Mar 06, 2016 18:50 UTC
  • karamin Sani kukumi-Me Ya Sanya Ake Aibanta Duniya

shirin da kan bijoro da wata tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma tafarkin iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ne, shirin da kan  bijoro da wata tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a makun da ya gabata mun bayyana cewa Duniya nan da muke rayuwa a cikinta na daga mafi girman ni’imar da Allah madaukakin sarki ya horewa hallitunsa baki daya kuma ita ce manomar  Lahira ce kuma a cikinta ne dan Adam yake tanadar guzirinsa na Lahira, to idan duniya haka take minene matsayi da taklifin dan Adam a cikinta, kuma minene ya sanya wasu ayoyi da hadisai ke aibata duniya? Kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari tanadi bisa abinda a kayi mana tanadi a kan faifai.


*******************Musuc*************************************


Masu saurare kamar yadda muka saba za mu fara da littafin Allah wato Alkur’ani mai tsarki,a cikin suratu An’am Aya ta 32 Allah madaukakin sarki ya ce:(Rawuyar Duniya ba komai ba ce illa wasa da sharholiya,kuma ba shakka gidan Lahira shi ya fi alheri ga wadanda suke jin tsoron (ta). Yanzu ba kwa hankalta ba?)


A cikin suratu Ankabut Aya ta 64 Allah madaukakin sarki na cewa:(kuma wannan rayuwar Duniyar  ba komai ba ce face nishadi da wasa, kuma hakika (rayuwar ) gidan lahira ita ce rayuwa idan sun kasance sun sani).a cikin suratu Hadid kuwa Allah madaukakin sarki ya ce:(ku sani cewa ita dai hakika rayuwar duniya wasa ce da sharholiya, da ado da fariya a tsakaninku da kuma rigegeniya cikin tara dukiya da ‘ya’ya, kamar misalin ruwan saman da tsiransa suka ba wa manoma sha’awa sannan ya bushe sai ga kanshi fatsi-fatsi,sannan kuma ya zama karmami (tarkace) a lahira kuma azaba ce mai tsanani da kuma gafara daga Allah da kuma yarda. Rayuwar duniya ba komai ba ce sai jin dadi dan kadan.) suratu hadid Aya ta 64.har ila yau a cikin suratu Nazi’at daga Aya ta 37 zuwa ta 39 Allah madaukakin sarki ya ce:(to (a wannan lokaci) duk wanda ya yi dagawa. Ya kuma zabi rayuwar duniya.to hakika wutar Jahima ita ce makoma) a cikin suratu A’ala kwa Allah madaukakin sarki ya ce:(kai ku dai kuna fifita rayuwar duniya. Lahira kuwa ita ta fi alheri ta kuma fi wanzuwa) suratu A’ala Aya ta 16 da 17.a karshen bari mu karanto wata Aya  dake cikin suratu Bakara inda Allah madaukakin sarki ke cewa:(wadancan su ne wadanda suke musanya rayuwar duniya da ta Lahira,ba za a saukaka  musu azaba ba, kuma ba za a taimake su ba (ta ko wani hali)).suratu Bakara Aya ta 86. masu saurare idan muka yi nazari  ga wadannan ayoyi da ma makamantansu za mu fahimci cewa ba wai suna aibata duniya ba ne a matsayinta na duniya wacce take a matsayin ni’imar da Allah madaukakin sarki ya horewa halittu saidai suna aibata aiyukan wasu Mutane ne da ba su dauke ta ba a matsayi hanyar samun kyakkyawar rayuwa ta Lahira ba su yi guziri ba da aiyuka kyawawa suka  canza wannan ni’ima zuwa wassani, sharholiya,rigangeniya wajen tara dukiya da ‘ya’ya har kwanukansu suka kare ba tare da sunyi amfani da duniyar ba kamar yadda ya kamata domin isa zuwa ga kamala da kuma samun hakikanin sa’adar Lahira wacce ita ce madawwamiya.


**********************Musuc**********************************


Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai yi bayyani ne kan tafarkin Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka,daga cikin galgadin da yake yiwa sahabansa Ma’aikin Allah (swa) na cewa(kadda ku fifita rayuwar duniya a kan ta Lahira  kadda kuma ku yaudaru da jin dadinta da kuma ababen sha’awar dake cikinta domin Allah madaukakin sarki ya ce:( duk wanda ya yi dagawa. Ya kuma zabi rayuwar duniya to hakika wutar Jahima ita ce makoma) ku sani ita duniya la’antata ce kuma an la’anci abinda ke cikinta saidai in ya kasance na Allah).har ila yau a cikin wata riwaya Ma’aikin Allah tsira da maincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa:(duk wanda ya zabi duniya a kan lahira, zai tarar da Allah madaukakin sarki ba tare da wani sakamako mai kyau ba wanda zai kiyaye shi daga shiga wuta). Shugaban mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya ce: (duk wanda ya bautawa duniya da abinda ke cikinta kuma ya fifita ta a kan Lahira zai yi mumunan sakamako).har ila yau a wata riwayar kwa, Amiri mumunin na cewa:(idan ka  sanya addininka  kalkashin duniyarka  ma’ana idan bawa ya  dauki rayuwar duniya ita ce gaba da adininsa Imam (a.s) ya ce ya hallaka duniyarsa da Lahirarsa kuma zai kasance a Lahira daga cikin tabbabu, duk wanda sanya duniyarsa kalkashin addininsa hakika ya kare addininsa da duniyarsa kuma zai kasance a lahira daga cikin masu rabo). har ila yau daga khudubobin Imam (a.s) na cewa:( Ya Ku Mutane ku sani duniya fa, gida ne na dan  wani Lokaci ,  a gudanar da rayuwa ta wani dan lokaci a cikinta a fice, ita kuma Lahira gida ne na dawwama don haka ku yi aiki mai kyau a cikinta domin samun rabauta a dawamamiyar rayurku).


Masu saurare idan muka yi nazari  bisa wadannan hadisai za mu fahimci cewa abin aibatawa shine mutune ya zamanto mai bauta wa duniya kamar zai dawwama a cikinta kuma ya manta da Lahirarsa alhali duniyar mai karewa ce ita kuma Lahira ita ce dawamamiya domin haka, wadannan hadisai ke galgalin cewa kadda dan adam ya manta da lahirar sa yayi aiki a nan duniya domin ya samu Lahira .a cikin wani hadisin kudusi Allah madaukakin sarki ya  cewa Annabi Musa (a.s):(Ya Musa ka sani duk wata fitina tana tasowa ne daga son duniya).har ila yau a wata riwayar kwa Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa :(mafi girman zunubi, son duniya) a wata riwayar kwa Ma’aikin Allah ya ce (son duniya shine asalin ko wani sabo kuma shine farko aikata ko wani zunubi). Amiru mumunin (a.s) ya ce (hakika babu wani aiki da ya fi cutar da Bawa a yayin saduwarsa da mahalicinsa kamar son duniya).


*********************Musuc**************************


Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a Maku na daga za a jimu dauke da ci gaban shirin ,a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri,wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.