suna wasa da abin wassansu ahanunsu, tunanin wannan malami  imam bai shiga wasan ne ba saboda ba shi da kayan wasa irin na wadannan yara sai wannan Malami (bai san matsayin imam ba hasali ma bai san ko dan waye ba) sai ya ce shin kana so insaya maka abinda za ka yi wasa da shi tare da wadannan abokaninka?sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa ba a halice mu don wasa ba. da jin wannan magana sai malimin nan ya fahimci cewa wannan yaro ya sha babban da sauren yara, cikin mamaki sai ya tambaye shi don mi aka halice mu? Sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa domin neman ilimi da Ibada. Sai Malamin ya ce masa daga ina ka samu wannan? Imam (a.s) ya ce daga fadar Allah madaukakin sarki:(Ko kuna tsammanin cewa Mun halicce ku ne da wasa kuma ku ba za a dawo da ku gare Mu ba?) suratu muminin Aya ta 115.


Kafin mu tattara amsar tanbayar, bari mu karanto wani bangare na Addu’ar shugabanmu imam  Hadi (a.s) wacce aka ruwaito a cikin littafin Ziyaratu Jami’a, a cikin wannan Ziyara ana ziyartar dukkanin limaman shiriya na iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka kamar yadda aka ruwaito cikin wani bangare na wannan ziyara, amincin Allah ya tabbata bisa ma’abota kira zuwa ga Allah,amintattu cikin soyayyar Allah,mukhlisai cikin tauhidin Allah, wadanda suka bayyanawa bayi  umarnin Allah da kuma haninsa , hakika mun shaida ku limaman shiriya ne kuma Ma’asumai ne, kun tseda Salla kum bayar da zakka, kuma kun yi umarni da Alheri kun yi hani da abin ki, kuma kunyi yaki saboda Allah har saida kuka bayyana da’awar sa kuka kuma bayyana farillansa kuka tsare iyakokunsa kuka kuma watsa shari’a da hukunce-hukuncen addininsa ku ka raya sunarsa kun ka kasance cikin wannan har saida kuka koma zuwa ga yardar Allah……………)


Daga karshe masu saurare, a Nasossin da muka karanto za mu fahimci cewa Ibadar da za cirar da mu wacce domin ta ne aka halicemu ita ce wacce a ka yi bisa ilimi da sani kuma cikin Ikhlasi ba tare da riya ba.


 


******************Musuc*******************************


Masu saurare ganin lokacin da aka bamu ya kawo karshe a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da ci gaban shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala musaman Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan alheri,wassalama alekum wa rahamatullahi ta’ala wa barkatuhu.