May 05, 2017 19:29 UTC

Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma

Jama’a Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi , shirin da kan  bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,Tambayarmu ta yau mine ne alakar dake tsakanin siffar da Allah madaukakin sarki ya siffanta Annabinsa (s.a.w.a) na cewa Shi ya fi cancanta da mumunai su yi masa biyayya fiye da kan su da kuma yadda Allah madaukakin sarki ya wajabta wulayarsa wato jibintar al'amuranmu gare shi da kuma Ma'aikinsa gami da Wasiyansa su kadai? Kafin amsa wannan tambaya sai a dakace mu da wannan.

*******************Musuc*******************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, Hakika a shirin da ya gabata, mun yi bayyani dangane da Siffar da Allah tabaraka wa ta'ala ya kebance Annabin Rahamarsa da shi kamar yadda ya zo cikin Suratu Akhzabi Aya ta 6:Allah madaukakin sarki ya ce :(Annabi Shi ya fi cancanta da mumunai su yi masa biyayya fiye da su yi wa kan su), Allah madaukakin sarki ya kebance Annabi Muhamadu (s.a.w.a) da wannan Siffa a tsakanin dukkanin Annabawan da suka gabata sakamakon girmar jin kai , tausayi da Rahamarsa a kan halittun Allah da kuma kokarinsa wajen kare duk wata cutuwa a gare su da kuma shiryar da su, tausayi da rahamar Ma'aiki (a.s) ga bayi kamar Tausayin Ma'aifi ne ga 'ya'yansa ,domin haka ne ma ya kira shi a  matsayin Uba ga Al'umma, alhali ga sauran Annabawa (a.s) ya kira su a matsayin 'yan uwa ga Mutanansu.kamar yadda Alkur'ani mai girma ya yi ishara da siffar (dan uwa )a yayin da ya Ambato lokacin da aka aika su zuwa wajen Mutanan su, kuma sanannan abu ne, tausayin Dan uwa ga 'yan uwansa ya fi zama kadan wajen martana ga tausayin Uba ga 'ya'yansa. domin haka ne Allah tabaraka wa ta'ala ya kebance Annabinsa mai girma (s.a.w.a) da wannan siffa wato shi ya fi cancanta da mumunai su yi masa biyayya fiye da su yi wa kan su.ma'ana shi ne ya fi cancanta ya shiryar da su kan yadda za su gudanar da Al'amuransu fiye da su saboda ya fi su sanin maslaharsu a karan kan su.amma dangane da kebance jibintar Al'amuran bayi gare shi da kuma Ma'aikin sa gami da wasiyansa su kadai, Hakika Allah tabaraka wa ta'ala ya Ambato tasiri da kuma albarkar hakan  a cikin Suratu Ma'ida inda Ya ce:(Allah a Hakika Shi ne: Mai jibintar al'amarinku da Manzonsa da kuma wadanda suka ba da gaskiya, wadanda suke tsai da salla da ba da Zakka, suna masu kaskantar da Kai* Duk kuwa wanda ya sa Allah a gaba a kan al'amarinsa da Manzonsa da kuma wadanda suka ba da gaskiya, to Hakika rundunar Allah su ne masu rinjaye) suratul-Ma'ida Aya ta 55 da kuma ta 56.Masu saurare abinda ake nufi da majibicin al'amura a wannan Aya mai albarka shi ne wanda zai jibinci al'amuran Mumunai wato shi ya fi kowa hakki wajen shiryar da su kan Al'amuransu, a cikin Littafin Kafi,an ruwaito Hadisi daga Shugabanmu Imam Ja'afaru Sadik (a.s) yayin da yake fassara Ayar da ta gabata yana mai cewa:(ma'ana wanda ya fi cancanta da hakki da ku da kuma Al'amuranku daga ku kanku da kuma Dukiyoyinku, Allah da Ma'aikinsa da kuma wandanda suka yi Imani wato Ali da kuma 'ya'yansa Shugabani 11 amincin Allah ya tabbata a gare su har zuwa ranar Alkiyama).da wannan ma'ana ne masu saurare za mu fahimci ma'anar wannan Aya (Annabi Shi ya fi cancanta da mumunai su yi masa biyayya fiye da su yi wa kan su) domin shi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya fi tausayi ga Mutane da kuma kiyaye maslaharsu da su kan kansu, kuma Shi Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka ya dabi'antu da dabi'ar Allah mai girma ne, Domin shi Allah tabaraka wa ta'ala shi ne wanda Rahamarsa ta gabaci fishinsa kuma shi ne mai tausayi ga bayinsa, kuma shi ne ya halicci bayinsa domin ya wadatar da su daga falalarsu kuma ya isar da su zuwa ga martaba da Kamala.kamar yadda yake hakika Shi Allah madaukakin sarki gwani kuma masani ne ga bayinsa a kan abinda yake maslaha a gare su, yana kuma kare musu duk wata cutarwa, kuma shi madaukaki wadatacce ne daga yi musu Azaba, da biyayyarsu, ba ya bukatar komai a gare su face alheri da kuma maslaha gami da rabautar su, kamar kuma yadda yake mafi kyau halittu da kyakkyawan tsari ga Al'amuran Bayi.a kan haka ,a kwai Ishara na dabi'antuwar Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib (a.s) haka zalika Shugabanin Mumunai daga 'ya'yansa da mafi martaba na Ruhin Tausayi da kuma jin kai irin na iyaye ga Al'umma domin haka ne ma suka kasance mafi cancanta da mumunai su yi masa biyayya fiye da su yi wa kan su.

************************Musuc******************************

Masu saurare barkanmu da sake saduwa, kuma kadda a sha'afa shirin na zo muku ne kai tsaye daga sashen Hausa na muryar jumhoriyar musulinci ta Iran dake nan birnin Tehran, Hakika Masu saurare da wannan bayyani da ya gabata za mu fahimci sirrin da ya sanya Shugaban Mumunai Aliyu bn Abi Talib(a.s) ya yi sadaka da Zobansa a yayin da yake halin ruku'I cikin sallarsa, da Ayar wulaya tayi ishara da hakan,a matsayin wata alama ga wanda zai Khalifanci Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ga Al'umma. Hakika wannan Waki'ar ta bayyana girman tausayin Shugaban Mumunai ga Al'umma da kuma tsananin jin kansa ga Al'umma a yayin da bai sha'afa ba wajen isar ga Alheri da kuma taimakon mabukata yayin da yake cikin salla., bisa bayanan da suka gabata kuma za mu fahimci sirrin nakalin Al'kur'ani mai tsarki dangane da siffar ma'aikin Allah (s.a.w.a) na cewa Shi ne ya fi caccanta ga Mutane su yi masa biyayya da kansu a yayin da ya isar da sakon Umarnin Allah na ya bayyana wasiyinsa Murtada a khudubar Qadir na karshen Hajjinsa kamar yadda ya zo cikin Littafin Kamaluddin a cikin wannan Khuduba, Ma'aikin Allah (s.a.w.a) ya ce:(Ya Ku Mutane! Shin kun san cewa Allah madaukakin sarki shi ne shugaba na, Ni kuma Shugaban Mumunai, kuma ni ne na fi cancanta da mumunai su yi masa biyayya fiye da su yi wa kan su, Sai Su Kace Haka ne Ya Ma'aikin Allah, sannan Ya ce Duk wanda Na kasance Mujibincinsa to Ali Majibincinsa ne Allah Ka jibinci wanda ya jibince sa ka kuma yi kiyayya ga wanda yayi kiyayya da shi, ka kuma taimaki wanda ya taimake shi, ka muzanta wanda ya muzanta shi, yi masa biyayya kamar yi mani biyayya ne, duk wanda na kasance mafi cancanta da ya yi mini biyayya fiye da yi wa kan sa, to Ali shi ma mafi cancanta ne da ya yi masa biyayya fiye da yi wa kan sa) sai wanda ya ruwaito hadisin ya ce bayan wannan kalamai na Ma'aikin Allah (s.a.w.a) sai wannan Aya   ta sauka,:(A Yau Na cika muku addininku, Na kuma cika ni'imata a gare ku, Na kuma zabar muku addinin Musulinci (shi ne) addini(na gaskiya)).Suratu Ma'ida Aya ta 3 sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi tare da iyalan gidansa tsarkaka yayi kabbara ya ce Allahu Akbar a kan cikar Ni'ima da kuma Anabta da Addinin Allah gami da wulayar Aliyu bn Abi Talib baya na.

**********************Musuc***************************

Masu Saurare, ganin Lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe, a nan za mu dasa Aya sai kuma a maku na ga ba da yardar Allah za a jimu dauke da wani sabon shiri, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kamala, musaman Aminu Ibrahim kiyawa, ni da na shirya kuma na gabatar nike muku fatan Alheri wassalama Alekum warahamatullahi ta'ala wa barkatuhu.