Mar 06, 2016 14:50 UTC
  • karamin sani kukumi-Wace Kamala ce Saboda Ita Aka Halice Mu

shirin da kan bijoro da wata tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah da kuma tafarkin iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ne, shirin da kan  bijoro da wata tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata, a shirin da ya gabata mun bayyana cewa hakika Allah madaukakin sarki ya halice mu ne domin isar da mu ga alherinsa, kafin cimma wannan alheri muna bukatar wata kamala,to wata Kamala ce wannan? Wannan ita ce tambayarmu ta yau,domin samun amsar wannan tambaya za muyi ruji’I zuwa nauyaya guda (kur’ani mai tsarki da kuma tafarkin Manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka domin su ne Allah maudaukakin sarki ya sanya hasken shiriya da kuma tabbacin tsira daga Bata ,amma kafin mu shiga shirin bari mu saurari abinda aka yi mana tanadai a kan faifai.


 


*******************Musuc***************************


Masu saurare kamar yadda aka saba shirin na yau zai fara da Littafin Allah wato Alkur’ani mai tsarki domin samun amsar wannan tambaya,a cikin Littafin A’ala Aya ta farko zuwa ta uku Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka tsarkake sunan Ubangijinka madaukaki.wanda ya halicci (halittu) sannan ya daidaita (ta).wanda kuma ya gwargwada (abubuwa)sannan ya shiryar da su).a cikin suratu Haj Aya ta 24 Allah madaukakin sarki na cewa :(Kuma an shiryar da su zuwa ga magana mai dadi (a duniya watau Kalmar shahada),an kuma shiryar da su zuwa ga tafarkin (Allah) abin yabo). A cikin suratu Alaq daga aya ta farko zuwa ta 5 Allah madaukakin sarki ya ce:(Ka yi karatu  da sunan Ubangijinka wanda ya yi halitta*Ya halicci Mutun daga gudan jini* Ka yi karatu  da sunan Ubangijinka mafi girma* wanda ya sanar da (mutun ta hanyar )alkalami*ya sanar da mutun abinda bai sani ba)


A cikin suratu Jum’a Aya ta 2 Allah madaukakin sarki ya ce :(shine wanda ya aiko manzo cikin mutanen da bas a karatu da rubutu daga gare su,yana karanta ayoyinsa a gare su yana kuma tsarkake su,kuma yana sanar da su littafi da hikma ko da yake da can sun kasance lallai cikin bata mabayyani) a cikin suratu Bakara Aya ta 268da kuma ta 269 Allah madaukakin sarki ya ce:(shaidan yana tsorata ku da talauci kuma yana umartar ku da munanan aiyuka.allah kuma yana yi muku alkawarin gafara daga gareshi da falala,kuma Allah Mayalwaci ne Masani.(Ubangiji) Yana bada hikma ga wanda ya so,wanda aka bai wa hikma kuwa,to hakika an ba shi alheri mai yawa,kuma ba mai wa’azantuwa sai ma’abuta hankula).


Masu saurare takaicecciyar da za mu fahimta daga wadannan ayoyi masu albarka da ma makamatansu  shine cewa hakika Allah madaukakin sarki ya halacci Mutune ya kuma daidaita shi cikin kyakyawar halitta sannan kuma ya kaddara masa kamala ya kuma shiryar da shi zuwa gareshi wannan shine mai kyau daga cikin ilimin ubangiji wanda ya sanar da bayinsa cikin fitirar su kuma ya aiko masu da Manzanni (amincin Allah ya tabbata a garesu) domin canza wannan ilimi na fitra zuwa aikata shi, domin haka ne suke kiransu zuwa shiriya da tsarkaka wacce za ta basu damar isa zuwa ga hikmar Allah madaukakin sarki.


Wannan hikma ita ce matattaran alheri mai yawa kuma ta hanyar ta ce ake samun falalar ubangiji Allah madaukakin sarki.kuma wannan shine hadisai da dama suke ishara a kansu.


 


****************************Musuc************************


 


Masu saurare barkanmu da sake saduwa,ci gaba shirin zai yi dubu ne kan hadisai Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, Abas dan Abdulmutalab ya tambayi Manzon Allah ya ce ya ma’aikin Allah minene ado ga Mutune? Sai ma’aikin Allah (s.a.w) ya amsa masa da cewa gaskiya cikin zance,sai Abas ya ce to minene kamala?sai Ma’aiki Allah tsoron Allah madaukakin sarki da kuma kyawawen dabi’u).


Amiru mumunin Aliyu bn Abi Talib(a.s)ya ce (ta hanyar  hankali ake samun kamalar zuciya kuma ta hanyar jihadi ake gyara zuciya).


A wata riwayar kuma Imam Ali(a.s) na cewa (kamalar Mutune hankalinsa, kuma kimar sa falalarsa).


An ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Bakir (a.s) na cewa:(kamalar ko wata kamala shine neman sani cikin addini da hakuri a kan musiba da kuma neman abinci ta hanyar halal).


An ruwaito hadisi daga shugabanmu Imam Sadik (a.s) inda yake bayyana siffofin kamilin Mutune ya ce ababe guda uku duk wanda yake da su ya cika kamilin mutune daga cikin ababe ukun da ya ambato a kwai hankali).


Shugabanmu Imam Rida (a.s) ya ruwaito hadisi daga iyayensa su kuma daga Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa( duk wanda yayi mu’amala da Mutane bai zalunce su ba,yayi magana da su bai yi masu karya ba, yayi masu alkawali ba tare da ya saba masu ba,na daga cikin wanda mutuntakarsa ta cika kuma adalcinsa ya bayyana sannan ya wajabta a kulla dan uwantaka da shi, kuma a ya haramta a ci namansa ko kuma a yi da shi).


A wani hadisin kuwa Amiru mumunin Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(sifofi guda shida na daga cikin kamalan Mutune kananasu da manyansu da kuma yanayinsu, siffofin kananansu shine yanayin aikin zuciyarsu da maganarsu, idan suna yaki za su yi cikin mazakunta idan kuma suna magana za su yi cikin fasaha da Balaga, su kuma manyansu hankalinsu da kuma yanayin kokarinsu…)


Masu saurare a karshe bari mu karanto muku riwayar Imam Sadik (a.s) inda a cikin wannan riwaya yake cewa(Mutune ya hadiu bisa abu biyu hankali ne da gangar jiki, duk wanda ya yi kuskuren hankali kuma gangar jikinsa ya bisa ba cika kamili ba, kuma zai kasance a matsayin wand aba shi da ruhi….asalin lamura a addini shine ruko da saloli na lokaci biyar tare da kaucewa sabon ubangiji da kuma nisantar manyan zunubai).


 


*********************Musuc*****************************