Mar 06, 2016 19:08 UTC
  • karamin Sani kukumi-Wani son Duniya Ne Abin Ki

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da kuma tafarki iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ne, shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirin da ya gabata mun bayyana cewa son duniya abu ne da ba shi da kyau, tambayarmu ta yau kwa ita  ce shin ko wani son duniya abin ki ko kuwa a kwai irin son duniyar da musulinci ya yarda dashi a musulinci, kafin amsa wannan tambaya bari mu saurari abinda a ka yi mana tanadi a kan faifai.


**********************Musuc*********************************


Masu saurare kamar yadda aka saba za mu fara da Littafin Allah mai tsarki wato alkur’ani mai girma,a cikin sauratu Al-Imran  Aya ta 148 Allah madaukakin sarki ya ce: (sai Allah  Ya Ba Su ladan duniya da kuma kyakkyawan ladan lahira(shi ne aljanna), Allah kuwa ya na son masu kyautatawa) a cikin suratu Nisa’a Aya ta 134 Allah madaukakin sarki ya ce:(Duk wanda ya zamanto yana son ladan duniya,to ya sani  cewa ladan duniya da na lahira yana wajen Allah .Allah kuwa ya kasance Mai Ji ne Mai gani) a cikin suratu Bakara wani bangare na Aya ta 200 zuwa ta 202 Allah madaukakin sarki ya ce:(……daga cikin Mutane a kwai masu cewa Ya Ubangijinmu ka bamu rabo , a lahira kuwa ba shi da wani rabo. A kwai kuwa daga cikinsu mai  cewa  “Ya Ubangijinmu  ka ba mu kyakkyawan (alheri ) a duniya , a lahira ma ka ba mu kyakkyawan (alheri) ka tsare mu daga azabar wuta.wadancan suna da babban rabo saboda abin da suka aikata, kuma Allah mai saurin hisabi ne).


Masu saurare idan muka yi nazari bisa wadannan ayoyi masu albarka da ma makamatansu za mu fahimci cewa Allah madaukakin sarki ya kan amincewa bayinsa da suka bukaci kyakkyawan alheri a duniya  kamar yadda suka bukaci na Lahira, kuma duk abinda ya kasance kyakkyawa da sakamako mai kyau abin so ne a wajen ubangiji, na duniya ne ko kuma na Lahira ne. har ila yau hadisai da dama sun bayyana mana cewa duk abinda Bawa zai nema a duniya saboda Allah madaukakin sarki kuma a matsayin ni’imar Allah domin maslahar sa,to wannan son so ne saboda Allah da kuma Lahirar sa , ba ya daga cikin Son duniya wanda addinin musulinci ya ki. An ruwaito hadisi daga ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka na cewa( ba ya daga cikin son duniya abinda bawa zai nema domin bukatuwarsa ba).


An ruwaito hadisi daga Ibn Abi Ya’afur inda yake cewa na cewa babban abdallah Imam Sadik (a.s) hakika ina  son duniya, sai Imam (a.s) ya ce da ni mi za ka aikata a cikinta?sai n ace masa, in yi aure a cikinta, inyi aikin hajji kuma in ciyar da iyalaina, in taimakawa ‘yan uwana kuma inyi sadaka, sai Imam sadik (a.s) wannan ba son  duniya ba ne, dukkan abinda ka zana na Lahira ne), abinda ya kasance daga cikin son duniya shine, fifitawa, da sadaukar da ita a kan lahira da kuma bauta mata, wannan shine abin ki, kuma shine abinda hadisai da dama suke galgadin da mu kiyaye aikata hakan.


****************************Musuc*********************************


Masu saurare, barkanmu da sake saduwa, ci gaban shirin zai fara ne da hadisin kudusi wanda iyalan gidan ma’aikin Allah tsarkaka suka ruwaito daga Kakansu Mustapa(s.aw) shi kuma daga Allah madaukakin sarki ya ce wa Annabi Dawud (a.s):(Ya Dawud,ka kiyayi zukatar da suka shaku da sha’awar duniya, domin hankulansu a katanke suke da ni). An ruwaito hadisi daga shugaban mumunai Aliyu bn abi Talib (a.s) na cewa:(duk wanda rayuwar duniya ta rude shi ya kasance maras gani da basira ga abinda ke gabansa).har ila yau a wata riwayar kuwa Imam (a.s) na cewa:( ku rabu da Duniya domin son ta ya kan sanya  Dan Adam ya makamce,ya zamanto baibai ko kurma daga fahimtar gaskiya daga karshe ya zamanto kaskantacce).a wata riwayar kuma Imam (a.s) ya ce:(hakika Duniya  da lahira makiyan juna ne wadanda hanyarsu ta sha banban da juna, duk wanda ya ke so duniya kuma ya yi mata biyayya sannan ya bauta mata zai kasance makiyin Lahira, matsayinsu kamar matsayin  gabas da yamma ne da kuma matafiyin cikinsu,duk wanda ya kusanci gabas yayi nisa da yamma haka zalika duk wanda ya kusanci yamma yayi nisa da gabas, ) ma’ana duk wanda ya kusanci duniya zai yi nisa da lahira, haka zalika duk wanda ya kusanci lahira zai yi nisa da duniya.


Masu saurare, hakika tsoron Allah ne kawai ke yaye kiyayar dake tsakanin duniya da Lahira kuma yan sanya  rayuwar duniya a matsayin matimakiyar rayuwar Lahira kamar yadda Allah madaukakin sarki ke cewa:(Aka kuma ce da wadanda suka ji tsoron Allah Me Ubangijinku ya saukar? Suka ce:Alheri wadanda suka kyautata a wannan duniya suna da kyakkyawar rayuwa a duniya.lallai kuma  gidan lahira shi ya fi alheri.madalla da gidan Masu tsoron Allah) suratu Nahl Aya ta 30. Kuma shugaban mumunai Aliyu bn Abi talib (a.s) ya ce:(bayin Allah ku sani hakika masu tsoron Allah sun kwashe alherin dake tattare da rayuwar duniya da lahira, domin sun yi tarayya da ma’abota duniya a duniyar ta su , su kuma ma’abota duniya ba za suyi  tarayya da ma’abota lahirar ba dangane da  lahirarsu, sun yi kyakkyawar rayuwa a duniya kuma sun amfanu  da mafi kyau na ababen rayuwar duniya, sun rabauta da duniya kamar yadda ma’abota duniya suka rabauta da shi,sun kwashi abinda masu sabo da girmar kai suka kwasa daga cikinta, sannan suka yi amfani da jin dadin duniyar wajen guzirin lahira ,suka ci ribarta ta yadda ma’abota duniyar ba su ci ba, sun dandana dadin zuhudu a rayuwarsu ta duniya sannan suka samu tabbacin cewa su makobtan Allah a ranar gobe wato a lahira, ba a kin karbar adu’arsu kuma ba za a rage masu komai ba daga rabon da jin dadi ba).har ila yau a wata khudubar Amiru mumunin (a.s) ya ce:( na hore ku da tsoron Allah domin tsoron Allah shi ke tattara duk wani alheri , kuma babu wani alheri bayansa, da tsoron Allah ake cimma duk wani alheri na duniya da Lahira  wanda babu wani abu da zai kai  wannan, wajen cimma irin wadannan aherin).


Shugabanmu Imam Kazim (a.s)ya ce:(ku sanyawa zukatantu rabo  na duniya ta hanyar basu abinda yake na halal, ku yi garkuwa da hakan bisa al’amuran addininku, domin an ruwaito hadisi daga shugaban hallitu (a.s) na cewa ba ya daga cikinmu wanda ya bar duniyarsa don Addininsa ko kuma ya bar addininsa domin duniyarsa).


*********************Musuc**************************


Masu saurare anan za mu dasa aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a Maku na daga za a jimu dauke da ci gaban shirin ,a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri,wassalama alekum warahamatullahi ta’ala wa barka tuhu.