Mar 06, 2016 19:10 UTC
  • karamin Sani kukumi-Wani son Duniya Ne Abin Ki(2)

shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka


Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ne, shirin da kan  bijoro tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirin da ya gabata mun bayyana cewa duniya manonar lahira ce to hakan na nufin mutane su bar duk wani jin dadi na duniya su koma su rungumi ibada kawai domin su cimma kyakkyawan sakamako na Lahira ? Wannan ita ce tambayarmu ta yau,kafin mu shiga cikin shirin ga wannan


*****************************Musuc**************************


Masu saurare kamar yadda aka saba ,shirin zai fara ne  da Littafin Allah wato alku’ani mai tsarki, a cikin suratu A’araf Aya ta 32 Allah madaukakin sarki ya ce:(ka ce (da su) Wane ne ya haramta (kyawawen)ababan ado na Allah, wadanda ya halitta don bayinsa, da kuma halali na arzuki (na abin-ci da abin sha)? Ka ce (da su)’’ wadannan abubuwa na wadanda suka bada gaskiya ne a rayuwar duniya, kuma halaliya ne gare su ranar Lahira, kamar haka ne muke bayyana ayoyi ga mutanen da za su san (gaskiyarsu)).a cikin Suratu Ma’ida Aya ta 4, Allah madaukakin sarki ya ce:(suna tambayar ka (cewa)me aka halatta musu(su ci)? Ka ce (da su)’’An halatta muku tsarkakan abubuwa…..) sannan ya tabbatar da hakan a cikin Aya ta 5 cikin wannan surat mai albarka bayan saukar Ayar cikar addini da kuma bayyana wulayar Aliyu bn abi talib (a.s), Allah madaukakin sarki ya ce:(A yau na halatta muku abubuwa tsarkaka………), a cikin suratu A’araf Aya ta 157 Allah madaukakin sarki ya yi bayyani irin ababan jin dadin da shugaban halittu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya zo da su((Su ne) wadanda suke bin Manzo Annabi Ummiyi wanda za su same shi a rubuce a gurinsu cikin Attaura da Linjila, yana  umartar su da aikin alheri yana kuma hana su  ga yin mugun aiki, yana kuma halatta musu (abubuwa) tsarkaka yana kuma haramta musu najasa,yana kuma sauke musu nauye-nauyensu da hukumce-hukumcen da suka kasance a kansu,saboda haka wadanda suka bada gaskiya da shi, suka kuma girmama shi,suka kuma taimake shi, suka kuma bi hasken da aka saukar a tare da shi,to wadannan su ne marabauta).a cikin suratu Rahaman kuwa Allah madaukakin sarki ya bayyana cewa dukkanin ababe tsarkaka da aka saukar wa bayi ni’ama ce daga cikin ni’imomin Allah ga  bayinsa.Allah madaukakin sarki ya ce:( Kasa kuma ya sanya ta saboda talikai*A cikinta kuma akwai ‘ya’yan itatuwa da dabinai ma’abota Kwansanni*Da kwayoyi ma’abota kaikayi da kuma masu kanshi*(saboda) haka da wane ne daga ayoyin Ubangijinku (ku mutane da aljanu) kuke karyatawa?). suratu Rahaman daga Aya ta 10 zuwa ta 13.


Masu saurare abin fahimta a cikin wadannan ayoyi masu albarka da ma makamantansu shine dukkanin ababen rayuwa tsarkaka da Allah madaukin sarki ya saukar, ni’ima ce daga cikin ni’imomi ga hallitu baki daya musaman ma ga bayinsa mumunai a matsayi na farko domin su rayu a nan duniya  su bauta masa kuma su gode masa a kan hakan,amma kuma abinda aka tanadi a Lahira na muminai ne kawai ba tare da kafirai ba wadanda suke amfana da ni’imar Allah a nan duniya ba tare da yi  masa godiya ba , domin haka ni’imar rayuwar duniya za ta kasance ga dukkanin halittu,mumunai da kafirai,  amma ni’imar Lahira ta mumunai ne ka dai).


*********************Musuc*****************


Masu saurare barkanmu da sake saduwa,cikakkun bayanai da sharhi na wadannan ayoyi za mu same su ne a tafarkin ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, da farko za mu fara da riwayar amiri mumunin Aliyu bn abi talib (a.s) wacce aka ruwaito a cikin Litattafan Kafi, Nahjul Balaga, Al’Ihtijaj  da saurensu, a cikin wannan riwaya an bayyana cewa daya daga cikin sahaban amiri mumunin Aliyu bn Abi Talib(a.s) mai suna Ala’a bn Ziyad ya kai karar dan uwansa mai  suna Asim bn Ziyad ,kan cewa ya kauracewa kayansa masu kyau ya sanya tsofuwar abaya, a kan cewa ya juyawa ni’ima da dadin duniya baya, sai Imam (a.s)ya tura aka kira shi sannan ya ce masa Ya wanda yake kiyayya da  kansa hakika kurabacecce ne ne  ya yi maka wahayi wato (shaidan), shin b aka yi wa iyalanka da ‘yan uwanka rahama ba, shin ka na ganin cewa Allah zai halatta maka ababamore rayuwa tsarkaka kuma yak i ka yi amfani da su, hakika kan mai rauni ne a kan hakan,sannan ya ce masa shin ba Allah madaukakin sarki ba ne ya ce: :( Kasa kuma ya sanya ta saboda talikai*A cikinta kuma akwai ‘ya’yan itatuwa da dabinai ma’abota Kwansanni*) shin ba Allah madaukakin sarki ba ne ya ce:(Ya Kwararo Koguna guda biyu suna haduwa (da juna) (na dadi da na zartsi)) sannan ba Allah madaukakin sarki ba ne ya ce:(Lu’ulu’u da mirjani suna fito wa daga cikinsu), wallahi bayyana ni’imar Allah a aika ce shi ne mafi so wajen Allah ga bayyana ta a baki, Hakika kuma Allah yana cewa:(Amma kuma ka zantar da ni’imar Ubangijinka).masu saurare a karshen wannan hadisi Asim bn Ziyad ya tambayi Amiru muminin (a.s) kan tafarkin shi da kansa, ya ce Ya Amiri muminin bisa wani dalili ka takaita kanka a kan cin abincin tallakawa da sanya sutura irin tasu, sai Amiri mumunin(a.s)ya ce a kwai babbanci tsakani na da kai, domin Allah madaukakin sarki ya wajabta shugabani adilai da tilastawa kansu  rayuwa irin da tallakawa  domin kar tallaka ya cutu da talaucinsa, bayan Asim ya saurari wannan galgadi , sai ya fita daga kuncin da ya dorawa kansa ya koma kan rayuwar sa kamar yadda ya saba ya ci gaba da amfanin da ni’imar da Allah madaukakin sarki wacce ya horewa bayinsa kuma ya gode masa.


A cikin littafin Wasa’il an ruwaito hadisi daga Sufyan Saury ya ce wata rana ya shiga wajen Imam Sadik(a.s) sai ya gansa da riga mai kyau, sannan ya ce masa hakika wannan riga ba ta daga cikin daga irin rigunanku ba sai Imam (a.s) ya amsa masa da cewa ka saurari ni kuma ka wa’azantu daga abinda zan gaya maka domin ya kasance alheri a gareka duniya da Lahira, kuma shi zai sanya ka koma ga Allah bisa sunnar Ma’aikinsa (S.A.W) ba kuma za ka mutu ba bisa bidi’aba ).sannan Imam (a.s) ya ci gaba da cewa hakika Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya kasace cikin wani lokaci da Al’ummar musulmi ke cikin rashi, kuma idan ni’ima ta samu a duniya, to ‘yantattu suke da hakkin amfani da ni’imar ba fajirai ba, mumunan cikinta ba munafikai ba, musulmin cikinta ba kafirai ba,shin kana inkarin haka ne ya Saury?n a rantse da Allah ina tare da abinda ka gani dare da Rana, hakika duk wani Hakki na Allah cikin dukiya ta ina sanya ta hanyar da Allah madaukakin sarki ya umarce ni da na sanya ta)


Masu abinda za mu fahimta ga wadannan riwayoyi shine, Allah madaukakin ya na son bayinsa su amfanu da ni’imar da yah ore masu tun a nan duniya kafin su koma lahira kuma sun amfanu da ita wajen gina rayuwarsu ta Lahira.


*******************************Musuc***********************


Masu saurare,a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman ma Injeniyamu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar ni ke muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatu llahi wa barkatuhu.