karamin Sani kukumi-Amfanuwa Da Ni'imar Duniya
Shirin da kan bijoro da tambaya tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki da tafarkin Iyalan gidan Ma'aikin Allah tsarkaka
Masu saurare barkanku da warhahaka da kuma sake sauduwa da mu a cikin shirin Karamin Sani Kukumi ne, shirin da kan bijoro da tambaya ne tare da kokarin amsa ta bisa bincike a cikin Littafin Allah wato Alkur'ani mai tsarki wanda barna ba ta zuwa masa ta gabansa ko kuma ta bayansa, saukekke ne daga Mai Hikima abin gode wa, da kuma hadisan Iyalan gidan Manzon Allah tsarkaka wadanda sune suka kiyaye hadisai da kuma Sunar Kakansu Mustafa tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi tare da iyalan gidansa tsarkaka, sun kiyaye shi daga duk wata gurabata na ragi ne ko na kari sannan suka bayyanawa Al'umma hakikanin ilimi, Sunna da tafarkin Manzon Allah domin samun tsira daga Bata,a shirin da ya gabata mun bayyana cewa Allah madaukakin sarki ya na son bayinsa su amfanu da ni’imar da ya hore masu a duniya, to ta yaya za su amfanu da wannan ni’imar a nan duniya ba tare da hakan yayi illa ba ga aiyuka ko kuma guzirinsu na Lahira? Wannan ita ce tambayar da za mu yi kokarin amsawa a shirin na mu na yau, amma kafin nan, bari mu saurari abinda a kayi mana tanadi a bisa faifai.
*******************************Musuc******************************
Masu saurare kamar yadda aka saba za mu fara da Littafin Allah wato alkur’ani mai girma,a cikin suratu Bakara Aya ta 172 Allah madaukakin sarki ya bamu amsar wannan tambaya a jimilce inda yake cewa:(Ya Ku wadanda kuka bada gaskiya, ku ci daga tsarkakan abubuwan da muka arzuta ku da su ku gode wa Allah idan kun kasance shi kadai kuke bauta wa).masu saurare wannan aya ta bayyana mana cewa amfanuwa da ni’imar Allah madaukakin sarki ya kamata ta kasance ta hanyar tsarkakun ababen da Allah madaukakin sarki ya hore mana kuma ta hanyar shari’a, wannan shi zai sanya mu amfanu da ni’imar Allah a nan duniya ba tare da wata cutarwa ba.
Na biyu kuma ya kasance anfanuwa da wannan ni’ima bisa godiyar Allah madaukakin sarki , idan hakan ya kasance zai zamanto amfanuwa da Ni’imar Allah a duniya guziri ne ga rayuwar lahira.masu saurare wannan shine abinda muka fahimta daga wannan Aya mai albarka,to ko mi riwayoyi za su ce dangane da wannan tambaya? Za mu fara a riwayar Abi Abduillah Al’abi daya daga cikin maluman Ahlu sunna wacce aka ruwaito a cikin sharhin usulul kafi, abu Abdullah Al’aby ya ce wani Mutune ya aibata duniya a gaban Sayyidina Aliyu bn Abi Talib (r.a) sai Imam Ali (a.s) ya ce masa minene ya sanya ka ke aibata duniya alhali ita gidan wadata ce ga wanda yayi guziri a cikinta, gidan girma ne ga wanda ya fahimce ta, kuma ita ce masaukar wahayin Allah , mahalin salatin mala’ikunsa kuma masalacin Annabawansa, kasuwar waliyansa, ku ribantu daga cikin kyawawen dake cikinta, kuma ku ci daga cikin ababe tsarkakan dake cikinta kuma ku godewa Allah madaukakin sarki bisa ni’imar da ya yi maku a cikinta).a cikin littafin Kafi an ruwaito hadisi daga Yusuf bn Ibrahim ya ce ya je wajen Imam Sadik (a.s) ya na sanye da kayan alfahari, sai Imam (a.s) ya tambaye shi a kan kayan da ya saka, sai ya ce masa na sanya fansar kaina a gareka, wannan riga da kuma abayar da kake gani dukkaninsu na saka an saka su ne da alhariri , mi zaka ce dangane da sakar alhariri? Sai Imam (a.s) ya ce masa minene laifin Alhariri? Hakika yayin da Imam Husain (a.s) ya yi shahada a Karbala’a yana sanye ne da Rigar da aka saka da Alhariri, sannan Imam (a.s) ya ci gaba da cewa, yayin da Amiri mumunin Aliyu bn Abi Talib (a.s) ya aiki Abdullahi bn Abas zuwa ga khawarijawa ya saka mafi kyau daga cikin kayansa kuma ya sanya mafi gamshi daga cikin turaransa kuma ya hau mafi kyau daga cikin abin hawansa) sai Imam (a.s) ya karanto wannan Aya (K ace (da su) wane ne ya haramta (kyawawen) ababen ado na Allah wadanda ya halitta bayinsa, da kuma halali na arzuka(na abin ci ne ko na abin sha)? Ka ce da su wadannan abubuwa na wadanda suka ba da gaskiya ne a rayuwar duniya, kuma halaliya ne gare su ranar Lahira. Kamar haka ne muka bayyana ayoyi ga mutanen da za su san gaskiya) suratu A’araf Aya ta 32 sannan sai Imam ya ci gaba da cewa Yusuf bn Ibrahim ka yi ado domin Allah ya na son masu ado saidai ya kasance abinda za ka sanyan ya zamto na halali).
**********************Musuc*********************************
Masu saurare barkanmu da sake saduwa,a cikin Littafin Kafi na sikatu Islam kulaini an ruwaito wani hadisi daga Sufyanu Sauri ya ce wata rana yana ficewa daga kofar Massalacin Harami sai ya ga Imam Sadik (a.s) sanye da kayan alfarma wato kaya masu kyau sai a cikin zuciyarsa ya ce wannan wata dama cena samu domin na tozarta Imam Sadikk daya daga iyalan gidan Ma’aikin Allah tsarkaka kuma in tozarta sa a bainar jama’ai, sai ya fice kai tsaye cikin Massalti sanan ya ce masa ya dan Ma’aikin Allah, Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi bai taba sanya irin wadannan kaya da alfarma ba, haka zalika daga cikin iyayenka babu wani da ya taba saka irin wadannan kaya.sai Imam (a.s) ya amsa da cewa:Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi ya yi rayuwarsa ne lokacin da babu kuma musulmai suna cikin bukata, kuma ya kasance yana amfani da daidai kwalkwadon abinda yake bukata domin gudanar da rayuwarsa, bayan wannan lokaci duniya ta wadata kuma babu wadanda suka dace ko kuma suka cancanci su yi amfani da ni’imarta kamar ‘yantattu, kuma mune muka fi kowa haki wajen amfani da ni’imar da Allah madaukakin sarki ya saukar mana , sannan sai Imam (a.s) ya ci gaba da cewa hakika Ni’imar duniya ba ta shagaltar da mumuni hakin da Allah madaukakin sarki ya wajabta a kansa ba, ya Sauri wannan kaya da ka ke gani na sanya ,na sanya su domin Mutane, sannan Imam (a.s) ya jakuda kusan Sufyan, ya kama ya kusanto da shi a kusansa sannan ya daga rigarsa sama ya nuna masa kayan da ya saka kalkashin wannan kaya na alfarma wata riga ce mai kaushi sai ya ce wannan riga ita ce na sanya domin kaina, wannan kwa da kake gani na saka ta ce domin Mutane. Sannan sai ya kalli rigar Sufyan yayin da yake sanya da tsofuwar riga mai kaushi a sama, a kasan rigar kwa a kwai rigar alfarma mai laushi sai ya ce masa wannan riga ta sama da ka saka ka sanya ta domin Mutane, ta kasan kwa ka saka ta domin kanka).
Masu saurare a takaice dai amfanuwa da ni’imar Allah madaukakin sarki na tsarkakeken ababen more rayuwa da ya horewa halittunsa alheri ga mumunai matukar na Halaliya ne da kuma godiyar Allah madaukakin sarki bisa ni’imar da ya horewa bayinsa .
*******************************Musuc***********************
Masu saurare,a nan za mu dasa Aya ganin lokacin da aka debawa shirin ya kawo karshe sai kuma a maku na gaba za a jimu dauke da wani sabon shirin idan Allah ya yarda, a madadin wadanda suka taimakawa shirin har ya kammala, musaman ma Injeniyamu Aminu Ibrahim Kiyawa, ni da shirya kuma na gabatar ni ke muku fatan alheri, wassalama alekum warahamatu llahi wa barkatuhu.