karamin Sani kukumi-yaya za mu bautawa Allah(2)
shirin da kan bijoro da wata tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah da kuma tafarkin Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka
Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ne, shirin da kan bijoro da wata tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirin da ya gabata Alkur’ani mai girma gami da hadisan iyalan gidan sa tsarkaka sun tabbatar da cewa hakika Allah madaukakin sarki ya halicce mu domin samun rabauta na isa ga kamala da kuma kyakyawar rayuma mai nagarta a duniya da lahira, kuma hakika hanyar cimma wannan guri shine sanin Allah madaukakin sarki tare da bautamasa,a shirin na Yau ma za mu ci gaba daga inda muka tsaya, amma kafin mu shiga shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadai a kan faifai.
*****************************Musuc***********************
Masu saurare kamar yadda aka saba shirin na Yau ma zai fara da Littaifin Allah mai tsarki wato Alkur’ani kafin mu ji sharhin daga tafarkin Ma’aikin Allah da iyalan gidansa tsarkaka, a cikin suratu Zumar Aya ta 2 da ta 3 Allah madaukakin sarki na cewa:(Hakika Mu Muka saukar maka Littafi da gaskiya, to ka bauta wa Allah kana mai tsarkake addini a gareshi.
Ka gane cewa tataccen addini na Allah ne. wadanda kuwa suka riki wasu iyayen giji ba shi ba,(suna cewa) Ba ma bauta masu sai kawai don su kusantar da mu zuwa ga Allah, ba shakka Allah zai yi hukunci a tsakaninsu game da abinda suke sassabawa a cikinsa. Hakika Allah ba ya shiryar wanda yake makaryaci kafiri).
Har ila yau a cikin wannan Sura daga Aya ta 11 zuwa 12 Allah madaukakin sarki na cewa:(Ka ce hakika ni an umarce ni da in bauta wa Allah ina mai tsarkake addini a gareshi.An kuma umarce ni da in kasance farkon Musulmi).
A cikin Suratu Bayyinat Aya ta 5 Allah madaukakin sarki na cewa:(Ba a kuma umarce su ba sai don su bauta wa Allah suna masu tsarkake addini gare shi masu kaucewa(bata), su kuma tsayar da salla kuma sub a da zakka, wannan kuwa shine addini mikakke (na gaskiya).
A cikin suratu Bakara Aya ta 112 Allah madaukakin sarki Ya ce:(Na’am,wanda ya mika wuyansa ga Allah yana mai kyautatawa, to yana da ladansa a wurin Ubangijinsa,(kuma masu yin haka) babu tsoro a gare su ba kuma za su yi bakin ciki ba).
Aya ta 79 cikin suratul An’am Allah madaukakin sarki na bayyana mana kaolin Khalifansa Annabi Ibrahim (a.s)(Hakika ni kam na juya fuskata ga wanda yahalicci sammai da kassai, ina mai karkata ga addini na gaskiya, kuma Ni ba na cikin Mushrikai).
Har ila yau a cikin wannan surat daga Aya ta 161 zuwa ta 163 Allah madaukakin sarki na cewa(ka ce (da su)Hakika ni Ubangiji na ya shiriyar da ni zuwa ga hanya madaidaiciya, hanyar Ibahimu mikakkiya kuma bai kasance daga mushrikai ba.
Ka ce (da su) hakika Sallata da Ibadata da rayuwata da mutuwata na Allah ne Ubangijin talikai
Ba shi da abokin tarayya.Da wannan aka umarce ni,kuma ni ne farkon mai mika wuya (a wannan al’ummar)).
Masu saurare a jimilce amsar daza mu dauka daga wadannan ayoyi masu albarka da ma makamantansu shine abinda aka umarce mu da shi, bautar Allah madaukakin sarki da Ikhlasi kuma wannan bauta ta kasance da dukkanin mu’amalarmu ta rayuwa kamar Salla, Azumi, ziyara, ciyarwa, sadaka, infaki tare da mu’amalmu da sauren hallitu, dukkaninsu su kasance don neman yardar Allah madaukakin sarki, kuma Ibadarmu ta kasance cikin kyautatawa,kuma bawa ya sallama Al’amuransa ga Allah yana mai kyautatawa.
**********************Musuc*******************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara da riwayar shugaban hallitu Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayin da aka tambaye shi ma’anar Ihsani sai ya ce ka bautawa Allah kamar kana ganinshi, idan kai ba ka ganinsa hakika shi yana ganinka).
A cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga shuganmu Imam Sadik (a.s) yayin da yake bayyani kan kaolin Allah madaukakin sarki(wanda ya halicci mutuwa da rayuwa don ya jarraba ku,(ya ga) waye a cikinku ya fi kyakkyawan aiki.)sai Imam (a.s) ya ce ba ana nufin wanda ya fi ku aiki ba ne,a’a ana nufin wanda ya fi kowa kawo aikin da aka bukata kuma ya kawo daidai cikin tsoron Allah da Niya ta gaskiya).har ila yau Imam (a.s) na cewa:(dawama a kan aiki har ya zamanto cikin ikhlasi ya fi yawan aiki, aiki khalisi shine wanda za ka aikata ba tare da neman godiya ko yardar wani ba, sai Allah madaukakin sarki).
A cikin littafin Tuhuful Ukul an ruwaito hadisi daga Imam Husain (a.s) na cewa:(hakika wasu Mutane suna bautar Allah domin nemam sakamako, wannan ita ce ibadar ‘yan kasuwa, wasu kuma suna bautar Allah domin tsoronsa wannan ita ce Ibadar Bayi, wasu kuwa suna bautar Allah ne domin godiya a gareshi wannan ibada ita ce ibadar ‘yantattu kuma ita ce ibadar da ta fi)
Kamar yadda aka ruwaito wani hadisin daga shugabanmu Iman Sadik (a.s) na cewa Ibada Kashi uku ce, wasu Mutane suna bautawa Allah domin tsoronsa wannan ibada ita ce ibadar Bayi,wasu Mutanan kwa suna bautawa Allah madaukakin sarki domin nemam Lada wannan ibada ita ce ibadar ‘yan kasuwa, wasu bayin Allah kuwa suna bauta masa don soyayyarsu a gareshi wannan ibada ta su ita ce ibadar ‘yan tattu kuma ita ce ibadar da ta fi).
A cikin littafin Almahasin An ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) na cewa:(Hakika Ubangijinku mai jin kai ne kuma yana godewa kadan,Hakika Idan Bawa yayi Salla Raka’a biyu domin neman yardar Allah ,Allah zai sanya shi Aljanna).
Bayan wadannan ayoyi da kuma hadisan iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka za mu fahimci amsar tambarmu da cewa duk ibada ya kamata a yi ta domin yardar Allah madaukakin sarki kuma fiyayyar Ibada ita ce wacce aka yita domin soyayya da godiya ga Allah madaukakin sarki.
*******************Musuc**************************
Masu anan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a madadin wadanda suka taimakawa shirin a ka saurara musam